Ticker

6/recent/ticker-posts

TSAKANIN LIMAN DA LADAN WAYE YA FI SAMUN LADA?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Asalamu'Alaikum Malan inada Tambaya Kamar Haka Malan Tsakanin Liman Da Ladani Waye Yafi Samun Lada Awajan ALLAh.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

 An sami Saɓani a kan Wannan Mas'alar. Wasu Suna Ganin Ladan ya fi Liamn Samun Lada. Waɗansu kuma suna Ganin Liman ya fi Ladan Samun lada.

Wadanda suke Ce ladani ya fi Limami Samun Lada suna ganin Cewar!

👉 Duk wanda ya Ji kiran sallah, Kuma ya zo ya yi sallah ko ya tashi ya yi sallah, ko da ba a Wannan Masallcin ba, To fa Malam Ladan yana da Lada Akansa. Sabida ya Tunatar da shi Cewar lokacin sallah yayi.

👉 Duk wanda ya Ji kiran sallarsa zai Bayar da Sheda akan Sa a Ranar Alkiyama. Hatta Mala'iku Zasu Bayar da Shedar Ladani a Ranar Alkiyama. Haka Dabbobi da Tsuntsaye da Kwari da Aljanu.

👉 Ladan yana Tayar da Mutane daga barci don su Bautawa Allah. Har da Shi Kansa Limamin Malam Ladan Ne yake Tayar da shi.

👉 Ladani yana Korar Shaiɗanun Aljanu a Daidai Lokacin da suka Ji Kiran sallar da yakeyi.

👉 Ladan Zai Kira Sallah kuma ya Jira har zuwa Lokacin Sallah yayi, Har Zuwan Limami Wannan Masallacin. Shima wannan Jiran da Ladan zaiyi, Ana Rubuta Masa cikakken Ladan sallah.

👉 Ladani Shi ne wanda zai zo ya Buɗe Masallaci ya tsaftace shi, ya Kunna Futulun Masallci. Wani Lokacin ma ya share Masallcin Kafin Zuwan Kowa da Kowa.

 HUJJAR WAƊANDA SUKE GANIN LIMAMI YA FI LADANI SAMUN LADA SHI NE.

👉 Shi Limanci Aikin Annabawa ne. Daga wannan Ban san Wani Abu ba. Sabida haka Da Kace Wanene ya fi Daraja Tsakanin Liman da Ladan, Kai Tsaye Zance maka Liman Shi ne Mai Daraja ta Farko. Amma Samun lada Kam Ina Ganin Kamar Malam Ladan Yafi Malam Liman Samun Lada. Amma a tawa Fahimtar Fa. Sabida Manzon Allah ﷺ Ya ce DA MUTANE SUN SAN  abin da YA KE CIKIN LADANCI NA DARAJA , Ma'ana Kafin ka zama Ladani, DA SAI an yi ƘURI'AH SANNAN IDAN KA CINYE ZA KA ZAMA LADANI.

Allah shi ne Masani.

Zauren Tambaya Da Amsa Abisa Alkur'ani Da Sunnah. Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Za ku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/BSA30hdZD7V3WSJF8WVwUj

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

 

Post a Comment

0 Comments