Ticker

6/recent/ticker-posts

Mai Janaba Da Mai Haila Taimama Za Su Yi Idan Suka Rasa Ruwan Wanka.

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Malam da fatan an wuni lafiya, Allah ya kara Nisan kwana mai anfani. Malam tambayata ita ce "Ni ce ina jinin al'ada sai jinin ya dauke kamar karfe 1:00 na rana, to malam gidan da nake ba ruwa ko kaɗan ga shi kuma lokacin sallah zai wuce kawai sai na sayi pure water guda ɗaya na yi alwala da shi na yi sallah, sai wajen la'asar na samu ruwa da na yi wankan tsarki lokacin sallar la'asar ya yi kawai sai na yi sallar la'asar. To malam ya matsayin sallar azahar di na take?

Allah ya karawa malam sani ina bukatar Karin bayani. Na gode

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salám, ‘yar uwa idan mai janaba ko mai hailar da jini ya ɗauke mata suka yi nufin wankan tsarki sai ba su sami ruwan wanka ba, to ba alwala za su yi ba, abin da za su yi shi ne taimama, su yi sallarsu da ita. Haka nan shi ma wanda yake halin tafiya a inda ba ruwan da zai yi alwala, kuma ya yi nufin yin sallah, haka nan maras lafiyar da ba zai iya taɓa ruwa ba saboda wannan rashin lafiyar tasa, dukkansu hukuncinsu shi ne su yi taimama a maimakon wanka ko alwala. Kamar yadda aya ta 6 da ke suratul Má'ida ta tabbatar.

A nan taimamar tana matsayin tamkar alwala ce, kuma tana matsayin tamkar wanka ne wurin ɗauke hadasi. Kuma duk ibadar da suka yi da wannan taimama ko da sun sami ruwa sun yi wanka, to ba za su sake ibadojin da suka yi a baya da taimamar nan ba. Abin da za su yi kawai a lokacin da suka sami ruwa shi ne su yi wanka saboda ibadojinsu na gaba.

Saboda haka ‘yar uwa sallar da kika yi da waccan alwalar a lokacin da babu ruwan wankan tsarki na hailar da ta same ki ba ta inganta ba, saboda ba alwala aka ce mai hailar da ta rasa ruwan wanka ta yi ba. Yanzu za ki sake waccan sallar da kika yi ne saboda taimama za ki yi a lokacin ba alwala ba.

Allah S.W.T ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Fb6ƙgYPXfEeHb8CD1SWAkK

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments