𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum, barka da warhaka
malam, Don Allah ya namijin da duk abin da ya haɗa shi da iyalinsa, sai ya
dunga ikirarin zan iya sakin ki wallahi, kuma ba ɗaya ba, zan iya sakin ki uku?
Allah ya kara maka daukaka.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salamu, mijin da ke ce
wa matarsa zai iya sakin ta ba za a ce ya yi wani laifi ba idan ya kasance
wacce ba ta jin nasiha ce har sai ya haɗa mata da tsoratarwar sakin, wata ƙil
hakan ne kaɗai kan sa ta natsu idan ya hana ta yin wani abin ta ƙi hanuwa. Kuma
wannan magana tasa ba saki ba ne.
Sai dai bai dace mutum ya zama duk
abin da matarsa ta yi masa babba da ƙarami ya riƙa mata barazanar saki ba, saboda
wani abin bai kai girman da za a yi barazanar saki ba. Haka nan bai dace yawan
yin rantsuwa a duk lokacin da zai faɗi kalmar ba, sai dai faɗakar da mace da
kalmar saki a inda aka buƙaci hakan ba laifi ba ne kamar yadda ya gabata.
Allah S.W.T ne mafi sani.
Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.
Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group
Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/FmJ5Ojsns1KFolTP8ƙu9GT
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.