Ticker

6/recent/ticker-posts

Sana’ar Dinkin Tela Da Bunkasa Tattalin Arziki Ga Al’umma

 Takardar ƙara wa juna sani da aka gabatar a ajin ALH 400: Seminars, a Sashen Nazarin Harsuna Da Aladu, Jamiar Tarayya Gusau, Nijeriya, (2022/2023 Academic Session).

Federal University Gusau (FUG) Nigeria

Sana’ar Dinkin Tela Da Bunkasa Tattalin Arziki Ga Alumma

NA

SUFIYANU MUHAMMAD DAURAN

LAMBA G S M: 07038879248

KIBƊAU: sufiyanumuhammaddauran@gmail.com

TSAKURE

Sana’ar ɗinki hanya ce da ɗan’adam yake bi domin ya nemi abinci da lalurorin yau da kullum. Masana sun haƙiƙance cewa tana ɗaya daga cikin sana’o’in da ake aiwatarwa da nufin biyan buƙatan yau da kullum. Wannan hanya ta neman abinci, cike take da fasahohi daban-daban waɗanda masu yin ta suke bi yayin gudanar da ita. Wannan sana’a a halin yanzu ta samu haɓaka da bunƙasa domin samun wasu kayan aikin ta musamman ma sakamakon juyawar zamani ya haifar da wasu kayayyaki ɗinki na tela.

Da wannan dalilin ne nazarin ya yi amfani da ra’in adana al’adu. Tunanin ra’in ya tafi akan cewa al’umma da take son cigaba, to lalle ne ta kyautata hanyoyin da zata samar wa matasanta sana’ar yi domin guje wa salwantar matasanta.

Da wannan dalilin ne ya sa wannan muƙala ta yi ƙoƙarin nazarin waɗannan al’adu na Bahaushe, ganin cewa a inda aka fito, ba a yi wani Bincike mai zurfi ba dangane da al’adun ɗinkin tela. Wannan maƙalan an ziyar teloli daban-daban domin samun muhimman bayanai ga me da sanaar. Amfani da ziyar gani da ido a wajen masu gudanar da wannan aiki na ɗinkin tela kuma an yi amfani da bitar dabarun Bincike ta neman bayanai wajen masu yin wannan sana’ar da bugaggun littafai.

1.0       GABATARWA

Wannan muƙala na nufin sanaar ɗinkin tela da bunƙasa tattalin arziki. Duk da cewa a wajen masanin nan Salisu Ahmad Yakasai (1958:118) ya bayyana sanaa hanya ce ta neman ɗan abin dogaro da kai, kuma shi malam Bahaushe a al’adance ko kaɗan bai amince da mutum ya zama cima kwance ko ɗan zaman kasha wando ba. Abin da yafi burgewa da ban sha’awa a wurin malam Bahaushe, shi ne mutum ya riƙa yar sanaarsa komi ƙanƙantar ta. Don haka ne ma, akan ce sanaa goma maganin kwanan ban za, maana idan kana da yar sanaarka ta neman abinci, ba yadda zaa yi ka zauna wawi, kana ta sharer barci babu gaira babu dalili. Rayuwar yau da kullum ta malam bahaushe ita ta haifar da gudanar da wannan sanaar ɗinkin tela da bunƙasa tattalin arzki ga alumma.

1.1 DABARUN BINCIKE

 Domin ɗora wannan Bincike ga sahihiyar hanya ne ya sa aka yi amfani ta hanyoyin tattara bayanai kamar haka;

i.bitar ayyukan da suka gabata

ii.neman bayanai ta hanyar ziyar gani da ido

iii.karance-karance bugaggun litattafai

iv.nazarin kundayen Bincike da muƙalu

v. Zantawa da wasu masana’antun ɗinkin tela kai tsaye ko amfani da wayar salula

2.0 WAIWAYEN KALMAR SANA’AR ƊINKIN TELA

 Kamar yadda masana bayanin wannan sana’ar ɗinkin tela na daga cikin al’ada a ƙarƙashin adabin Hausawa ya jefa wannan kasha cikin alada.Dinkin tela na nufin sanaa ce da mutune ke yi wanda suke sawa ko sakawa a jikinsu, yawancin mutane ne, zai sawo yadinsa ya kai wa wanda ake kira maɗinkin tela. Kuma sai wanda kake son kai ma sana’ar ɗinkin kayan.

 Kalmar sana’a kalma ce da aka aro daga harshen larabci, kuma take ɗaukar ma’ana ta samar da wani abin amfani ta hanyar hikima a Hausance. Yakasai Salisu Ahmad (1958) ya bayyana cewa. Har ita yau sana’a hanya c eta neman ɗan abin dogaro da kai, kuma shi malam Bahaushe a al’adance ko kaɗan bai amin ce da mutum ya zama cima-kwance ko kaɗan zaman kasha wando ba. Abin day a fi burgewa da ban sha’awa a wurin malam Bahaushe, shi ne mutum ya yaƙa yar sanaarsa, komi ƙanƙantarta. Don haka ne ma, akan ce sanaa goma maganin kwanan banza maana idan kana da yar sanaarka ta neman abinci, ba yadda zaa yi ka zauna wawi, kana ta sharar barci babu gaira babu dalili. Rayuwar yau da kullum ta malam Bahaushe ita ta haifar da Hausar teloli kamar yadda zamu ga misali

S/N

KALMOMIN/JUMLA

MA’ANA

1

Babbar Lamba

Ayi ɗinki mai tazara (bakwai)

2

Ga almakashin da kake nema

Mai kuɗi ya kawo dinki za’a yankarmasa wuya

3

Na bashi bagaga

Ya yiwa wani ɗinki da babbarku ba(dinki marar inganci)

4

Rawar tela

Ɗinki a waje guda don ya yi karfi

5

Ya kawo ajiya

Ɗinkin da aka kawo ba kuɗi

6

Yana

Yana yanka

 

2.1 KAYAN DA AKE BUKATA MANYA DA ƘANANA

 Ana buƙutar kayayyaki kamr haka, Na farko dai jarin sayen kayan aiki: kowa ce sana’a na buƙatar jari ko yaya ta ke kafin fara samun kuɗi da ita, ya danganta ƙarami ne ko babba, kuma wannan sanaa kana iya fara tad a ƙaramin jari kawai dai ana buƙatar abubuwa da ka-ke buƙata su ne ya kasance ka sayi duk wani abu na aiki kamar haka

(i)                 Ke-ken ɗinki

(ii)              Zare

(iii)            Allura

(iv)            Almakashi

(v)               Reza

(vi)            Man ke-ken ɗinki

(vii)          Abin awo (tape)

(viii)       Mashin Ziza

(ix)             Kujera Zama da sauransu

Bayan haka akwai wurare da dama da za ka koyi wannan sana’a wanda su ka haɗa da wajen horaswa na sana’o’in zamani ko kuma a samu kuɗi ƙalilan ka je gun mai shago ka biya shi lada shi kuma shi koya maka.

2.2 BUNƘASAR TATTALIN ARZIKI (Economy)

 Ya dogara ne a kan samar da abinci da sutura da ayyuka, kiwon lafiya da ilimi da gine-gine da sauransu da kuma rarraba su da cinikayyarsu har zuwa ga amfani das u ga al’umma. Ɗinkin tela yana daga cikin hanyoyin tattalin arziki domin tanan ne bunƙasa da aiwatarwa da haɓaka ayyukan da ke kawo cogaban ƙasa da kuma kula das u.

2.3 ABUBUWAN DAKE HAƁAKA TATTALIN ARZIKIN MATASA SUN HAƊA KASUWANCI DA MAAIKATU DA GWAMNATI.

 Abdulra’uf Lawan saleh Sarkin yakin Arewa ne ya wallafa. Ayyukan tattalin arziki yafara ne tun daga cinikayya, wato a sanda mutane biyu suka kulla yarjejeniyar cimma ciniki a kan wani abu da ake so, ta hanyar amfani kuɗi ko wani abu mai daraja manyan shaddodi da atamfofi da sauran matiriyal na ‘ya duddukan ɗink.

2.3.1 TATTALIN ARZIKI NA SAMUN HIMMA NE TUN DAGA SAMAR DA AYYUKA

 Ko abubuwan da ke amfani da albarka tun ƙasa ko maadinai da aikin dan-adam da sa jari. Amma haka ya canja sanadiyar canjin rayuwa da kuma cigaban fasahar ɗan-adam wurin amfani da injinia masu sarrafa kansu.Haka ya kawo samun sauki da saurin aikata ayyukan da kuma rage kuɗin da ayyukan ƙasa. Haka a nan kuma samun cigaba wurin ƙirƙiran sababin abubuwa da sababbin hanyoyi aiki da sababbin hanyoyin gabatar da ayyuka manya-manya kasuwanni, kasuwannin da suka tattari abubuwa daban-daban, an kuma sami karin kuɗin shiga.

2.3.2 TATTALIN ARZIKI

 Yana samun nasara ne sanadiyar ayyukan al’adun al’ummah, martabar da ilimin su da faɗaɗar fasaharsu da tarihinsu da tsarin al’ummarsu da tsarin tafiya da siyasansu da dokokinsu, har wayan da kuma irin yana yin ƙarar da maadinan ƙasa da yana yin rayuwar halittun ƙasar, waɗannan su ne ke bayar da cikakkiyar samun haɓakar arzikin ƙasa. Kuma wadannan abubuwan suke bayar da guri da abubuwan da arziki ke cigaba das u sannan ya tsarasu a kan amfanuwar ƙasa da alummarta.

2.3.3 AKWAI TATTALIN ARZIKIN DA YA DOGARA KACOKAN AKAN KASUWANCI

 Kuma yana gudana ne akan cinikayyar ayyuka ko kayayyaki tsakanin mutane ta hanyar samar da su da kai su kasuwanni domin cinikinsu da kuɗaɗe ko da wani abun da aka ƙayyade mai daraja.

2.3.4 AKWAI TATTALIN ARKI DA YA DOGARA A KAN BAYAR DA UMURNI DAGA YAN SIYASA KAI TSAYE

 Da kula da yadda ake samar wa ‘yan ƙasa da ayyuka ko kayayyaki da kuma yadda zaa sayar das u da rarrabasu. Daga bisani kuma akwai tattalin arziki day a dogara a kan ma’adinan ƙasa da sanya alumma cikin gudanarwarsu.

3.0    SAKAMAKON BINCIKE

 Wannan Bincike ya sami nasarar fito da wasu kalmomi/jimla da ma’anoninsu a sarari. Yin haka zai taimaka ainun wajen da waɗannan al’adu musamman idan aka yi la’akari barazanar da wannan muhimmiyar sana’a ta ke fuskanta. A halin yanzu rashin jari da tashin kayan dinki da kuma uwa uba telolin kan su sun haɓɓaka da sauyin da zamani ya kawo. A cikin wannan muƙala, an kawo wasu sunayen daga kayan amfani ko aikin ɗinki da Hausar Teloli da ma’anarta.

3.1 SHAWARWARI (ADVICE)

 Bisa ga ababen da wannan Bincike ya binciko ne ake ganin da akwai hangen na bayar da shawara a kan wannan gas u kamar haka

(i)                 Yana da kyau masu dinkin tela su haɗa da wata sana’ar ganin a halin yanzu an samu canje-canjen kayan aiki na tela.

(ii)              Akula da kwastomomi da sakin fuska da yin ragowa komai ƙanƙantarta,domin sanya wa abokin hulɗa rai.

(iii)            A rinƙa ba wa teloli tazara misali,sati ɗaya da ɗunki, kuma a rinƙa haɗawa da abun fara aiki ma’ana wasu kuɗi

(iv)            Kuma uwayen gida a riƙa yaran shago da kyau, domin tela ɗaya kusan mutum goma na neman abinci gareta don haka a yi haƙuri da yara

3.2 KAMMALAWA (CONCLUTION )

 Wannan muƙala ta yi tsokaci dan gane da sanaar ɗinkin tela da bunƙasa tattalin arziki.

 Haka ma an kawo a cikin muƙalar bayanai dangane da sanaoin Hausawa suka jiɓinta, kamar ma’anar sana’a da kuma ma’anar ɗinkin tela da yin bayani ga me da Hausar teloli da bayani a kan tattalin arziki.Don haka ra’ayin wannan muƙala ne cewa a ƙara zurfafa Bincike a kan lamarin domin fito da bayanin wannan sanaa a fili ganin cewa yanzu lamarin ɗinkin na ƙara samun cigaba da bunƙasa ta wajen tattalin arziki.

 Idan aka yi haka an rare wannan muhimmin abu daga haɗirin salwanta gaba daya. Wannan ba ƙaramin ba ne ga alummar Hausawa masu tasowa, da mazauna birane, wadanda za su rayu a wani lokaci nan gaba.

Sunayen Wadanda aka yi Hira da su.

1        Mai gida Halliru Ibrahim Dauran, Dattijo mai halin girma kuma ya na da shekara 54, Ranar 14/11/2023

2        Kabiru Na’ala Gusau Tashar magami Bakin Masallacin Dogon Koli Mai Shekara 50, Ranar 11/12/2023

3        Alhaji Sani Dahiru S/tazame dattijo mai Halin Girma nagode. Kuma yana da Shekara 60, Ranar 2/12/2023

Babban tela kuma mai gyaran tela a garin Kwatarkwashi Hayi.

4        Samira Tela Mace mai kama da maza a wajen ɗinkin tela mace mai shekara 25,Ranar 19/12/2023

A wajen Sana’arta in da ta ke ɗinka kayan makaranta ga yara da manya.

Post a Comment

0 Comments