Ticker

6/recent/ticker-posts

INA SHAN WAHALA WAJEN BIYA MIJINA BUƘATA

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu Alaikum malam inashan wahala wajen biyawa mijina bukata nikuma har nagaji da neman magani to zan iya neman hutu intafi gida? ko hakuri zanyi haka kaddarata take?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumussalam Warahamatullahi wabarkatuhu.

Wato matsalar bushewan gabane shike kawo rashin gamsuwa Ma'ana de rashin ni'ima wanda mata da yawa ke fama da wannan matsalan.

baidace ki koma gida ba, tunda ke ce da problem! dan haka komawan kaman kintonawa kanki asirine, dan irin haka zakiga mijin ma kansa haquri yakeyi, bawai dan yana jin dadiba 

Kuma irin haka mace ko tana magani inba tana tare da mijinba bazata taɓa fahimtar ingancin maganinba.

_Gasude kaman haka ⤵

Kicire kunya dan inbayayi ki gaya mishi ya dinga wasa da ke sosai ta yanda se kinji kaman zaki kawo kafin yafara saduwa da ke

1. ki dinga yawan sa zuma agabanki kuma kina shafa man zaitun, Kuma kina sha safe da yamma.

2. Ko Kisamu ruwan albasa, mazar kwaila Seki dafasu a waje guda ki dinga sha qaramar kofi.

3. Ki nemi garin minjirya ki haɗa da peak milk seki dafasu zakiga ya haɗu a dunkule se ki dinga ci.

4. Ko Ki samu sassaken baure, kanunfi, zuma, citta, mazarkwaila.

Dafarko zakisa sassaken baure a wuta kibari ya tafasa har se ya canza kala saiki sauke ruwan ki tace ki daka kanun fari da citta ya yi laushi seki zuba aciki kisa zuma da mazarkwaila sannan kisake mayar da shi kan wutan idan ya nuna sosai zakiji yana qamshi saiki sauke ki ajiye kina sha sau biyu arana.

5. Ko Ki samu furen zogale ki haɗa da "yayan da kuma gyanyen kisa a inuwa inya bushe seki daka su kisamu zuma ko milk kina sha safe da yamma.

6. Kuma ki nemi man kadanya ki haɗa da man shanu ki kwaba kina shafawa agabanki inyayi kaman awa ɗaya ki wanke da ruwan zafi.

7. Zaki iya samun ita zogalen danye ki haɗa da cucumber ki markadasu a blender saiki tace kisa peak milk da zuma kisha kuma ki dan digashi agabanki

8. Ko ki samu gero ki surfa ki haɗa da mazar kwaila da kanunfari da man shanu ki saka ruwa ki dora akan wuta ya dafu sosai saiki tace ruwan kisha.

Shi wannan ma yafi saurin kawo ni'ima. 

Allah ta'ala yasa mudace.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IQUc0RxgCwA3JFiEKl8j5E

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments