Ticker

6/recent/ticker-posts

HUKUNCIN KARATUN ALQUR'ANI DA MUS'HAFI A CIKIN SALLAH!

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalamu alaikum malam. Barka da wannan lokaci mai tarin albarka. Ya ibadah? Ina da tambaya malam. Tambayata kuma ita ce; wanda bai haddace Alqur'ani ba zai iya ɗaukan Alqur'ani yana gani yana karantawa a yayin da yake cikin sallah? Nagode...

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salámu, babu laifi mutum ya yi karatun Alqur'ani ta hanyar kallon Mus'hafi a sallar nafila, kamar qiyamul laili da makamantansa. Amma an karhanta hakan a sallar farilla saboda kasancewar qarancin buqatar hakan, amma idan buqata ta sa a yi hakan a sallar farilla, to nan ma babu laifi idan an yi karatun da Mus'hafi.


Ibn Qudama Almaqdisiy ya faɗi daga Imam Ahmad cewa: "Babu laifi liman ya yi wa mutane sallar dare alhali yana kallon Mus'hafi, sai aka ce masa: Har a sallar farillah? Sai ya ce: A'a, ban ji komai game da hakan ba... Almugniy (1/412).


Imam Annawawiy ya ce: "In da mai sallah zai karanta Alqur'ani daga Mus'hafi, to hakan bai ɓata masa sallarsa ba, ko da ya haddace Alqur'ani ko bai haddace ba, kai wajibi ne ma ya aikata hakan idan bai haddace Fatiha ba... Almajmú'u (4/95)


An tambayi Assheikh Ibn Baaz cewa: Shin ya halasta ga liman a salloli biyar na farilla ya yi karatu daga Mus'hafi, musamman ma a sallar Asubahi, saboda an so a tsawaita karatu a cikinta saboda tsoron yin kuskure ko mantuwa?


Sai ya ba da amsa da cewa: "Hakan ya halasta idan buqata ta haifar da hakan, kamar yadda ya halasta a sallar Tarawihi ga wanda bai haddace Alqur'ani ba, haqiqa ZAK'WAN bararren bawan A'isha Allah ya qara mata yarda ya kasance yana yi mata sallah da Mus'hafi a Ramadana... 

Majmú'u Fataawá (11/117).


Don haka 'yar uwa ba laifi mutum ya kalli Mus'hafi ya yi sallar nafila da shi musamman qiyamul laili, haka nan ma a sallar farilla idan buqata ta haifar da hakan musamman ga wanda bai haddace ayoyin da zai yi sallah da su ba.


Allah S.W.T ne mafi sanin daidai.


Jamilu Ibrahim, Zaria.


Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FBuwMyVjc2sGOEGLm0W7ed

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments