HUKUNCIN FITSARIN ƘANANAN YARA

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

    malam menene hukuncin tufafin da karamin yaro ya yi maka fitsari mutum zai yayyafa ruwane ko sai ya wanke , kuma shin akwai bambamcin hukuncin tsakanin fitsarin yaro namiji da mace? Allah ya bada ikon amsawa.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Shi fitsarin Qananan yara ya rabu ne zuwa kashi biyu. Idan fitsarin yarinya jaririya mace ne, to daidai yake da na babban mutum. wajibi sai an wankeshi.

    Idan kuma fitsarin Qaramin yaro ne jariri, to yayyafa ruwa kawai ya wadatar. Amma Malaman Fiqhu sun ce wannan hukuncin ya keɓanci yaron da bai fara cin abinci bane. Idan ya riga ya fara cin abinci, to hukuncin fitsarinsa kamar na babban mutum ne.

    Hujjah anan ita ce hadisin da Bukhary da Muslim suka ruwaito daga Sayyidah Ummu Qays bintu Mihsaan (ra) ta kawo wani yaronta wanda bai fara cin abinci ba, ta kawoshi wajen Manzon Allah ﷺ

    Manzon Allah ﷺ ya karbeshi ya dorashi akan cinyarsa mai albarka, Sai yaron ya yi masa fitsari. Sai Manzon Allah ﷺ yasa aka kawo masa ruwa ya yayyafa a tufafinsa, bai wankeshi ba.

    (aduba Sahihul Bukhary hadisi na 223, Sahihu Muslim hadisi na 287).


    Akwai wani hadisin ma daga Sayyiduna Aliyu bn Abi Talib (ra) daga Manzon Allah ﷺ yana cewa : "KUYI YAYYAFI GA FITSARIN JARIRI QARAMI, KUMA KU WANKE FUTSARIN YARINYA QARAMA".

    (Aduba Sunanut Tirmiziy hadisi na 610, Ibnu Maajah hadisi na 525).

    Imam Qataadah yace Wannan hukuncinsu kenan kafin su fara cin abinci. amma idan har sun fara cin abinci to Wajibi ne awanke fitsarin kowannensu.

    Don Qarin bayani aduba Tuhfatul Maurood shafi na 190).


    WALLAHU A'ALAM.


    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/K7RkQRMf2b57l3UENoJ1Or

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.