Ticker

6/recent/ticker-posts

Shehin Adabi Da Al'ada

Daga taskar Farfesa Sa'idu Muhammad Gusau.


SHEHIN ADABI DA AL'ADA
(PROF. SA'IDU MUHAMMAD GUSAU) 

Jagora: Allah Ahadi guda Ɗai ne,

'Y/amshi: Sarkin mazaje.

Jagora: Rabbul Alamina Shi Ɗai ne,

'Y/amshi: Sarkin mazaje.

Jagora: Mai Ƙuluhiya kun ga Shi Ɗai ne,

'Y/amshi: Wanda Yai mazaje.

Jagora: Rububiya kun ga Shi Ɗai ne,

'Y/amshi: Ikon mazaje.

Jagora: Tauhidin Kaɗaitaka Tai ne,

'Y/amshi: Sarkin mazaje.

Jagora: Sunansa ɗari fa ba ɗai ne,

'Y/amshi: Sarkin mazaje.

Jagora: Muhammadu Annabi ɗai ne,

'Y/amshi: Shugaban mazaje.

Jagora: Mai ida Risala Manzo ne,

'Y/amshi: Shugaban mazaje.

Jagora: Gare shi farin masoyi ne,

'Y/amshi: Sarkin mazaje.

Jagora: Mai koya a bautatamai ne,

: Mafakar mazaje.

 

Jagora: Shehin Adabi da al'ada,

: Sa'idu Gusau Furofesa mafakar mazaje.

 

Jagora: Shehin adabi da al'ada,

: Mamman na Gusau Furofesa mafakar mazaje.

 

'Y/amshi: Shehin Adabi da al'ada,

: Sa'idu Gusau Furofesa mafakar mazaje.

 

Jagora: Sa'idu Gusau ubana ne,

'Y/amshi: Ɗan maƙi garaje.

Jagora: Malam na Gusau masoyi ne,

'Y/amshi: Namijin mazaje.

Jagora: Shehi na Gusau Murabbi ne,

'Y/amshi: Ɗan maƙi garaje.

Jagora: Jigo na Gusau sadauki ne,

'Y/amshi: Namijin mazaje

Jagora: Malam na Gusau kadarko ne,

'Y/amshi: Ɗan maƙi garaje.

Jagora: Tsani ilimi adibi ne,

'Y/amshi: Namijin mazaje

Jagora: Rumbun adabi na ilimi ne,

'Y/amshi: Ɗan maƙi garaje.

Jagora: A yau a fagen karimi ne,

'Y/amshi: Namijin mazaje

Jagora: Ya zama fitilar Adibai ne,

'Y/amshi: Ɗan maƙi garaje.

Jagora: Gare su Gusau gadon bai ne,

: Mabiyar mazaje.

 

'Y/amshi: Shehin Adabi da al'ada,

: Sa'idu Gusau Furofesa mafakar mazaje.

 

Jagora: Ruhin adabi da al'ada,

'Y/amshi: Ɗan maƙi garaje.

Jagora: Jigon adabi da al'ada,

'Y/amshi: Namijin mazaje.

Jagora: Murhun adabi da al'ada,

'Y/amshi: Ɗan maƙi garaje.

Jagora: Domin ka a yau muke tsada,

'Y/amshi: Namijin mazaje.

Jagora: Ba donka ba tunni an kauda,

'Y/amshi: Ɗan maƙi garaje.

Jagora: Farin adabi farar tsada,

'Y/amshi: Namijin mazaje

Jagora: Shi ne atafa farar tsada,

'Y/amshi: Ɗan maƙi garaje.

Jagora: Satu muka yi fagen harda,

'Y/amshi: Namijin mazaje.

Jagora: Fannin na Gusau muke harda,

'Y/amshi: Ɗan maƙi garaje.

Jagora: Gatan adabi da al'ada Gusau mazaje.

 

'Y/amshi: Shehin Adabi da al'ada,

: Sa'idu Gusau Furofesa mafakar mazaje.

