Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Tsotsan Al'aurar Juna Tsakanin Ma'aurata Yayin Jima'i

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum. Yaya matsayin tsotsan alaurar juna tsakanin maaurata yayin jima'i? ko Yaya amsar take a taimaka min da ayar Alƙur'ani Domin inyi amfani dasu Na gamsar da mijina. Nagode.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikum salam. Hakika Ayoyi sun tabba a Ƙur'ani waɗanda suke nuna halaccin jin daɗin juna tsakanin ma'aurata Allah yake cewa:

ﻫﻦ ﻟﺒﺎﺱ ﻟﻜﻢ ﻭﺃﻧﺘﻢ ﻟﺒﺎﺱ ﻟﻬﻦ ‏)

[SU (MATANNAN) SUTURA NE AGAREKU KUMA KUMA SUTURA NE AGARESU]

Wani wajan kuma Allah ya ce:

ﻧﺴﺎﺅﻛﻢ ﺣﺮﺙ ﻟﻜﻢﻓﺄﺗﻮﺍ ﺣﺮﺛﻜﻢ ﺃﻧﻰﺷﺌﺘﻢ

[MATAYANKU GONAKINKU NE KUJEWA GONAKINKU TA INDA KUKESO]

Waɗannan ayoyin suna nuni gamida goyan bayan ma'aurata suji daɗin junan su ta inda suke so, to sede awani wajan Allah yace KARKU WUCE IYAKA wato karku ketare haddi.

Misalin ketare haddi shi ne miji yajewa matarsa ta dubura ko alokacin da take jinin haila sannan ketare iyaka yakan iya ɗaukan yin dukkanin abinda yake haramun.

To anan gameda tambayanki se mu duba mugani inda manzan Allah ﷺ yace idan zaku jewa matayanku Ku aika da Ɗan sako, Ɗan sako anan shi ne dukkan yan wasannin da akeyi gabanin jima'i, To anan se muce kenan ya halasta yan wasannin da akeyi sede idan awannan lokacin haramun ze iya shigowa se abi ta wani hanya misalin awannan halin na wasannin miji /komata ze iya sa al'auaran Ɗan uwansa abaki MAZIYI ZE IYA FITOWA KUMA SHI BA LALLAI BANE KASAN FITIWANSA SEDE KAGA YA FITO to anan idan har ka sanya Al'auran matanka/ ko kijinki abaki alhalin maziyi ya fito kaga ka aikata haramun (HARAMUN YA SHIGO CIKI) domin kuwa MAZIYI NAJASA NE kuma sanya shi abaki ze gadar da shansa Wanda hakan haramun ne.

Dan haka tunda sanya najasa abaki haramun ne kuma tunda maziyi ze iya fita awannan halin ba tare da sanninku ba har a iya hadiyeshi to barinsa shi yafi, a yi wasannin da hannu.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Tambaya Da Amsa Abisa Alkur'ani Da Sunnah. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments