DARASI NA 38
Yadda Allah Ya Hukunta Saduwar Aure
Annabi {s.a.w} ya yi nuni da idan
mutum zai kusanci matarsa, to ya aika ɗan aike,
Abinda
ake nufi da ɗan aike anan shi ne ka fara gabatar da wasanni sosai kafin fara
saduwa da ita.
Amma
a cikin saduwar akwai iyoyinkin da ALLAH ya iyakance, wanda ya kiyayesu zai
sami lada, wanda ya tsalleke dokar ALLAH kuma zai haɗu da azabar ALLAH, kamar
yadda hadisai suka tabbatar.
Jabiru
Ɗan Abdullahi (R.A) ya ce:
Yahudawa sun kasance suna cewa:
Idan mutum ya yi jima’i da matarsa ta baya, a cikin farjinta, yaronsa zai zama
mai ido a juye,
Sai ALLAH Maɗaukakin sarki ya
saukar da cewa:
Matayenku
gonaki ne a gareku kuzo ga gonarku ta inda kuke so.
[Bukhari da Muslim]
Wannan hadisi yana magana ne akan
halaccin saduwa ta ko wacce siga, a kwance ko a juye koma ta yaya ne, amma kada
mutum ya sadu da matarsa ta duburarta, kuma kada ya sadu da ita idan tana
haila.
Manzon
ALLAH {s.a.w} ya la'anci wanda ya sadu da matarsa ta duburarta (luwaɗi kenan)
kuma ya tsine wa wanda ya sadu da matarsa tana haila.
Abbas (R.A) ya ce: Manzon ALLAH
{s.a.w} ya ce: ALLAH baya dubi ga mutumin da yazowa namiji, ko macce ta
duburunta.
[Tirmizi da Nisa’i da ɗan Hibban]
Wannan hadisin yana nuni da cewa
ALLAH baya kallon Rahma ga wanda ya sadu namiji ko mace ta baya, wato ya aikata
luwadi da namiji ko da mace.
Abu
Huraira (R.A) Ya ce:
Manzon
ALLAH {s.a.w} Ya ce:
Wanda aka la’ana shi ne luɗu da
mace ta duburunta.
[Abu Dawuda da Nisa’i]
Wato wannan hadisin ma yana magana
akan yadda ALLAH ya tsine wa me yin luwaɗi da mace, wato me saduwa da matarsa
ta duburarta.
ALLAH
TA'ALAH ya tsine wa namijin da yake saduwa da mace tana haila da kuma wanda yake
saduwa da mace ta duburarta.
Duk
wanda yake aikata irin wannan aiki ya yi ƙoƙari ya tuba ya daina, duk wacce
tasan mijinta yana aikata irin wannan aiki da ita daga yanzu ta daina, inba
haka ba da ita da mijin ALLAH zai yi musu azabah.
Kome
mijinki zai yi kada ki yarda ya sadu dake idan kina haila, kuma kada ki yarda
mijinki ya sadu dake ta duburarki, wato ya yi luwaɗi dake.
Domin
hakkin ALLAH da hakkin Manzon ALLAH {s.a.w} sama suke da hakkin iyaye da kuma
hakkin miji.
ALLAH ka bamu ikon aiki da abinda
muka karanta.
ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.
Hukuncin Wanda Ya Sadu Da Dabba
Manzon
ALLAH {s.a.w} ya ce:
Wanda ya yi zina da dabba, to a kashe
shi, kuma a kashe ta itama,
Sai nace: Ibn Abbas (R.A) Mene ne
sha'anin dabbar kuma?
Sai ya ce: Nima ban sani ba, sai
dai ya faɗi wannan ne saboda kawai yana ƙyamar kada aci namanta bayan an aikata
wannan aikin da ita.
[Abu Dawud da Tirmizi]
Wannan hadisi yana nuni kai tsaye
da duk wanda aka samu ya aikata zina da dabba to a kashe shi itama dabbar a
kasheta,
Sai
dai kuma muna wani zamani da ba a hukunci da littafin ALLAH, saboda haka duk
wanda ya aikata irin wannan aiki, to sai ya gaggauta tuba ga ALLAH, idan ALLAH
yaso sai ya yafe masa, idan yaso kuma sai ya yi masa hukunci a ranar lahira.
Amma
wajibi ne a kashe wannan dabbar saboda namanta ya haramta.
ALLAH ka bamu ikon aiki da abinda
abinda muka karanta.
ALLAH ka gafarta mana zunubanmu
baki ɗayanmu Ameen.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.