 

Jagora: Shi ne ya tsaya ya kalle mu,

'Y/amshi: Ɗan maƙi garaje.

Jagora: Ya kalli baza da raujinmu,

'Y/amshi: Namijin mazaje.

Jagora: Ya dubi zubi na waƙenmu,

'Y/amshi: Ɗan maƙi garaje.

Jagora: Ya dubi hawa da saukarmu,

'Y/amshi: Namijin mazaje.

Jagora: Zubi na kiɗi da waƙenmu,

'Y/amshi:      Ɗan maƙi garaje.

Jagora: Da yarda muke tunaninmu,

'Y/amshi: Namijin mazaje

Jagora: Tsari na daɓe a dagarmu

'Y/amshi: Ɗan maƙi garaje.

Jagora: Sai yai mana hurrumi namu,

'Y/amshi: Namijin mazaje.

Jagora: Kiɗan baka yakkiraye mu,

'Y/amshi: Ɗan maƙi garaje.

Jagora: Duba da salelaki namu,

: Zubin gidaje.

 

'Y/amshi: Shehin Adabi da al'ada,

: Sa'idu Gusau Furofesa mafakar mazaje.

 

Jagora: Yabi mu daki-daki namu,

'Y/amshi: Ɗan maƙi garaje.

Jagora: Ya tattara salsala tamu,

'Y/amshi: Namijin mazaje.

Jagora: Ya bibiyi talifai namu,

'Y/amshi: Ɗan maƙi garaje.

Jagora: A kan nazarin ladubbanmu,

'Y/amshi: Namijin mazaje.

Jagora: Yana nazarin gudunmuwarmu,

'Y/amshi: Ɗan maƙi garaje.

Jagora: A da wasu na ta ƙyamarmu,

'Y/amshi: Namijin mazaje.

Jagora: Basa nazari na aikinmu,

'Y/amshi: Ɗan maƙi garaje.

Jagora: Sun raina irin tunaninmu,

'Y/amshi: Namijin mazaje.

Jagora: Sun raina dukkan fa saƙonmu,

'Y/amshi: Ɗan maƙi garaje.

Jagora: Malam ya tsaya ya kalle mu,

: Gusau mazaje.

 

'Y/amshi: Shehin Adabi da al'ada,

: Sa'idu Gusau Furofesa mafakar mazaje.

 

Jagora: Waɗansu su ce abin kunya,

'Y/amshi: Ɗan maƙi garaje.

Jagora: Jigonsu guda na soyayya,

'Y/amshi: Namijin mazaje.

Jagora: Ba la'akkari da tarbiyya,

'Y/amshi: Ɗan maƙi garaje.

Jagora: Wai ba ilimi da tarbiyya,

'Y/amshi: Namijin mazaje.

Jagora: Wai ba hikima ta tsinkaya,

'Y/amshi: Ɗan maƙi garaje.

Jagora: Sai kauda ɗiyanmu kan hanya,

'Y/amshi: Namijin mazaje.

Jagora: Shehi na Gusau ya ce kayya,

'Y/amshi: Ɗan maƙi garaje.

Jagora: Kar kui musu fyaɗiyar Kanya,

'Y/amshi: Namijin mazaje.

Jagora: Cikinsu akwai na rauraya,

'Y/amshi: Ɗan maƙi garaje.

Jagora: Ku bi su da kyau da tsinkaya,

: Kada kui garaje.

 

'Y/amshi: Shehin Adabi da al'ada,

: Sa'idu Gusau Furofesa mafakar mazaje.

 

Jagora: Shehin Adabi da al'ada,

: Sa'idu Gusau Furofesa mafakar mazaje.

 

Jagora: Shehin Adabi da al'ada,

: Mamman na Gusau Furofesa mafakar mazaje.

 

'Y/amshi: Shehin Adabi da Al'ada,

: Sa'idu Gusau Furofesa mafakar mazaje.

 

Post a Comment

0 Comments