Takardar Da Aka Gabatar A Taron Ƙara Wa Juna Sani Kan Gudunmawar Musa Ɗanƙwairo Maradun Wajen Bunƙasa Waƙoƙin Baka Na Hausa A Jami’ar Bayero, Kano A Ranakun Litinin 13 Zuwa Laraba 15 Ga Watan Satumba, 2021 A Harabar Jami’ar.
Tsafi Gaskiyar Mai Shi: Jirwayen Tsafi A Wasu Waƙoƙin Musa Ɗanƙwairo
Ibrahim Ɗalha
Government Day Senior Secondary School Birnin Kudu,
Ministry of Education Science And Tecnology, Dutse,
Jigawa state
Ƙibɗau: Ibrahimdalha1@gmail.com
Lambar Waya: 08060574254
Da
Muhammad Tukur Tanko
Niger State College of Education, Minna
Ƙibɗau: Tukur255@gmail.com
Lambar Waya: 07065915934
Da
Anas Umar
Sashen Harsunan Nijeriya
Shehu Shagari College of Education, Sokoto
Ƙibɗau: anascafu66@gmail.com
Lambar Waya: 08060079335
Tsakure
Wannan bincike mai taken “Tsafi gaskiyar Mai Shi: Jirwayen Tsafi A Waƙoƙin Musa Ɗanƙwairo.” An gudanar da shi ne da manufar lalubo tunanin Bahaushe game da tsafi a cikin waƙoƙin baka, inda aka yi turke da waƙoƙin Makaɗa Musa Ɗanƙwairo Maradun. An ɗora binciken kan ra’in “Buƙatuwar ɗan Adam (Theory of Human Needs)” wanda Abraham Maslow ya gano a 1943; daga baya Burtun ya ƙara faɗaɗa ra’in a wata maƙalarsa a 1979. Haka kuma, binciken kan iya hawa Bahaushen ra’i da ke cewa: “Tsafi Gaskiyar Mai Shi.” Kasancewar zomo ba shi kamuwa daga zaune, an bi wasu hanyoyin tattara bayanai da suka haɗa da tuntuɓar waɗanda ake ga suna da wata masaniya kan binciken da ake gudanarwa da rangadi ɗakunan adana bayanan ilimi (libraries) da kuma sauraren waƙoƙinsa daga bakinsa ta hanyar sauraren faifan memori, sai kuma wasu hirarraki masu alaƙa da binciken. An yi garkuwa da wasu ɗiyan waƙoƙi guda goma (10) waɗanda aka ciro su daga nau’o’in waƙoƙinsa guda huɗu(4). Nau’o’in waƙokin su ne: Waƙoƙin Manoma da na Sarakuna da na Hakimai(Iyayen ƙasa) da kuma na masu riƙe da muƙaman sarauta.Domin yin susa a gurbin da yake ƙaiƙayi, an lissafo tambayoyin bincike guda biyar waɗanda ake da yaƙinin samun amsa su shi ne isar da saƙon muƙalar. Binciken ya kalli ma’anar tsafi daga wurin masana daban-daban. A ɓangaren rabe-raben tsafi kuwa, binciken ya dogara da rabe-raben da Bunza, (2006:39) ya bayar a littafinsa. A ƙarshe, binciken ya sami zarafin fito da sakamakon bincike guda biyar (5) da shawarwari guda biyar. Daga cikin abubuwan da binciken ya gano sun ƙushi yadda Ɗanƙwairo ya fito da tsohuwar al’adar Hausawa da kuma yadda yake hannunka-mai-sanda kan wasu munannan al’adu da suka kauce wa koyarwar Addinn Musulunci.
1.0 Shimfiɗa
Ga al’ada, tunanin ɗan Adam ba ya wuce al’adarsa da ya gada iyaye da kakanni. Wannan ya sanya a duk wurin da Bahaushe yake, fasahohin
sana’o’insa da hikimominsa da ke ƙunshe a cikin salailan maganarsa da waƙokinsa suna ƙara fashin baƙin al’adarsa ne. Wannan dalili ya
sanya ake iya ƙyallaro al’adun
Hausawa ta hanyar nazarin fasahohin da ke ƙunshe a cikin waƙoƙin na baka. Irin
wannan tunani shi ya haifar da zamowar mawaƙan baka tamkar
wata ma’adanar al’adu da ke taskance
al’adunmu. Hakan ya taimaka ƙwarai wajen yi wa masana da manazarta ƙaimi inda suke bankaɗo kyawawan al’adun Hausawa da suka yi ɓatan dabo tare da ci gaba da maƙure al’adun da ke taƙin saƙa da addinin Bahaushe (Addinin Musulunci) a cikin waƙoƙin na baka. Irin
wannan yunƙuri shi ya haifar da ayyukan Balbasatu (2000) da Dunfawa (2003) da Sanyinawal
(2009) da Satatima (2009) da Bunza (2012) da Ibrahim (2013) da Rabi’u (2019) da
kuma Sifawa (2019). Kasancewar binciken yana da manufar fito da irin rawar da
Makaɗa Musa Ɗanƙwairo ya taka kan
gargaɗin waɗanda ke neman mayar da hannun agogo baya ta fuskar rayar
da al’adar da tuni hasken addinin Musulunci ya bishe su, binciken yana da tunanin fito da tunanin Bahaushe kan tsafi a taƙaice, sai kuma
daga baya a alaƙanta irin yadda tsafin ya yi katutu a rayuwar Hausawa da kuma dabarun da Ɗanƙwairo ya bi wajen
ankarar da al’umma yadda za su hana tsafin masauