Ticker

6/recent/ticker-posts

Zambo Da Habaici A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai (5)

Habaici suka ce da ake yi kaikaice cikin wasu ɓoyayyun kalmomi na hikima masu ban sha’awa da ban dariya ga mai sauraro tare da cusa haushi da ban takaici da ɓata rai ga wanda ake wa. Habaici ba kai tsaye ake gane da wanda ake ba, sai wanda ya san abin da ke faruwa.

Zambo Da Habaici A Cikin Wasu Waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai (5)

 

NA

SHEHU HIRABRI
08143533314

Kayan Kiɗan Hausawa


BABI NA BIYAR

KAMMALAWA

5.0 Shimfiɗa

          Wannan babi zai yi bayanin kammalawa da yadda tsarin aikin ya kasance daga babi na ɗaya zuwa babi na biyar, sannan za a kawo sakamakon bincike da naɗewa. Haka kuma bayan naɗewa, manazarta da ratayen waƙoƙin makaɗa Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai za su biyo a ƙarshen aiki.

5.1 Kammalawa

          Wannan aikin bincike mai taken: “Zambo da habaici a cikin wasu waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai.” Na ɗauke da babi biyar. Babi na ɗaya shi ne gabatarwa da ke ƙunshe da shimfiɗa da bitar ayyukan da suka gabata da hujjar ci gaba da bincike da hanyoyin gudanar da bincike da muhallin bincike da kuma matsalolin bincike. A ƙarshe aka biyo da naɗewa.

          A babi na biyu an kawo taƙaitaccen tarihin rayuwar Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai mai ɗauke da haihuwarsa da iliminsa da iyayensa da matansa da yaransa da fara waƙarsa. Haka kuma an kawo jerin sunayen yaransa makaɗa da maroƙa da nau’o’in waƙoƙinsa da abubuwan da yake sha’awa. An kuma bayyana dangantakarsa da sauran makaɗa da kuma dangantakarsa da sauran al’umma. A ƙarshe aka kawo naɗewa da babin ke ɗauke da ita.

          A babi na uku an kawo bayanin asalin kalmar zambo da ma’anarta da ire-irenta tare da bayyana dalilin da ke sa a yi zambo. Haka kuma an kawo amfaninsa, sannan aka yi sharhin zambo a cikin wasu waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u da kuma bayanin naɗewa a ƙarshen babin.

          A babi na huɗu an tattauna habaici tun daga asalin kalmar da ma’anarta da ire-iren habaici da dalilan da ke sa ana yin sa tare da bayyana amfaninsa. Sannan aka yi sharhin habaicin tare da fito da shi a cikin wasu waƙoƙin Alhaji Musa Ɗanba’u Gidan Buwai. A ƙarshe an kawo naɗewa.

          Babi na biyar aka yi bayanin kammalawa tare da bayyana sakamakon bincike kamar haka:

 

5.2 Sakamakon Bincike

          Kamar yadda Bahaushe ke cewa: “Komai da ranarsa.” Wannan magana haka take, domin al’ummomi da dama sun ɗauki zambo da habaici a matsayi hanya ta ɓatanci da cin zarafi, a haka su ma masana da manazarta suka bayyana ra’ayoyinsu dangane da ma’anonin kalmomin biyu inda suka bayyana zambo a matsayin suka ta kai tsaye shi kuma habaici suka a kaikaice. Amma tare da haka sashen wannan aiki ya gano cewa zambo da habaici suna da matuƙar amfani ga jama’a a wurare daban-daban kamar haka:

1.     Zambo da habaici dukkansu taska ce ta adana adabin Bahaushe.

2.     Zambo da habaici na hana yin shisshigi wato mutum ya shiga sha’anin da bai shafe shi ba.

3.     Zambo da habaici dukkansu ado ne da ke ƙawata harshe musamman a cikin waƙa da kuma zantukan yau da kullum.

4.     Zambo da habaici na faɗakar da mutane ta hanyar sanin miyagun ɗabi’u ko ƙazafi ko wani abu na daban da jama’a ke zargin sa da shi.

5.     Zambo da habaici kan taimaka wajen ƙara soke abokin hamayya.

6.     Zambo da habaici na bayyana miyagun ɗabi’un mutum cikin hikima domin a kauce masa.

7.     Zambo da habaici na samar da nishaɗi ga mai sauraro. Yakan iya kasancewa hannunka-mai-sanda ga wanda ake wa.

8.     Zambo da habaici kan taimaka wajen mai da martani musamman ga sarakuna da masu mulki ta hanyar wani zalunci da suke yi wa talakawansu.

9.     Zambo da habaici a cikin waƙoƙi ko maganganu yau da kullum na ƙara bunƙasa harshe.

10. Zambo da habaici na taimakawa wajen huce haushin wanda ba a iya mayar wa raddi kai tsaye.

11. Ƙwarewa wajen yin zambo da habaici a cikin waƙoƙin siyasa da na sarauta na ƙara wa makaɗi ɗaukaka da farin jini ga wanda ba shi ake yi wa ba. Wanda aka yi wa kuwa, an tsira gaba ta har abada.

12. Ƙwarewa wajen yin zambo da habaici kan sa mawaƙi ko makaɗi ko maroƙi ya samu alheri.

13. Muhimmancin zambo da habaici ga al’umma har ya kai ga samun gurbi a cikin adabi da ake nazarin su a ƙananan makarantu da kwalejoji da kuma manya-manyan jami’o’i.

 

5.3 Naɗewa

          Wannan babi an yi bayanin kammalawa ne tare da bayyana yadda tsarin aikin yake, sannan an kawo sakamakon bincike inda aka gano muhimmancin zambo da habaici ga al’ummar Hausawa.

Post a Comment

0 Comments