Ticker

6/recent/ticker-posts

ZAN IYA TAFIYA SUJJADA DA GUIWA KO KUMA DOLE SAI DA HANNU ?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓

Assalam Alaikum. Mallam, dangane da zuwa sujada, tafiya da gwuiwa ko da hannu a cikin sallah, wanne yafi inganci?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam. mutum zai iya yi, saboda akwai riwayoyin hadisi mabanbanta akan haka, kuma kowacce riwaya akwai malaman Hadisin da suka ingantata.


Abin da ya fi kamar yadda Malaminmu Dr. Ahmad Muhammad Ibrahim ya fada mana a karatunsa na SunanutTirmizi shi ne: wani lokocin mutum ya tafi da guiwa, wasu lokutan kuma da hannu, saboda aiki da riwayoyin gaba ɗaya, da kuma fita daga saɓanin Malamai.


Allah ne mafi sani


Amsawa: Dr. Jamilu Zarewa


Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8qu9GT

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments