𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum, Mene ne hukuncin
matar auren dataje ta yi zina, shin aurenta yananan kokuma yalalace? Sannan
kuma dole ne saitayi ISTIBRA'I kafin mijinta ya sake saduwa da'ita kokuma a'a?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
wa'alaikum salam... Hakika laifine
babba ga Musulmi yaje ya'aikata zina, Shin yanada da aure ko bashida aure
haramunne agareshi ya yi Zina, domin Zina tana daga cikin manyan laifuka da
Allah(ﷻ) ya haramta a kan dukkan musulmi namiji ko mace, Kamar yadda Allah(ﷻ)
yakecewa:
وَلَا تَقْرَبُوا الزِّنَا ۖ إِنَّهُ
كَانَ فَاحِشَةً وَسَاءَ سَبِيلًا (سورة الإسراء/32)
FASSARA:
Allah(ﷻ) ya ce: kada ku kusanci
zina, domin ita alfahashace da kuma mummunar hanya:
Danhaka yazama wajibi agareta ta
tubaga Allah(ﷻ) ingantaccen tuban da ba za ta sake aikata irin wannan danyen
aikiba.
To amma dangane da maganar cewa ko
auren yananan ko bayanan, zance mafi inganci shi ne auresu yananan, hakanan magana
mafi inganci daga cikin zantukan da Malamai sukayi a kan wannan matsala shi ne
cewa mijinta zai'iya cigaba da saduwa da'ita batareda ta yi wani ISTIBRA'I ba,
duk dacewa akwai Malaman da sukace dole saitayi ISTIBRA'I, wasu sukace jini ③ za ta yi wasu kuma sukace jini ① za tayi, to amma magana mafi
inganci babu wani ISTIBRA'I daza tayi, domin idan ɗaya daga cikin ma'aurata
yaje ya yi zina, to wannan zinar ba za ta ɓata auren da ke tsakaninsuba, amma
inda a ce mace batada aurene to shi ne za ta yi istibra'i, Sai dai abin da
Malamai sukace shi ne idan Miji yasan cewa Matarsa mazinaciya ce to mafikyau
yarabu da'ita, domin za ta'iya ɓata masa Zurriyya, to amma idan ya kasance ciki
yashiga asakamakon zinar datayi, to ashari'ance za'ajingina wannan cikin kokuma
ɗan da tahaifa zuwaga Mijin da take aure amatsayin ubansa, saboda Manzon Allah(ﷺ)
ya ce:
(الولد للفراش وللعاهر الحجر)
Sai dai idan shi Mijinne yakore ya
ce ba ɗansa ba ne to shikenan sai ajinginashi zuwaga Mahaifiyarsa.
WALLAHU A'ALAM
Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group
Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/Fc3hX6HoDt65aKhhKOiDpX
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.