Hukuncin Wanda Yake Taɓa Jikin Budurwarsa

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Menene Hukuncin Wanda Yake Taɓa Budurwarsa Har Tana Yanke Masa Farce Da Sunan Soyayya?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    الحمد لله.

    Zina bawai ana nufin zinar farji ita ce kaɗai zina ba, akwai zinar hannu shi ne mutum yadunga taɓa jikin wacce take muharrama a gare shi, da zinar ido shi ne kallon muharrama, duk da zinar farji ita ce ake tsaidawa mutum haddi a kanta.

    Daka Abu huraira Allah yakara yarda dashi daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: (Allah yarubutuwa ɗan adam kason laifinsa na zina, zai riskeshi babu makawa, zinar ido kallo, zinar baki magana, zinar kunne jin zance, zinar hannu taɓawa, zuciya ita take riyawa farji kuma yagasgata ko ya karyata. Bukhari (5889) da Muslim (2657)

    Hadisi ya tabbata wanda manzon Allah ﷺ ya ce: (Abuga Narkakkiyar kusar wuta ta bakin karfe akan ɗayanku shi yafi masa alkhairi akan ya shafi jikin macen da bata hallata a gare shi ba ). Albany yace hadisine ingantacce a cikin sahihul jami’ul kabeer (5045).

    Bai halatta ga musulmi ya taɓa jikin budurwarsa ba kamar yi mata kiss, ko keɓancewa da ita, ko rungumar juna, ko kallo dukkansu haramun ne suna kaiwa zuwaga ga Alfasha babba ita ce Zina.

    Allah madaukakin sarki ya ce:

    ﻭﻻ ﺗﻘﺮﺑﻮﺍ ﺍﻟﺰﻧﻰ ﺇﻧﻪ ﻛﺎﻥ ﻓﺎﺣﺸﺔ ﻭﺳﺎﺀ ﺳﺒﻴﻼً {ﺍﻹﺳﺮﺍﺀ/32}

    Kada ku kusanci zina domin alfashace kuma mummunar hanyace mai saurin fatattaka ɗan adam.

    Kallo na haramun bom💥ne daka cikin bama-baman Shaiɗan, waɗanda suke kai wanda yakebinsu zuwa ramuna na halaƙa, ko da dafarko bai nufi kaiwa ga aikin halaƙarba shiyasa Allah madaukakin sarki ya ce:

    ﻗﻞﻟﻠﻤﺆﻣﻨﻴﻦ ﻳﻐﻀﻮﺍ ﻣﻦ ﺃﺑﺼﺎﺭﻫﻢ ﻭﻳﺤﻔﻈﻮﺍﻓﺮﻭﺟﻬﻢ ﺫﻟﻚ ﺃﺯﻛﻰ ﻟﻬﻢ ﺇﻥ ﺍﻟﻠﻪ ﺧﺒﻴﺮ ﺑﻤﺎ ﻳﺼﻨﻌﻮﻥ . ﻭﻗﻞ ﻟﻠﻤﺆﻣﻨﺎﺕ ﻳﻐﻀﻀﻦ ﻣﻦ ﺃﺑﺼﺎﺭﻫﻦ ﻭﻳﺤﻔﻈﻦ ﻓﺮﻭﺟﻬﻦ { ﺍﻟﻨﻮﺭ / 30-30.

    Ya manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam kafadawa muminai su runtse ganinsu sukiyaye farjinsu, wannan shi ne yafi tsarki agaresu, tabbas Allah mai bada labarine akan abun da kuke aikatawa, kace da muminai mata suruntse ganinsu su kiyaye farjinsu.

    Kalura kanutsu kaga yanda Allah yahada rintse gani dakiyaye farji a cikin waɗannan ayoyin. Dubi yanda yafara da runtse gani kafin kiyaye farji, domin gani shi ne jagoran farji shi ne ke kai masa sako.

    Ibnul ƙayyeem rahimahullahu ya ce: Tsoratarwa akan dukkan wani aikin saɓo bashi da haddi ko kaffara, ayyukan saɓo nau'i ukune, nau'in dayake akwai haddi amma babu kaffara, akwai nau'in dayake akwai kaffara a cikinsa amma babu haddi, akwai nau'inda bashi da kaffara kuma babu haddi,

    1. Nafarko: kamar sata da shan giya, da zina da kazafi.

    2. Nabiyu: kamar jima'i da rana a watan Ramadan da jima'i yayinda mutum yadaura ihramin aikin hajji.

    3 Na uku: kamar saduwar da baiwar da mutum sukai tarayya da wani wajan mallakarta, da sumbatar macenda take muharramarsa, da keɓancewa da ita, da shiga banɗaki ba tare da mayafi ko wani abu dazai rufew mutum Al'aurarsa ba yayin fitowa daka banɗakin, da cin naman mushe, da shan jini da cin naman alade, dasauransu duba I'ilamul muwaƙƙe'een (2/77)

    Wajibi ne akan duk wanda aka jarabta dawani abu cikinsu yatuba zuwa ga Allah maɗaukakin sarki, domin duk wanda yatuba Allah zai karɓi tubansa, mai tuba daka zunubai kamar wanda bashida zunubinne kwata-kwata.

    Mafi girman abun da zai kiyaye mutum daka ayyukan saɓo shi ne kiyaye salloli biyar, Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: (Salloli guda biyar da juma'a zuwa wata juma'ar da Ramaḍān zuwa wani Ramaḍān ɗin yana kan-kare abun dake tsakaninsu na zunubai idan mutum yanisanci manyan laifuka) Muslim (1/209)

    WALLAHU A'ALAMU.

    Zauren Tambaya da Amsa Abisa fahimtar magabata Nakwarai. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.