𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum. Malam ga
tambayata kamar haka: Shin idan wadda akayi zinan da ita ko wacce za'ayi da ita
ta fada maka, to wannan shaidar ya shaidu ne ko yaya.?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa,alaikum salam. Idan wanda ya
aikata Zina ko wacce ta aikata Zina ta/ya fadi cewa ya/ta aikata Zina, kuma a
cikin hayyacinsa yake/take to, wannan shaida ta isa a zartar da hukuncin Zina a
kansu basai an samu shaidu mutum huɗu ba. Saboda tabbatuwar Hadisai kamar haka:
An karbo daga Abu Hurayrah da Zayd
ibn Khaalid al-Juhani (Radiyallahu anhum) sun ce: Manzon Allah (sallallahu
alaihi wa sallam) ya ce: Ya Unais gobe kaje wajen wannan matar idan ta yadda
(cewa ta yi Zina) Ku jefe ta, (Unais) ya ce washe gari naje wajenta kuma ta
fada (cewa ta yi Zina), Sai Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) ya ba da
umarni aka jefe ta (har ta mutu). (Bukhari, 2575. Muslim, 1698).
Jabir (radiyallahu anhu) ya ruwaito
cewa wani mutum daga kabilar Aslam yazo wajen Manzon Allah (sallallahu alaihi
Wa sallam) lokacin yana cikin masallaci sai (mutumin) ya ce: "NA YI
ZINA" Sai Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) ya kauda kansa daga
mutumin, sai mutumin ya sake dawowa gefen da Manzon Allah ya juya fuskarsa, ya
sake cewa NA YI ZINA har sau hudu, Manzon Allah (sallallahu alaihi Wa sallam) ya
ce: Kai mahaukaci ne? Sai (mutumin) ya ce "A'a" Manzon Allah ya ce
kayi aure? Ya ce "Eh" Sai (Manzon Allah) ya ba da Umarnin a jefe shi
a musallah (Filin sallar idi), da (mutumin) ya fara jin dirikkowar duwatsu sai
ya gudu, saida aka kamo shi a Alharrah aka kashe shi. (Bukhaari, 4969; Muslim,
1691)
WALLAHU A'ALAM
Ga Masu Buƙatar Shiga Wannan Group
Zaku iya bi ta Links ɗin mu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://chat.whatsapp.com/GUƙ2GCCzlcdL6nknƙLYYox
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.