DARASI NA 35
MAZA INA KIRA GAREKU
Da yawa daga
cikin mazan aure a wannan zamanin inda za ka leƙa wayoyinsu ba za ka rasasu da
chat da wasu matan banza a waje ba.
Da yawansu kuma za ka ga basa so su sami
matansu da aikata irin wannan laifin, amma shi yana aikatawa saboda rashin
tsoron ALLAH.
Malamai sun ce baya halatta mace ta rinƙa
bincike a wayar mijinta, sai ku kuma maza kuke amfani da wannan hujjar kuke abin
da kuka ga dama, kuna chat na batsa, kuna tura hotunan jikinku ga matan banza,
suma suna turo muku, shin kuna tunanin kuna yiwa ALLAH wayo ne?
WALLAHI yadda matarka zataci amanarka ALLAH ya
ƙona ta, haka kaima za kaci amanarta ALLAH ya ƙonaka, duk laifin da idan
matarka ta yi maka zai jawo mata shiga wuta kaima idan ka yi mata irinsa za ka
shiga wuta.
Kada son kanka ya sa ka ruguza lahirarka, kuma
duk yadda kakai da wayo da dabara na kada a gane kana kula matan banza a waje
alhali kana da mata a gida, to kaima sai an lalata ‘yarka ko matarka ko
mahaifiyarka ko ƙanwarka ko yayarka ko kanaso ko bakaso.
Sannan kuma tayaya za ka rinƙa bincike a wayar
matarka amma kai don an hanasu bincike a wayoyinku sai kuma ku rinƙa
zaluntarsu, kuna cin amanarsu, kana tunanin ALLAH zai barka ne?
Yadda idan matarka taƙi amsa kiranka izuwa
makwanci mala'iku za su la'anceta, haka kaima idan ta zo da buƙatarta, kaƙi
amsa mata ba tare da dalili na larura ba, ALLAH zai yi fushi dakai, domin yadda
kake da haƙƙi a kanta haka itama take da haƙƙi akanka, kuma duk wanda ya tauye haƙƙin
wani a cikinku ALLAH sai ya karɓa masa haƙƙinsa.
Kawai don an baku dama saiku rinƙa abin da
kukaga dama, lallai ku sani ALLAH yana sane da abin da kuke aikatawa, kuma kowa
zai sami sakamakonsa tun anan duniya, sannan kuma kaje lahira ka haɗu mala'ikun
azaba.
ALLAH ka bamu
ikon aiki da abin da muka karanta.
ALLAH ka yafe
mana zunubanmu baki ɗayanme Ameen.
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.