Hukunci Yawaita Hamma A cikin Sallah.

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Mene ne Hukunci Yawaita Hamma A cikin Sallah.

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    الحمد لله رب العالميين.

    Allah ya yabi bayinsa muminai dacewa sune masu nutsuwa da kushu'i a cikin sallar su,

    (الذين هم في صلاتهم خاشعون

    Sune waɗanda a cikin sallar su, suna tsoran Allah.

    Annabi sallallahu Alaihi wasallam ya ambaci cewa Shaiɗan yana kai kawo dan daukewa mutum hankali a cikin sallarsa, Allah kuma ya jarrabi muminan dahakan, hanyar da Shaiɗan yake daukewa mutum hankali asallarsa shi ne ya zo yakawo masa tunanin abubuwan duniya, dasanya masa kokwanto a cikin sallar sa, daka ciki akwai tursasawa mumini hamma a cikin sallarsa, Annabi sallallahu Alaihi wasallam yabada labari cewa hamma daka Shaiɗan ce, kuma ya umarcemu damu mayar da hamma gwar-gwadon yanda muka samu hali, idan kuma hammar taci karfinmu tomu sanya hannayen mu akan bakunanmu, ga wasu daka cikin nassoshin da mutum zai yi idan hamma ta gallabeshi a cikin sallar sa.

    Daka abu sa'idul kudri yardar Allah takara tabbata a gare shi ya ce: manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam ya ce: (Idan dayanku yai hamma awata ruyawar a cikin salla toya kame hammar karyayita gwar-gwadon ikonsa domin Shaiɗan yana shiga bakin mutum idan yai hamma) Muslim (2995).

    Daka Abu huraira yardar Allah takara tabbata a gare shi daka Annabi sallallahu Alaihi wasallam ya ce:(hamma daka Shaiɗan ne, idan dayanku yai hamma yamar dashi gwar-gwadon yanda zai iya, domin idan dayanku yai hamma yace " Ha" sai Shaiɗan yai dariya, ) Bukhari (3115) da muslmi (2994).

    Ibnu hajar rahimahulla ya ce:

    An jingina hamma zuwa Shaiɗan ne, saboda yana san yaga mutum yana hamma, domin fuskar mutum takan canja yayinda ya yi hamma sai Shaiɗan yai dariya, bawai ana nufin Shaiɗan ne ya yi hammar ba.

    Ibnul arabi ya ce: Ana jingina dukkan wani mugun aiki zuwa Shaiɗan ne domin tahanyarsa aikin ke faruwa, haka dukkan wani aikin alkahiri kyakkyawa ana jinginashi ga Allah saboda dataimakonsa yake sanuwa, hamma tana zuwa saboda cika ciki, kasala tana wanzuwa saboda hamma, hakan nafaruwa dataimakon Shaiɗan, Attishawa kuma tana faruwa saboda karanta abunci, kuma jiki yakan samu nishadi da karsashi saboda dataimakon Allah take samuwa,.

    Imamun Nawawi rahimahulla ya ce: An danganta hamma zuwa ga Shaiɗan ne, saboda yana janyowa jiki sha'awa, kuma yana faruwa saboda jiki yai nauyi dacika shi da abunci, abun nufi shi ne tsoratarwa daka abubuwan dasuke haifar da hammar, shi ne cika ciki ta wajan ci ko sha.

    Da Annabi sallallahu Alaihi wasallam ya ce: Idan dayanku ya yi hamma yamar da ita gwar-gwadon iyawarsa) ana nufin ya yi riko da abubuwan dasuke hana yinta, bawai ana nufin mutum yahana zuwanta ba, domin idan tafaru ba a iya mayar da ita ahakika, wasu sukace: (idan yai hamma) ana nufin idan yai nufin yin hamma.

    Abun da ake nufi da fadinsa a cikin hadisin muslim (Shaiɗan yana shiga) zai dauki ma'anar shiga tahakika, saboda Shaiɗan yana gudana ajikin ɗan adam kamar yanda jini ke wakana ajikinsa, saidai bashi dawani abu dazai iya yiwa mutum matukar yana cikin ambaton Allah, wanda yai hamma ahalinda baya cikin ambaton Allah Shaiɗan zai iya shiga bakinsa shiga ta hakika.

    Zai iya ɗaukar kuma an ambaci cewa Shaiɗan zai shiga bakinsa, ana nufin zai samu dama a kansa, domin sha'anin abun da yashiga cikin wani shi ne yasamu dama a kansa.

    Umarni dacewa mutum yasanya hannu, ana nufin idan yai hammar ya sa hannu yarufe bakinsa, da makamantansa.

    Yana daka cikin ma'anar sanya hannu abakinsa sanya tufafi da abun da zai iya zama manufar da'akeso ta rufe baki, ana ayyana hannune idan babu abun da za a maida hammar da shi babu banbanci tsakanin wanda yake sallah dawanda yake wajen sallah, saidai umarnin zaifi karfi lokacin da mutum ke cikin sallah, hani da'akai kada mai sallah ya sanya hannunsa abakinsa, anyi togaciya banda lokacinda ya yi hamma.

     Yana daka abun da aka umarci mai sallah dayi idan hamma ta zo masa yana cikin sallah, ya dena karatu, har sai yagama hammar dan kada ya canja tsarin karatu.

    Fat hu baari (10/612).

    Imamun Nawawi rahimahullah ya ce: " idan mutum yai hamma a cikin sallah ko awajan sallah mustahabbine yasanya hannunsa akan bakinsa, an karhantawa mai sallah yasanya hannunsa abakinsa, idan ba hamma damaka mantantaa ya yi ba. Al'azkarr (346).

    Saboda haka hukuncin hamma asallah bawani abu bane, illah kawai duk lokacin da mutum zai fara sallah, yafara da kwarin jiki da nishadi yasani Shaiɗan makiyinsane, yadaukeshi amatsayin mikiyi, duk lokacin da hamma ta zo mai yai iyakacin kokarinsa wajan maida ita, idan taci karfinsa ya sa hannunsa akan bakinsa.

    Sannan ya nisanci ababen dake haifar da hammar kamar cin abunci sosai da cika ciki da abubuwa barkatai

     WALLAHU A'ALAM.

    سبحانك اللهم لا علم لنا إلا ما علمتنا إنك أنت العليم الحكيم.

    Tambaya da Amsa Abisa fahimtar magabata Nakwarai

    +2348123432272

    +2348163731622.

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.