Ticker

6/recent/ticker-posts

Zan Iya Sake Matata Saboda Tana Da Cutar Ƙanjamau (HIV AIDS)?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Malam matata ta yi rashin lafiya, da aka gwada ta, sai aka ce tana da cutar aids, ni kuma an gwada ni amma an ce ba ni da ita, Sannan an gwada ragowar matana, suma an samu ba su da ita, gaskiya malam ina so zan sake ta, saboda kar ta shafe mu, amma ina neman shawara?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

To dan’uwa cutar aids tana daga cikin cututtuka sababbi, waɗanda ba a tattauna su ba a manyan kundayen musulunci, sai dai idan muka duba manufar da ta sa aka shar’anta saki wato tunkude cuta da matsala, daga daya daga cikin ma’aurata ko su duka, za muga ta tabbata a wannan cuta, tun da ilimin likitanci ya tabbatar da cewa cuta ce mai haɗari kuma ana daukarta, don haka ya halatta ka sake ta, saboda wannan dalilin, tun da malaman Fikhu sun halatta raba aure saboda cutar kuturta, kamar yadda hakan ya zo a Minahul Jalil Sharhu Muktasarul Khalil: 6\478 Cutar Sida kuma tafi kuturta tsanani. Sannan ba za a kalli cutuwar da za ta yi ba, bayan an saketa, domin yana daga cikin ka’idojin Sharia: kau da kai daga tunkude cutar da za ta shafi wani saboda cutar da za ta game, Cigaba da zama da ita zai jawo ka dauki cutar, kuma iyalanka su dauka, wannan ya sa ba za a waiga zuwa damuwarta ba a nan wurin.

Allah ne mafi sani.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBƙfaiPwf28l

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi


Post a Comment

0 Comments