KaÉ—an Daga Cikin Gudunmawar Noams Chomsky A Fagen Harshe
Abubakar Sarki ASUK
HAIHUWARSA A TAƘAICE:
An haifi Abram Noam Chomsky a
Philadelphia ranar 7 ga Disamba, 1928. Mashahurin Farfesa na Linguistics a
Cibiyar Fasaha ta Massachusetts, masanin ilimin sadarwa, an gane shi a matsayin
wanda ya kafa nahawu mai canzawa
WASU DAGA CIKIN GUDUNMAWARSA:
Kasancewar Chomsky masani ne a
fagen harshe, kuma idan aka yi la’akari da irin tarihin rayuwarsa kama daga
karatunsa zuwa rubuce-rubucensa za a fahinci cewa akwai gudummawar da ya ba da
daman gaske ga al’umma musamman a É“angaren
harshe waÉ—anda ba za a
iya ƙididdige
adadinsu ba amma an binciko wasu daga cikin irin gudummawar da ya ba da kamar
haka:
1. Ya fito da matakin ma’ana iri
biyu (zurfafa abin da aka faÉ—a
da kuma na farfajiya) wato “deep structure and surface structure” shi deep
structure na nuni da abin da yake cikin zuciyar kowane mai amfani da harshe,
sannan surface structure kuma ya shafi yadda sadarwa take gudana.
2. Ya kuma nuna Bambanci tsakanin competence da performance wato
(iyawa) da
(aiwatarwa) ya ce competence
(iyawa) na nufin muhimmin ilmi a harshe, shi kuma performance (yi/aiwatarwa) na
nufin ainihin yadda harshe ke amfani a zahiri.
3. Shi ya ƙirƙiro da hanyar sabunta
Nahawu wato (Transformation Generative Grammar) wanda a ka mayar zuwa
Transformational Analysis ma’ana
tsarin sabuntawa wanda ke bayyana tsarin jimla a harshe.
4. Ya taimaka wajen fito da
hanyar nazari da warware jimla a harshe da ake wa take da “Syntactic Analysis”
daga cikin Government and Binding Theory Ya sake fito
da ra’ayinsa na karyata cewa
mutum na samun harshe ne ta kwaikwayo, a wurinsa abin da ya bayyana a fili
wajen samun harshe wani abu ne da ya fi matsayin kwaikwayo.
5. Ya yi aiki a É“angaren ilmin tsarin sauti da kuma ilmin sautin harshe wanda aka wa rajista cikin kundin ilmin sautin harshe.
Chomsky ya yi aikace-aikace
kala-kala ba ma a É“angaren
harshe ba har da sauran fanfonin limi da dama.
Na buga tarihin rayuwarsa da wasu
aikace-aikacensa a cikin muryar audio ga mai buƙata zai iya tuntuɓa ta.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.