Ticker

6/recent/ticker-posts

Mu San Tauhidi 05 - Mallaka Ta Haram Data Halal

Da yawa daga cikin ‘yan mata sukanso mallake samarinsu ta hanyar zuwa gurin malamai da yin amfani da ayoyin ALLAH wato sihiri badan komai ba, sai don su zama mazan aure a garesu, sannan akwai wasu lalatattu daga cikinsu waɗanda suke mallake maza saboda abin duniya kawai badan aure ba.

 Haka kuma akwai da yawa daga cikin maza masu irin wannan aƙidar suma, amma wasu daga cikin mazan suna mallake matan ne don suyi lalata dasu badan su auresu ba, kaɗan ne suke auran waɗanda suka mallake.

 Gaskiyar magana shi sihiri ko da da ayar ALLAH akayishi haramun ne, kuma yana kai mutum ga kafurci, domin ALLAH ya kira mai sihiri da kafiri.

 Sannan kuma shi sihiri akwai lokacin da yake daina aiki musammanma na mallaka, yana saurin karyewa, kuma idan ya daina aiki ana samun tsana mai ƙarfi ta shigo tsakani.

 Don haka maza da mata kuji tsoron ALLAH kudaina yiwa junanku sihiri, domin kada mutum ya mutu yana cikin masu kafircewa ALLAH.

 Mallaka ta halal kuwa ita ana samunta ne ta hanyar ɗabi'u nagari, kyautata kalamai, magana mai daɗi, girmama ita wacce akeso da kuma girmama shi wanda akeso.

 Ana mallake juna ta hanyar kyautuka da kuma gaskiya da amana, ana mallake juna ta hanyar kalamai masu daɗi, tare da girmana iyayen juna, kuma ana mallake juna ta hanyar haƙuri da juna da kuma yiwa juna uzuri.

 Mace da mijinta ko saurayi da buduruwa indai sunbi irin wannan hanya in sha ALLAH ko shaiɗan ba zai yi tasiri a tsakaninsu ba.

 Saboda haka mudaina wahalar da kanmu na zuwa gurin malamai suna karɓe mana kuɗaɗe suna kuma aikata shirka, mu dasu duk muje mu haɗu da azabar ALLAH.

 Mubi hanyar da shari'ah ta tanada da haka ne za mu mallaki juna cikin sauƙi kuma ga farin cikin dawwamamme.

 Ta waɗannan hanyoyine ko da bayan mutuwar abokin rayuwa, babu abin da zai rinƙa fita daga bakin ɗayan sai fata na alkhairi.

ALLAH ka bamu ikon aiki da abin da muka karanta.

ALLAH ka gafarta mana zunubanmu baki ɗayanmu Ameen.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments