YAYA AKE DAIDAITA SAHU ACIKIN SALLAH ?

     𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Menene Matsayin Sahu Acikin Sallah sannan kuma ya shari'ah Tace a Daidaita Shi???

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wajibi ne ga musulmai su tabbatar da sahunsu ya daidaita kuma ya haɗe gam!! Kuma anayin hakan ne ta tsayuwa kafada da kafada, kafa da kafa.

    An ruwaito hadisi daga Anas bn Malik ya ce: Manzon Allah ﷺ ya ce: Ku mike sahunku ya daidaita saboda ina ganinku daga baya. (Bukhari 686, Muslim 425).

    An karbo daga Abdullahi ibn Umar ya ce Manzon Allah ﷺ ya ce: Ku daidaita sahunku ya mike daidai kuma Ku rufe ratan (gap) dake tsakaninku, kuma kada Ku kyamaci hannayen yan'uwanku. Kada Ku bar rata wa Shaiɗan. Wanda ya cika sahu Allah zai bashi lada, Wanda kuma ya lalata sahu Allah zai barshi da dabararsa.

    Abu Dawuda ya ce  abin da ake nufi da "Kar Ku kyamaci hannayen yan'uwanku" shi ne mutum ya yi hakuri da sassauci ga Ɗan'uwansa idan ya turashi gaba ko baya wajen daidaita sahu (Awn al-Ma’bood).

    Abu dawud 666, Al-Nisaa'i 819. Albani ya ingantashi a Saheeh Abi Dawood , 620.

    An ruwaito cewa Nu'umanu ibn Basheer ya ce: Manzon Allah ﷺ yana juyowa baya ya fuskanci mutane ya ce "Ku daidaita sahu, har sau uku (3), Na rantse da Allah kodai Ku daidaita sahu ko Allah ya kirkira muku rarrabuwa a zukatanku". Nu'uman ya ce naga mutane suna tsayuwa kafada da kafada, guiwa da guiwa, idon sawu da idon sawu.

    Abu Dawud ya ruwaitoshi (Abu Dawood, 662); Al-Albaani ya ingantashi a Saheeh Abi

    Dawood , 616.

    Haɗa sahu yana ingata ne idan kafar mutum biyu suka haɗu tin daga haɗewa karamin yatsan kafafunsu har izuwa yaɗuwar idon sawun kafafun biyu.

    Saidai malamai sun yi bayani cewa mutum bazai zurfafa ba wajen haɗe sahu da Ɗan'uwansa Wanda bayason haɗewa idan har yunkurin haɗa sahun zai sa kafar mutum ta karkace daga Alƙiblah.

    (Laa jadeed fi Ahkaam al-Salaah , 12. 13).

    ﻭﺍﻟﻠﻪ ﺃﻋﻠﻢ

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah, ta fahimtar magabatan kwarai.

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi.

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

     

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.