Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Ana Janye Saki Bayan An Yi Shi?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum, malam miji ne ya saki matarsa saki 1 a ranar ya janye bayan an daidaita, sai mahaifiyarsa ta zo gidan ana maida magana sai ya ce dama na sake ki na sakeki kitafi gidanku, malan ya sakin yake?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam, ai ba a janye saki bayan an yi shi, matuƙar mutum ya ce ya saki matarsa, to saki ya tabbata, ba maganar ya ce ya janye ko ya fasa, sai dai ki ce an sulhunta an ci gaba da zama a kan wannan saki da aka yi. Sannan hukuncin saki ɗayan nan ne za a yi masa hukunci a kai, saboda ai labarin abin da ya wuce yake bayarwa a lokacin mayar da magana, yana cikin magana ne sai ya ce dama ai na sake ki, wato sakin nan da ya gabatar yake ba da labari, sai kuma ya ce na sake ki, ki tafi gidanku, wannan a gaskiya a zahiri sakin da ya gabatar yake tabbatarwa ba wani sabo ba.

Sai dai yana da kyau bayan ya dawo hayyacinsa a tuntuɓe shi a kan hakan don a ji abin da yake nufi, shin sakin da ya riga ya gabatar yake nufi tare da wani ƙarin sakin, ko kuwa sakin da ya riga ya gabatar ne kaɗai yake ƙara tabbatarwa? saboda inda shubhar take a maganarsa da ya ce: "dama na sake ki" wato labari ne wannan yake bayarwa tare da tabbatar da abin da ya wuce.

Allah ne mafi sani.

Jamilu Ibrahim Sarki, Zaria.🏻

Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/IerSx3AH0ZSJyHIuIYfƙds

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Questions and Answers

Post a Comment

0 Comments