𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum. Malam ni ce
mahaifina ya rasu ya bar ni da ƙannena, ni ce babba ya bar kuɗi (N170, 000) sai
na ɗauki wannan kuɗin na fara kasuwanci da shi ina musu cefane yau da gobe sai
cefanen ya fi ƙarfin kuɗin, sai kuɗin suka ƙare, daga cikin ƙannen nawa akwai
waɗanda ba sa gidan ba da su ake cin abincin ba, to yanzu zan biya kuɗin ne ko
ba zan biya ba, kuma ya hukuncin waɗanda ba sa gidan? Na gode.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus salam, ‘yar uwa a
cikin Alƙur'ani aya ta 5 da ke suratun Nisá'i, Allah maɗaukakin Sarki ya
bayyana cewa kada a ba marayun da ba su hankalta ba dukiyar gadonsu da ake kula
masu da ita, amma ya ba da umurnin za a iya ciyar da su, a tufatar da su daga
wannan dukiya tasu, sannan kuma a riƙa faɗa masu magana mai daɗi. Wato sai ya
zama kenan ba laifi ne ba don mai kula da maraya ya ciyar da shi marayar daga
dukiyarsa, idan kuma da mutum zai yi sadaka ya ciyar da marayar a dukiyarsa ta ƙashin
kansa ba tare da waiwayar dukiyar marayar ba, to hakan ya yi kyau.
To sai ya zama kenan abin da kika
yi na kasuwanci da dukiyar gadon naku, da yin cefanen abincinku a ciki ba laifi
ba ne matuƙar an shirya gaskiya, amma inda matsalar take shi ne da har kika
bari kuɗin nan suka ƙare a cefane ba tare da cire wa sauran marayun da ba sa
gidan haƙƙinsu a cikin wannan kuɗi ba, a nan ne inda matsalar take, don haka
bisa shawara abin da ya kamata ki yi yanzu shi ne;
Ki nemi malami ko alƙalin da ke
da ilimin rabon gado, ya lissafa haƙƙin kowa daga cikin magadan nan, bayan an
gama lissafawa, sai ki nemo dai-dai haƙƙin waɗancan ‘yan uwa naku magada da ba
a ci abincin nan da su ba, sai ki nemo dai-dai abin da aka ce shi ne rabonsu a
N170, 000 ɗin ki ba su, in Allah ya so yin hakan zai fitar da ke daga shubha.
Ko kuma idan duk sun mallaki hankalin kansu, sai ki kira su ki sanar da su,
idan Allah ya sa sun ce ba komai sun yafe to shi kenan, amma idan ya kasance ba
su gama hankali ba, to ki bi wancan mataki na farko na nemo masu dai-dai
rabonsu, hakan ya fi alheri.
Allah S.W.T ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan
Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.