Ticker

6/recent/ticker-posts

Ga Ka Farfesa, Ga Ka Katibi Kan Adabi

Daga taskar Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau.

Prof Sa'idu Muhammad Gusau

GA KA FARFESA, GA KA KATIBI KAN ADABI
(PROF. SA'IDU MUHAMMAD GUSAU)

Jagora: Ga ka Farfesa,

: Sannu Farfesa Sa'idu Ɗan Muhammadu Na Gusau.

Jagora: Ga ka Farfesa, Ga ka katibi kan Adabi,

: Sannu Farfesa Sa'idu Ɗan Muhammadu Na Gusau.

'Y/amshi: Ga ka Farfesa, Ga ka katibi kan Adabi,

'Y/amshi: Ehhh! Ga ka Farfesa, Ga ka katibi kan Adabi,

: Sannu Farfesa Sa'idu Ɗan Muhammadu Na Gusau.

Jagora: Rabbu na gode da dubun basira da Ka ban,

: Kuma na gode da tulin basira Ka zuban,

: Falalar Allah da Ka ba ni a Watan Sha'aban,

: Ka tsare min ita kar ya zam ta zam tai nusau.

'Y/amshi: Ga ka Farfesa, Ga ka katibi kan Adabi,

: Sannu Farfesa Sa'idu Ɗan Muhammadu Na Gusau.

Jagora: Gaisuwa gun Mahmudu ɗan ƙabilar Arabi,

: Sayyadil Umma, ga cikamakin gun su Nabi,

: Sayyadil akalaƙi abin a dube shi a bi,

: Nayi tsanina da biyarsa sawu fa gasau.

'Y/amshi: Ga ka Farfesa, Ga ka katibi kan Adabi,

: Sannu Farfesa Sa'idu Ɗan Muhammadu Na Gusau.

Jagora: Yau akala na karkata na tunkari Gusau,

: Zan yabon masani mutafannunin nan na Gusau,

: Wanda yai harsasai kala-kala yamma yasau,

: A fagen ilmi yau da gobe ya zamma gasau.

'Y/amshi: Ga ka Farfesa, Ga ka katibi kan Adabi,

: Sannu Farfesa Sa'idu Ɗan Muhammadu Na Gusau.

Jagora: Wani yacce Ala me za ka kallo a Gusau,

: Wa ka ke so ka kwarzaza ka wasa a Gusau,

: In kuɗi anka baka ai Kano ta fi Gusau,

: Ko fagen bunƙasa da yalwata sun fi Gusau.

'Y/amshi: Ga ka Farfesa, Ga ka katibi kan Adabi,

: Sannu Farfesa Sa'idu Ɗan Muhammadu Na Gusau.

Jagora: Dakata, in ana ƙi gudu ba sa gudu ne,

: Yau da ka ji ana ga maɗi ba mai zuma ne,

: Ba kitabul ra'asi gunsu fesa shaihu ne,

: Ni ganau jiyau na zama a kan Sa'idu Na Gusau.

'Y/amshi: Ga ka Farfesa, Ga ka katibi kan Adabi,

: Sannu Farfesa Sa'idu Ɗan Muhammadu Na Gusau.

Jagora: Maƙurar Lauya idan ka ce SAN ai haka ne,

: Sanda duk ka ji gangaran gwanin Ƙur'an ne,

: Sanda duk ka ji an taru to fagen yaƙi ne,

: Maƙurar illimin zamani kwa Farfesa a sau.

'Y/amshi: Ga ka Farfesa, Ga ka katibi kan Adabi,

: Sannu Farfesa Sa'idu Ɗan Muhammadu Na Gusau.

Jagora: Wani Farfesa ne a ɓangaren turanci,

: Wani Daktor ne a ɓangaren larabci,

: Shi kwa mutafannuni a ɓangaren larabci,

: Kuma Farfesa ɓangaren Adab ɗa a Gusau.

'Y/amshi: Ga ka Farfesa, Ga ka katibi kan Adabi,

: Sannu Farfesa Sa'idu Ɗan Muhammadu Na Gusau.

Jagora: Masanin harshen Hausa Ɗan Muhammadu na Gusau,

: Masanin Lugga Hausa Ɗan Muhammadu na Gusau,

: Manazarci ne katibi da yammaye sau,

: Ya yi fintinkau, a tarar shi za ai ginsau.

'Y/amshi: Ga ka Farfesa, Ga ka katibi kan Adabi,

: Sannu Farfesa Sa'idu Ɗan Muhammadu Na Gusau.

Jagora: Adabin Hausa na yaba ka Farfesa Gusau,

: Manazarta ma kayi tubali sun ɗau sau,

: Littafan turke ba da barbarar Hausa kasau,

: Har da ta'alifai na saya da dama a Gusau.

'Y/amshi: Ga ka Farfesa, Ga ka katibi kan Adabi,

: Sannu Farfesa Sa'idu Ɗan Muhammadu Na Gusau.

Jagora: In yana larabci da za a sanya hijabi,

: Sai ka ce masa makkiyu kuma ƙabilar arabi,

: In yana turanci laka ta harshen adabi,

: Sai ka ce Banasare da yai ɓatan kai a Gusau.

'Y/amshi: Ga ka Farfesa, Ga ka katibi kan Adabi,

: Sannu Farfesa Sa'idu Ɗan Muhammadu Na Gusau.

Jagora: A fagen harshen Hausa gangaran ka fi gwani,

: In yana magana ba gura-gura ƙunƙuni,

: Sai ka ce Maɗari ke zuba da jera tunani,

: Ga azanci ga hikkima a gun ba gimsau.

'Y/amshi: Ga ka Farfesa, Ga ka katibi kan Adabi,

: Sannu Farfesa Sa'idu Ɗan Muhammadu Na Gusau.

Jagora: Alan waƙa ke yabonka don ka ɗara sau,

: A fagen waƙa kai rubutuka sun fice sau,

: Haka labaran ƙage kai nazar kansu a sau,

: Binciken Ala da yawansu taskarka Gusau.

'Y/amshi: Ga ka Farfesa, Ga ka katibi kan Adabi,

: Sannu Farfesa Sa'idu Ɗan Muhammadu Na Gusau.

Jagora: Shehu ɗan Shehu, Ɗan Muhammadu ɗan kullum,

: Shehu nai tammi a gurin Gusau ɗan kullum,

: Ɗan'uwan Malam, Shehu Na'ibin ɗan kullum,

: Ɗan'uwan Alƙali na Alƙalan yanzu Gusau.

'Y/amshi: Ga ka Farfesa, Ga ka katibi kan Adabi,

: Sannu Farfesa Sa'idu Ɗan Muhammadu na Gusau.

Jagora: Na taho murna yau ka ke bikin taka ɗiya,

: A walimar nan ta Sa'adatu taka ɗiya,

: Allah sambarka da zaman lumana amarya,

: A cikin waƙar gangaran na yakinmu tisau.

'Y/amshi: Ga ka Farfesa, ga ka katibi kan Adabi,

: Sannu Farfesa Sa'idu Ɗan Muhammadu na Gusau.

Jagora: Ga ka Farfesa, ga ka katibi kan Adabi,

: Sannu Farfesa Sa'idu Ɗan Muhammadu na Gusau.

'Y/amshi: Ga ka Farfesa, ga ka katibi kan Adabi,

: Sannu Farfesa Sa'idu Ɗan Muhammadu na Gusau.

'Y/amshi: Ga ka Farfesa, ga ka katibi kan Adabi,

: Sannu Farfesa Sa'idu Ɗan Muhammadu na Gusau.

Post a Comment

0 Comments