FATAN ALHERI ZUWA GA UBA MAI GOYA 'YA'YANSA FARFESA SA'IDU MUHAMMAD GUSAU DAGA ƊALIBINSA FARFESA BASHIR ALIYU SALLAU (SARKIN ASKAR YARIMAN KATSINA).
DAGA
FARFESA BASHIR ALIYU SALLAU
(SARKIN ASKAR YARIMAN KATSINA)
Ina farawa da sunan Allah, Maigirma da daukaka, wanda shi ne farko, kuma wanda karshensa ba ya karewa, ina yin salati ga Annabi Muhammadu, tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi.
Hakika, kome yana farko da karshe ban da ikon Allah. Allah cikin ikonSa, a karshen wannan wata na Maris, 2022, mashahurin Malaminmu, Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau, zai ajiye aikin koyarwa a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami'ar Bayero ta Kano, sakamakon cika shekara 70 a duniya, amma ba don ya gaji ba. Ya ajiye ne saboda haka dokar dauka da ajiye aikin Jami'a ta tsara ga dukkan Farfesan da ya kai shekara 70 da haihuwa.
A matsayina na dalibin Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau, tun daga shekara ta 2009 zuwa yau, na koyi kyawawan dabi'u da halaye wadanda suke taimakawa rayuwata a yau.
Da farko, lokacin da na kammala rubuta kundin digiri na biyu, shi ya sake duba aikin kafin a kai wa mai duba aiki na waje. Ya gyara min aikin yadda lokacin da aka yi min jarrabawa, ba a dauki minti 15 aka kammala tare da sanar da ni aikina ya yi kyau ba tare da ba wasu gyare-gyare ba.
Lokacin karatun digiri na uku, da farko Jami'ar Usmanu Danfodiyo ta Sakkwato suka dauke ni, da na sanar da shi, sai ya ce, bai yarda in tafi Sakkwato ba, dole in dawo Jami'ar Bayero don yin digiri na uku. Wannan ne ya sa, Malam ya sa aka dauke ni tun kafin sakamakon jarabawarmu na digiri na biyu ya fito.
Bayan kammala karatun aji a digiri na uku, Malam shi ya dauki nauyin duba aikina har Allah Ya sa na kammala. An sami wasu matsaloli wadanda suka sa ban kammala karatun a lokacin da ya dace na kammala wanda ta kai ga Tsangayar Kula da Karatun Babban Digiri ta ce, an kore mu saboda mun wuce lokacin da aka tsara, amma a nan Malam ya rubuta takarda mai zafi ya tura wa wannan Tsangaya, ya bayyana musu ba laifin mu ne ba, matsalar daga gare su take. Da suka fahimci haka, sai suka rubutu muna takardar ba da hakuri, aka amshi ayyukanmu aka ba takardar shaidar kammala karatun digiri na uku.
A lokacin da Malam yake duba ni, ya ba ni, ya ba ni kula irin wadda uba yake ba dan da ya haifa. A duk lokacin da nake Kano, a gidansa nake cin abincin safe da na rana da ma na dare. Haka kuma, idan zan taho gida, shi yake ba ni kuɗin da zan zuba wa motata mai da waɗanda zan yi wa yara tsaraba.
Malam, shi ya ɗora ni bisa hanyar da na zama abin da nake a yau, don kuwa shi ya fara sanya ni hanyar rubuta takarda aka buga a Mujallar Algaita ta Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami'ar Bayero. Haka kuma, shi ya sanya ni hanyar da na rubuta littattafai biyu daga kundin digirina na biyu, "Wanzanci da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa" da "Magani a Sha a yi Wanka a Buway". Bai tsaya a nan ba, don kuwa shi ya tilasta min mayar da kundin digirina na uku littafi, "Wanzanci da Sauye-,Sauyen Zamani".
Wasu muhimman abubuwa da na koya a wajen Malam sun hada da taimako da alheri da kyautata wa dukkan mutum ko da kuwa ba ka san shi. Kulla dankon zumunci tsakanin shi da dalibansa da waɗanda yake aiki tare da su. Duk lokacin da ya ji wani abu na murna ko bakin-ciki ya faru a gidanmu yana zuwa a yi da shi.
Wani abin ban sha'awa game da Malam shi ne, ba ya raina baiwar da Allah ya ba na kasa da shi, don kuwa, akwai lokacin da na je wajensa, ya rubuta wata takarda, sai ya miko min ita, ya ce, in duba ko akwai wani kuskure don ya gyara. Na amsa masa da cewar, ya zan kuskure a cikin wannan takarda, sai ya ce, a'a, in dai duba. Wannan ya nuna, Malam yana ba kowa dama wajen ilimi, bai dauka shi ya san komi ba.
A lokacin da na na zama Farfesa, na sanar da shi, murnar da ya nuna min, ko da Dr. Anas Sa'idu Muhammad Gusau, irin ta zai nuna masa.
Hakika, tarbiyyar da Malam ya koyi min, daidai take da irin wadda uba zai koya wa ɗan da ya haifa. Idan na watsar da ita ko ban amfani da ita ba wajen taimaka wa al'umma, na san, sai Allah Ya yi wa Malam sakayya a kai.
Malam ya ajiye aiki, amma na san bai gaji ba, don "ko gobe na san ruwa na maganin dauda".
A madadin dukkanin zuri'ar Muhammadu Sallau, Sarkin Askar Yariman Katsina, Hakimin Safana, muna taya Malam murnar ajiye aiki lafiya. Muna yi masa addu'ar, Allah Maigirma da Daukaka, Ya kara sa albarka cikin rayuwarsa da dukkan zuri'ar Malam Muhammadu Dankullum Gusau, Ya sa su gama lafiya, Ya sa Aljanna Firdausi ta zama makomarsu.
Mun gode kwarai bisa ga kulawar da ake nuna muna.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.