Ticker

6/recent/ticker-posts

HUKUNCIN YIN LAYYA DA DAN-DAƘAƘƘEN RAGO

 𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya dawwama akan yin layya da dan-da ƙaƙƙen rago, shin ya halatta a yiwa rago dan-daƙa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد لله سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

Babu laifi a dan-daƙe rago ko taure, idan akwai maslaha ingantacciya ta dan-daƙewar, shi ne mazhabar jamhurin malamai.

Ba'a ruwaito A sunnah Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yana mu'amala kebantacciya da dabba wacce aka dan-daƙe ba, ko wasu hukunce hukunce da suka kebanci dabbar da aka dan-daƙeba, Maƙurar Abunda za'ace shi ne ya yi layyah da raguna wadanda akaiwa dan-daƙa, wannan yana nuna shar'antuwar dan-daƙe dabba..

Shar'antuwar dan-daƙe dabba ta wani bangaren, da shar'antuwar yin layya da dabbar da aka dan-daƙe, ta wata fuskar.

Imamu Ahmad ya ruwaito hadisi (23348) daka Abiy rafi'i ya ce: ( Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya yi layya da raguna kosassu, manya dan-daƙaƙƙu) Albani ya Ingantashi acikin Irwa'ul galeel (4/360).

Malamai Sukace: Saboda naman dan-daƙaƙƙen rago yafi dadi.

Amma bai halatta ayi layya da rago ko tauren da aka yankewa azza kari ba.

Annabi Sallallahu Alaihi wasallam Bai dawwama akan zabar dan-daƙaƙƙen rago a layya ba, yana zabar wanda ba'a dan-daƙe ba yai layya dashi.

Abu dauda ya ruwaito hadisi (2796) da Turmuzi (1496) daka Abiy sa'id ya ce: ( Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam ya kasance yana yin layya da rago mai ƙaho wanda ba'a dan-daƙe ba).

Albani ya Ingantashi.

Ibnu Abdul barri ya ce: Rago mai ƙaho wanda ba'a dan-daƙe ba, shi yafi falala wajan yin layya, awajan malik da Wasu malamai masu yawa.

Al'listizkaar (5/220)

Wasu malamai sun rinjayar da rago dan-daƙaƙƙe saboda dadin namansa.

Wasu malaman kuma sun dai-dai tasu wajan falala basu fi-fita wani akan wani ba, kamar yanda shaukani ya fada acikin Nailul Audããr (5/142).

Abunda yafi kusa da dai-dai shi ne: Wanda yafi koshi, da yawan nama, da kamalar halitta, yafi kyawun gani, shi ne yafi falala wajan layya kamar yanda yazo acikin Ahkamul za kah (2/229)..

Idan Wanda ba'a dan-daƙe ba, shi ne yafi girma da dadin nama to shi ne yafi falala wajan layya.

Ida Dan-daƙaƙƙene yafi girma namansa yafi, to shi ne yafi falala.

Wallahu A'alamu.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

 

 

Post a Comment

0 Comments