𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Menene Hukuncin Cinye Naman Layya Duka, Ko Sadaka Da shi Gaba Ɗaya?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Nassoshi Na shari'a sunyi nuni akan wajabcin yin sadaka da Wani abu na naman layyah, koda kaɗan ne, Allah maɗaukakin sarki ya ce: (Kuci daka naman layyarku, ku ciyar da Talakan daya kame bai roqa ba, da talakan daya roqa saboda buqata, saboda haka Allah ya Yassare muku ita danku zama masu godiya) Suraul Hajji aya ta (36).
Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: ( Kuci naman layya, ku ajiye, kuyi sadaka) Muslim (1971).
Malaman da Suka ce yin sadaka da Naman layya wajibine sune: Shafi'iyyah da Hanabila, Itace sahihiyar Magana Azahirin nassosin shari'a.
Wajibine sadaka da wani abu na naman wanda sunan sadaka zai gaskatu akansa, domin manufa shine yalwatawa miskinai,
Abisa Wannan idan mutum ya cinye naman layyar sa, duka wajibine ya siya yayi sadakar,
Rauzatul dhalibeen da Umdatul mufteen (3/223).
Kamar yanda Marudy ya faɗa acikin "Al'insaaf (6/491).
Kamar yanda Buhty yafada acikin kashshaful Qina'i (7/444).
Kamar Yanda Shaik Usaimeen ya bayyana acikin Maj-mu'u fatawa dinsa (25/132)
Malamai Sunyi Saɓani akan wajabcin cin wani abu daga cikin Naman layya, Jamhur ɗin malamai suna ganin cin wani Abu na naman layya mustahabbine, ba dole bane, wannan shine fatawar Manyan Mazhabobinnan guda huɗu.
Wasu sun tafi akan wajabcin cin wani Abu daka cikin naman layya koda kaɗan ne, saboda zahirin nassosin shari'a da sukayi Umarni akai.
Nawawi ya ce: Cin naman layya mustahabbine ba dole bane, shine mazhabar mu da Malamai gaba ɗaya, sai Abunda aka hakaito daka wasu magabata na wajabcin cin naman, saboda zahirin hadisin dayayi Umarni aci wani abu daga layya, da faɗin Allah maɗaukakin Sarki ( Kuci daka naman layya) Jamhur ɗin malamai sun dora wannan umarni akan halacci da Mustahabbanci,
Sharhin Sahihu Muslim (13/131).
Ibnu qudama ya ce: da Mutum zaiyi sadaka da naman layya gaba ɗaya, ko mafi yawan naman, ya halatta.
Al-mugni (13/380).
Idan ka yanka raguna da yawa, ko wanne saika debi wani abu daka namansa kayi Sadaka da shi.
da Zaka yanka raguna goma ko akuyoyi ko tumaki, ko wanne daka cikinsu saika debi namansa kayi Sadaka da shi, mustahabbine kowacce dabba kaci wani Abu na naman dukkan dabbobin daka yanka.
Domin kowacce layya cin gashin kanta take..
Shi yasa da Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya soke abun hadayarsa sai yayi umarni a debo masa wani kaso daka naman kowacce raquma.
Jabir ɗan Abdullahi Allah ya qara musu yarda ya ce: Sai muka nufi Abbatuwa Annabi ya Soke raquma talatin da Uku da hannunsa, sai ya bawa Aliyu ya yanka Abunda yayi Saura.
Sannan yayi Umarni akawo masa daka naman kowacce sai aka sanya atukunya aka dafa masa yaci namansu, yasha romonsu.
Mualim (1218).
Wannan yana nuna kowacce dabbar layya da'aka yanka tana da hukunci nata ita kaɗai.
saboda hakane yayi Umarni akawo masa wani Abu daka kowacce taguwa.
Nawawi ya ce: acikin wannan akwai mustahabbancin cin hadayar nafila, da layyya.
Malamai Suka ce: cin naman kowacce dabba daka yanka sunnah ne, cin yanka ɗaya na kowacce dabba akwai wadatarwa, ka sanya atukunya don kowacce ya zama akwai romon nata naman.
Sharhin Muslim (8/192).
Wallahu A'alamu.
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.