Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Wani Na Iya Sakin Matar Wani?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam, mutum ne aka ba shi sako ya kaiwa matarsa, yana zuwa sai ya ba ta, da ta duba sai ta ga saki uku, shi ne ta tafi gida, kuma ya ce shi bai sake ta ba, iyayenta kuma sun ce ba za ta koma ba sai ta yi wani auran, to yaya matsayin auren yake.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam, ‘yar uwa ai wani ba ya sakin matar wani, in dai har an tabbatar cewa ba shi ya rubuta wannan saki ba, kuma ba da yawunsa aka yi ba, to wannan mata ba ta saku ba, saboda wani ba ya sakin matar wani, Alƙali ne ke da wannan damar a inda Shari'a ta ba da damar haka. Abin da ya kamata a yi shi ne iyayen matar su yi bincike su gano daga inda wannan saƙo ya fito, matuƙar aka tabbatar ba yawunsa a ciki, to su sani ba ta saku ba, tun da ba shi ne ya yi sakin ba. Amma idan da aka bincika sai aka gano da saninsa aka yi haka, to ta saku.

Allah S.W.T ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBƙfaiPwf28l

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments