𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
alaikum warahamatullahi ta'ala wabarkatuhu. Don Allah ina tambaya shin maccen
Aure ya halasta ta sha Gaban mijinta Don ya ce mata yafi samun natsuwa da ita?
Na gode Allah ya saka da alkhairi.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus
Salám wa Rahmatullah wa Barakatuhu, wasu malaman suna ganin hakan bai yi daidai
da ɗabi'ar rayuwar mutum ba, amma sai dai babu wani nassi bayyananne da ya
haramta yin hakan, har ma wannan dalilin ya sa wasu malaman suke da fahimtar
halascin yin hakan, saboda Allah Maɗaukakin Sarki ya bayyana cewa: Matayenku
gonakinku ne, ku zakke wa gonakinku ta inda kuka so, kamar yadda ya bayyana a cikin
Suratul Baƙara aya ta 223.
Ayar nan ta
nuna cewa za a zo wa mataye ta inda aka so, to amma banda ta inda nassoshin
Shari'a suka haramta, kamar saduwa ta dubura, da kuma lokutan da Shari'a ta
haramta saduwa da mace, kamar lokacin da take yin jinin haila da jinin haihuwa.
Idan har an kiyaye waɗannan, to Shari'ar Musulunci ta amincewa ma'aurata da su
ji daɗin junansu ta yadda suka so.
A taƙaice dai,
matuƙar an amintu da kamuwa da wata cuta, kuma ma'aurata suka ga maslahar haka
a tsakaninsu, to ba wani nassi ingantacce kuma bayyananne da ya haramta yin
hakan.
Allah S.W.T ne
mafi sanin daidai.
Jamilu
Ibrahim, Zaria.
Ga Masu Buƙatar
Shiga Wannan Group Za ku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/BXjuXb1WxX99NV3OsXPnLV
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.