Ticker

6/recent/ticker-posts

DAGA INA SAHU YAKE FARAWA?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam ya gida ya kuma aiki, mal don Allah innada tambaya mal sahun sallah kan ta dama za'a fara ne ko ta hagu.?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikum assalamu To ɗan'uwa sahun da yake bin liman zai fara ne daga bayan liman ma'ana a sanya liman a tsakiya, saboda fadin Annabi ﷺ "Masu hankali daga cikinku, su bi bayana" kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 116. Sannam da fadin Anas R.A lokacin da yake bada labarin ziyarar da Annabi ﷺ ya kai gidansu: "Sai muka tsaya ni da marayan a bayansa" kamar yadda Bukhari ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 694, daga nan kuma sai a cigaba da cika shi ta bangaren dama.

Haka nan ake so sahu na biyu shi ma ya kasance, ya fara daga tsakiya ya tafi zuwa dama, saboda fadin Bara'u dan Azib R.A "Mun kasance idan muka yi sahu a bayan Annabi ﷺ mu kan so mu kasance a damansa, ya fuskanto mu da fuskarsa" Muslim a hadisi mai lamba ta: 709.

Allah ne mafi sani

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

 

Post a Comment

0 Comments