𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu Alaikum Malam nina kasance ina da aure to
amma matsalar danake fuskanta ita ce mijina baya iya biyamin buƙata hakan baya yimin dadi amma nakehurewa to hardai haƙurina yagaza idan yabiya buƙatarsa yatashi ni kuma
sainayi ƙoƙarin biyawa kaina buƙata to nadauki tsawon lokaci
ina'aikata haka 😭 gashi kuma nakasa daina
idan nadaina saina kuma cigaba wallahi abin yadameni narasa yandazan yi. Yanzu
haka kwatakwata sha'awata tadauke kome mijina zai yidani banajin komai
amatsayina namace ina cikin tashin hankali wllh. Ga infection yasani agaba
kulum inafama da fitar farin ruwa ga bushewa ahalin yanzu banafahimtar jindadin
mu'amala ta auratayya Inabuƙatar shawara dan Allah
𝐀𝐌𝐒𝐀👇
Wa alaikis salaam:- toh shawarar ke nan ki ji tsoron Allah,
ki ji tsoron haɗuwa da azabar ubangijin ki, ki tuna cewa akwai ranar
da za a ƙwantar da ke, daga ke sai
ayyukan ki, ki sani cewa ki saɓawa Allah na awa 1 tak
azabar shekara 1000 ne Allah zai miki, kiyi tunanin cewa azabar da ke cikin ƙabarin ki shin sha'awar ki na minti 10 zai iya ɗaukar sa? Kiyi tunanin cewa azabar da Allah zai miki ta
dalilin wannan jin sha'awar ki na minti 10 zai iya ɗaukar sa? Shakka babu wannan abun da kike aikatawa yana daga
cikin saɓon allah mafi girma, kiyi tunanin cewa shin idan kina
cikin aikata hakan sai allah ya ɗauki rayuwar ki, me za ki
gayawa ubangijin ki daga cikin ƙabarin ki har zuwa ranar
alkiyama? Shin kina cikin yin haka sai ga yaran ki ko mijin ki shin me za ki ce
musu kike yi?
Yar uwa ki ji tsoron Allah wannan
shi ne shawarar, duk wani abun da za ki yi matukar ba ki saka tsoron Allah a
cikin zuciyar ki ba, ba saka cewa lallai abun da kike yin nan azaba ce Allah yake
yi wa duk mai yi ba, ba ki tuna cewa lallai za ki mutu Allah ya je ya tambaye
ki ba, ba ki tuna cewa lallai idan kin mutu me za ki tarar a cikin ƙabarin ki ba, toh shakka babu ba za ki taɓa ɗena abun da kike yi ba, amma
idan kin saka tsoron allah a cikin ranki, kina tuna makomar ki, dole ne ki koma
ga Allah wajen dena wannan saɓon Allahn, amma idan ba ki
tuna komai ke kawai damuwar ki sha'awar ki ta biya, toh ki sani cewa za ki faɗa cikin ukubar Allah a ranar
alkiyama, ke ba za ki so a ce a ranar alkiyama hannayen ki ko kuma kin tashi da
ciki ba, duk mai aikata irin wannan a ranar alkiyama hannayen sa suna yin ciki
na azaba don haka kiyi gaggawan tuba zuwa ga ubangijin ki, ki yawaita
istigifari da ayyukan alkhairi allah zai yafe miki.
Shawara na Ƙarshe, Infection ɗin da kika ga yake yawan
miki kina Fitsari ko zubar Fitsari, ki Sani Cewa Wannan Biyawa Kanki Buƙatar shi ne ya jawo Miki Wannan abun, kin ga ke nan ke da
kanki kin jawo kanki Ciwo, sannan nan gaba bayan Lafiyar ki da hakan zai haifar
miki, toh ki sani Cewa Sha'awar na kin ma, nan gaba za ki nemi sa ki rasa.
Kin ga ke da
kanki za ki kashe kanki Matukar kin cigaba da yin hakan, Lafiyar ki zai taɓu yanzu ma kin fara ganin
haka, sannan Sha'awar ki ma zai dena za ki dawo tamkar ba ki jin komai game da
Sha'awar ko da ke za ki yi hakan da kanki ba za ki ji komai ba ki biyawa kanki buƙatar babu Abun da za ki ji, kin ga kin gama da kanki ke nan.
Duk Abun da aka ce muku Allah ya haramta shi ai Ubangiji ya fi mu sanin meyasa
ya yi hakan, amma sai mu rufe idon mu, mu aikata daga baya abun ya zo ya taɓa Lafiyar mu, mu zo muna
zare ido.
Meya sa a Lokacin da ke ba ki gamsuwa da Mijin ki ai sai
kiyi masa bayani Cewa ke fa Ƙwata-ƙwata ba ki jin komai, idan yana da Adalci da tausayi a Kullum
ko da Shi ya gama biyan buƙatar sa, sai ya jira ki ke
ma sai kin biya naki buƙatar haka zaman Aure yake,
amma bawai ɓangare ɗaya ya gamsu ɗayan bai gamsu ba kuma ɗayan ya bar shi, akwai
cutarwa ga hakan, in ma kin gaya masa ya Ƙi ai sai ki bi Hanyoyin da
Addinin ki ya ce a bi, ki nemi Waliyyan ku ki gaya musu.
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.