𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Abokina Ne
Yake Mafarki Dana Miji Suna Saduwa, Abun Yana Bashi Tsoro Sosai, Takai Inya
Zauna Cikin Abokansa, Sai Yaji Sha'awa Ta Kamashi Saidai Ya Tashi Daka Wajan,
Bayason Jinsin Sa Na Miji Ya Zauna Kusa Dashi, Kuma Bai Dena Mafarkin Ba, Ya Zai
yi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
الحمد لله.
Irin Wannan
mafarki damai Kama dashi suna cikin mafarkai waɗanda ba a san gani, suna
kunnowa daka Shaiɗan ne, Abun da Musulmi ya dace ya yi idan yai irin waɗannan
mafarkan munana ko yaga mafarkin da bayaso, yai tofi aɓarin hagu ɗinsa sau uku,
ya nemi tsari daka sharrin Wannan mafarkin da sharrin Abun da ya gani, sannan sai
ya juya akan ɗaya ɓarin nasa yaci gaba da baccinsa, Mafarkin Ba zai cutar dashi
ba, kada ya baiwa kowa labari, saboda faɗin Annabi Sallallahu Alaihi wasallam (Mafarki
Mai kyau daka Allah ne, Mummuna ko baragadan mafarki daka Shaiɗan ne, idan ɗayanku
yai mafarkin da yake tsoro yai tofi aɓarin hagu ɗinsa ya nemi tsarin Allah daka
Shaiɗan mafarkin ba zai cutar dashi ba, Bukhari Babin Bad'ul kalƙi (3049).
Idan Kai mafarki
wani yana jima'i dakai, Wannan ya Saɓawa dabi'a.
Abun da ya
kamata kabayar da kulawa akai shi ne lazimtar Neman Tsarin Allah da Shaiɗan, da
kuma lazimtar Koyarwar Annabi Sallallahu Alaihi wasallam, riƙo da Zikirorin
yini da dare, da zama da Alwala, Kwanciya bacci da Alwala Neman tsari da
karanta Falaƙi da Nasi da Ƙul-huwa ka shafe jikinka yayin Kwanciya bacci.
Lazimtar
Karanta Alƙur'ani ko Sauraronsa, Da Abokantaka da Mutanen kirki.
Da naci Wajan
rokon Allah ya tsareka daka dukkan wani Mugun mafarki da Mugun aikin da baya
so.
Da roƙonsa ya
fiddaka Wannan marhala ta balagar farko dake ciki lafia ba tare da aikata ko
zamewa zuwa aikata abun da baya so ba.
Babu shakka
kana cikin Marhala mafi haɗari arayuwar matashi ta fuskar sha'awa wato Shawa'ar
balagar farko, tafi kowacce tashin hankali da hatsari ga Matashi.
Amma Matuƙar
ka lazimci Zikirori da Addu'a da dabbaƙa abun da Annabi Sallallahu Alaihi
Wasallam ya koyar yayin kwanciya bacci babu shakka za ka wanye lafiya.
Muna Roƙon
Allah ya tsareka damu Da sauran musulmi daka dukkan Wani mummunan Mafarki da
dukkan wani abun ƙi.
Wallahu
A'alamu.
🖊Tambaya da Amsa Abisa fahimtar Magabata Na Kwarai
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBƙfaiPwf28l
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.