𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Idan Mace tana Sallah tare da Jariri abayanta sai Yaron yayi mata Kashi ko Fitsari, menene hukuncin Sallarta, Shin zataci gabane dayin Sallar ahaka ko kuma zata yanke tane?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Kamar yadda yake abu sananne a Shari'a cewa daga cikin Sharuɗɗan ingancin Sallāh wājibine yakasance an nisanci dukkan wata najasa dake gangan jikin Mai-Sallāh ko jikin tufāfinsa ko kuma shimfiɗar da zaiyi Sallar akanta, dan haka kenan duk wanda yayi Sallāh da najasa atāre da shi ko kuma yaɗauki Ƙaramin-Yāro, kamar Mace ta goyi Jārīrī tana cikin Sallāh kawai sai yayi mata Kāshi ko Fitsāri, Mālamai suka ce nantake Sallar Mutum tā ɓāci, domin Fitsārin-Jārīrī da Kāshinsa dukkansu najasane, to amma Saidai Sallār wadda taɗauki Yāro-Ƙarami tāna ɓācine idan yakasance dāmā tāsan cewa da najasa ajikin Yāron amma ta ɗauke shi tayi Sallāh da shi ahaka, ko kuma yakasance Mace tana cikin yin Sallārne sai Yāron yayi mata Kāshi ko Fitsāri:
Amma idan yakasance asali dāmā Mutum baisan cewa da najasa ajikin Yāronba ko kuma yāsan da najasar amma saidai yāmanta da ita, dan haka sai yaɗauki Yāron yayi Sallāh da shi to anan sai Mālamai suka ce Sallārsa tā inganta, domin da yawa daga cikin Mālamai suka ce dukkan wanda yayi Sallāh da najasa ajikinsa amma baisan da itaba ko kuma yāsan da ita ɗin amma yāriga yāmanta, anan sai waɗansu Mālaman suka ce dolene sai yāsake wannan Sallār, to amma magana mafi inganci Sallārsa tāyi, daga cikin hujjar Mālaman da suka ce Sallārsa tāyi akwai wannan Hadisi, na Mαиzoи Aʟʟαн(ﷺ) wanda yanā cikin yin Sallāh da tākalminsa sai Sahabbai suka ga yācire tākalmin daga ƙafarsa, suma duk sai suka cire nasu, bāyan an-idar da Sallāh sai Aηηαвι(ﷺ) ya gaya musu cewa Malā'ika-Jibril ne yazo ya ba shi labarin cewa akwai najasa ajikin takalmin nasa shine dalilin da ya sa ya cire shi:
Sai Mālamai suka ce inda ace Sallāh tana iya ɓāci akan wanda baisan da najasa ajikinsaba to lallaai da anga Mαиzoи Aʟʟαн(ﷺ) yāsake Sallāh, amma sai yaci gaba dayin Sallārsa ahaka, dan haka kenan idan Mace tana cikin Sallāh sai Yāro yayi mata Fitsāri ko Kāshi, to idan har zai yiwu ta iya ajje Yāron agefe ko kuma tajanye wannan tufafin daga jikinta idan akwai wani tufafin ajikinta me tsarki wanda zāta iya cigaba da Sallār da shi, to zāta iyayin hakan bā tāreda tā yanke Sallārtaba, ammafa idan najasar bata riga tā rātsa jikintaba, idankuwa har tashiga jikinta sosai to saidai tayanke Sallār taje tawanke wajen da najasar ta taɓa:
Doмυп пεмαп ƙαяıп вαчαпı sαı αdυвα шαɗαппαп ʟıтαттαғαı καмαя нακα:
"اَلْـمَـجْـمُـوعُ" (3/157)
"ألإنْــصَــاف" (1/486)
"كـشـاف الـقـنـاع" (1/289)
"المغني لإبن قدامة" (1/403)
шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ
AMSAWA
Mυѕтαρнα Uѕмαи
08032531505
Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/BSA30hdZD7V3WSJF8WVwUj
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.