𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum malam. Barka da warhaka, malam don Allah da gaske ne in an yi sakin aure Al'arshi yana girgiza?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus
Salam, dangane da maganar cewa Al'arshi yana girgiza idan aka yi sakin aure, an
ruwaito hadisi game da wannan maganar, sai dai hadisi ne bara-gurbi, wato
hadisin ƙarya
ne ƙirƙirarre,
bai tabbata daga Manzon Allah ﷺ
ba, malamai sun bayyana shi a matsayin hadisin ƙarya a cikin litaffai mabambanta.
Daga cikin maruwaita hadisin akwai JUWAIBIR da
AMRU BN JUMAI'I, malamai sun ce ba a aiki da hadisinsu. Kuma akwai ADDHAHHAK,
Ibnul Jauziy ya ce yana da rauni.
Duba
ALMAUDHU'ÁT (2/277), na Ibnul Jauziy.
Saboda haka
masu faɗin wannan
magana su daina faɗin
ta, saboda ba ta tabbata daga Fiyayyen Halitta ﷺ
ba. Kawai dai saki a aure ba abin so ba ne har sai idan akwai lallurar hakan.
Allah S.W.T ne
mafi sani.
Jamilu Ibrahim
Sarki, Zaria.
Ga Masu Buƙatar
Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin
mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfƙds
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.