Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Mala'iku Na Tsine wa Mijin Da Ya Ƙi Amsa Buƙatar Matarsa?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum, malam dan Allah ina da tambaya, na kasance ina da sha'awa sosai kuma ba ni kaɗai ba ce gurin mijina, kuma duk sanda na nuna ina bukatarsa ba ya yadda, duk yadda nabi se ya ce bacci, kullum se dai in shi ne yake da bukata, kuma in na ki se na tuna da malaikun rahma za su kwana suna tsine min, shin dan Allah malam shi mala'iku ba sa tsine masa ne?? kuma wallahi yana jefani cikin wani hali duk idan na nuna ina da bukata ze kawo hujja mare karfi ya fada min.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam, Lallai ‘yar uwa ya tabbata a hadisi ingantacce cewa duk matar da mijinta ya neme ta ta ƙi amsawa za ta kwana Mala'iku na tsine mata har zuwa safe. Amma ba a sami hadisin da ya nuna shi ma namiji idan matarsa ta neme shi ya ƙi amsawa cewa shi ma zai kwana Mala'iku na tsine masa ba. Kuma malamai ba sa ƙiyasta wannan hadisin a kan mijin da ya ƙi amsa kiran matarsa ba.

Amma malamai sun tabbatar cewa duk wanda ya ƙi amsa kiran mayarsa don manufar cutar da ita, ko ƙuntata mata, to wannan ya saɓa wa umurnin Allah a zamantakewar aure, saboda Allah Maɗaukakin Sarki ya ba da umurnin a mu'amalanci mata ɗa kyautatawa a Suratun Nisá'i, aya ta: 19.

Kuma Allah Maɗaukakin Sarki a wata ayar ya bayyana cewa mata suna da haƙƙi kwatankwacin wanda yake kansu, a suratul Baƙara, aya ta: 228.

Saboda haka wajibi ne a kan maza su riƙa ƙoƙarin biya wa iyalansu haƙƙoƙinsu na aure saboda taimaka masu wajen kaucewa faɗawa ga saɓa wa Allah S.W.T. Allah ya shiryar da mu.

Allah ne mafi sani.

 Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.🏻

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Za ku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8ƙu9GT

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshiﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments