𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum Malam ina da
tambaya, wata ce take jinyar mahaifiyarta sai likita ya ba da doka, kuma idan
aka karya wannan dokar zai haifar da wata matsala, amma ita mahaifiyar ba ta
son bin dokan, idan kuma 'yarta ta sa ta bin dokar sai ta yi ta mata Allah ya
isa har ma ta kai ga ta tsine mata, to dan Allah Malam ya za ta yi kuma ya
hukuncin furucin da tai mata?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salamu. Allah ba ya
kama rai sai da abin da ya zama laifi ne, ita kuma wannan yarinya ba laifi ta
yi ba, tana ƙoƙarin ta ga mahaifiyar nan tata ta kiyaye dokar lafiya ne don ta
sami lafiya su ci gaba da yin ingantacciyar rayuwa tare, ga shi kuma Allah Maɗaukakin
Sarki ya ce:
"KADA KU KASHE KAWUNANKU,
LALLAI ALLAH YA KASANCE MAI JINƘAI NE A GARE KU". Suratun Nisá'i, aya ta
29.
Wannan ya sa yarinyar ba ta son
mahaifiyar nan tata ta yi sanadin rasa ranta ta hanyar saɓa wa dokar lafiya, saboda
wannan dalili, wannan tsinuwa ba za ta kama yarinyar ba inshá Allah saboda
manufar yarinyar ba son ta ɓata wa mahaifiyar rai take yi ba.
Saboda haka ina ba ta shawara
idan akwai waɗanda mahaifiyar tata take jin maganarsu, ko aminanta, ta sanar da
su don su riƙa ba ta shawara a kan kiyaye dokokin maganin da aka gindaya mata,
don ki sami sauƙin shawo kanta wajen kiyaye tsarin magungunan.
Allah ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan
Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/GcU1I5wjOB18K4PA6eURƘƘ
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.