Banbancin Sallar Farilla Da Ta Nafila

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu Alaikum. Dan Allah malam menene banbancin sallar farilla dana nafila? Sannan malam dan Allah wai a cikin sallah wanda akeyi a baiyanane kawai ake karanta surah bayan fatiha sauran na bayan kuma ba a yi??

    Allah ya kara ilimi.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa'alaikumus Salaam Warahmatallahi Wabarkatahu

    1- Bambanci tsakanin sallar Farilla da na Nafila shi ne;

    Ita sallar farilla sallah ce da Allah (ﷻ) ya ke wajabtawa a kan bãwa, Wanda idan mutum ya bar ta da gan-gan za a iya azabtar da shi. Kuma mutum ba ya da zaɓi a kanta, dole ne a yi yanda ta zo, wato mutum ba zai ce ze yi sallar asuba raka'a huɗu ba, ko ya yi raka'a biyar a sallar Zuhr da gan-gan, mutum ba ya da ikon yin hakan, ko ya yi Allah ba zai amsa ba.

    Ita kuwa sallar Nafila sallace da mutum ya ga damar yi a karan kansa don neman lada a wajen Ubangiji, wanda idan mutum bai yi ta ba, baya da wani zunubi a wajen Allah. Kuma mutum na da zaɓin ya yi raka'o'in da ya so, imma biyu, huɗu, shida ko Takwas, har zuwa iya adadin da ya tabbata Manzon Allah (ﷺ) ba ya karawa daga hakan.

    2- Kwarai kuwa, raka'o'in da ake yin karatu a bayyane kamar Isha'i, to a biyun farko za a karanta Fatiha da Surah amma a biyun karshe Fatiha kawai ake karantawa. Haka ake yi a duk sauran sallolin amma banda Subhi saboda ita raka'a biyu ne kuma duka a bayyane ake yi.

    WALLAHU A'ALAM.

    🏿Ayyoub Mouser Giwa.

    08166650256.

    Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://chat.whatsapp.com/DSdbBS8RZVoIKYG5exOuZE

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.