Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Shiga Bayi Da Wayar Dake Ɗauke Da Alkur'ani

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

اَلسَلامُ عَلَيْكُم وَرَحْمَةُ اَللهِ وَبَرَكاتُهُ

Mene ne hukuncin shiga bayi da na’ura ko wayar da ke ɗauke da Al-Kur’ani?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

وعليكم السلام ورحمه الله وبركاته

Matsalar shiga bayi da na’ura ko wayar da ke ɗauke da Al-Kur’ani ta kasu gida biyu:

1 – Makaruhi ne a shiga da wayar ko na’urar da ke ɗauke da Al-Kur’ani idan gilashin na’urar/wayar na buɗe da Al-Kur’anin kuma ana ganinsa a gilashin (screen).

Malamai sun ce yin hakan kamar shiga da Al-Kur’ani ne bayi. Kuma haka ya saɓawa shari’ah, hasilima wasu malam sun haramta kai tsaye, domin rashin dacewarsa.

2 – Kauli na biyu shi ne halacci (Halal) idan gilashin wayar baya nuna (displaying the text of Ƙur’an) ayoyin Al-Kur’ani a fili. Ko kuma wayar na kashe (swich off), ko ta yi lumm da duhu ba a ganin komai na Al-Kur’ani a gilashinta. To, idan gilashin wayar bai nuna Al-Kur’ani ba, babu komai.

Sharadi ne sai mai tsarki zai ɗauki Al-Kur’ani, to shin tsarki sharadi ne game da Al-Kur’anin na’ura (kamar waya)?

Mafi yawan malamai na ganin cewa bai dace musulmi ya buɗe Al-Kur’anin wayarsa ba sai yanada tsarki (ma’ana babu haila ko janaba), domin hakan kamar ɗaukar Al-Kur’ani ne cikkake. Amma wasu malamai suna ganin babu komai matukar mutum ba zai taɓa gilashin (screen) da ke nuna rubutun ba.

WALLAHU A'ALAM

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/K7RkƘRMf2b57l3UENoJ1Or

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments