Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Mafarki Gaskiya Ne?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam. Dan Allah ina da tambaya, ina so a yi mana bayani a kan yawan yin mafarke mafarke, shin mafarki gaskiya ne? Kuma a ba ni addu'ar da za ta nisanta ni da yawaita mafarki, kuma wani lokaci idan na yi mafarkin yakan tabbata, koyaushe na kwanta nakan yi mafarkai marasa kan gado na abubuwa iri irii.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam. ‘Yar uwa shi dai mafarki ba kowanne ne yake zama gaskiya ba, kamar yadda ba kowanne ne yake zama ƙarya ba, sai dai duk mafarkin Annabawan Allah gaskiya ne, matuƙar wani Annabi ya ce ya yi nafarki a kan abu kaza ya faru, to da wahala ka ga wannan abu bai faru ba.

Mafarki ya kasu kashi uku, na farko akwai mafarki Rahamániy, na biyu akwai mafarki Nafsániy, na uku kuma akwai mafarki Shaiɗaniy, kamar yadda hadisin Annabi ya bayyana. Tirmizhiy 2270.

1. Mafarki Rahmaniy: Wannan mafarki ne na gaskiya daga Allah, sau da yawa idan aka yi shi yana aukuwa, kamar mafarkin Annabawa da sauran mutanen kirki.

2. Mafarki Nafsaniy: Wannan kuma nau'in mafarki ne na abubuwan da mutum ya dami kansa da su a lokacin da yake idonsa biyu, sai bayan da ya kwanta sai su yi ta zuwa masa a cikin barci saboda yadda ya damu da su da rana.

3. Mafarki Shaiɗaniy: Shi kuma wannan ya ƙunshi duk munanan mafarkai da mutum kan yi ya yin kwanciya barci.

To dai a hadisin da Abu Sa'id Alkhudriy ya ruwaito Annabi ya ce: "Idan ɗayanku ya yi mafarkin abin da yake so, to wannan mafarki daga Allah ne, sai ya gode wa Allah a kanta, ya bayar da labarinta, idan kuma ya yi mafarki akasin haka (wato mummunar mafarki), to ita wannan mafarki daga Shaiɗan ne, kada ya labarta ma kowa, domin za ta iya cutar da shi". Bukhariy 6985, Muslim 2261.

A taƙaice dai, idan mutum ya yi mummunan mafarki abin da zai yi shi ne; ya yi isti'aza sau uku ya tofa a ɓarin hagunsa, sannan sai ya juya daga ɓarin da yake kwance zuwa ɗaya ɓarin, wato idan yana ta hagu ne ya koma ta dama, idan ma ta daman ne yake sai ya koma ta hagu, amma bayan ya yi isti'aza ya tofa a ɓarin hagunsa ɗin, kamar yadda Jabir Allah ya ƙara masa yarda ya ruwaito daga Annabi Muslim 2262.

Sannan kuma ki yi ƙoƙari ki riƙa kwanciya da alwala, ki riƙa yin addu'ar kwanciya barci da na farkawa daga barci, kuma ki riƙa karanta ayatul Kursiyyi, da suratul Ikhlas da Falaƙ da Nás, kafin ki yi barci. Kuma ki lizimci yawan karatun Alƙurani da azkar na safiya da yammaci, in Allah ya so za ki daina waɗancan mafarkai marasa kan gado ɗin. Allah ya sa mu dace.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria. 🏻

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/JLojawdOWYsEOeSHZMNdjf

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments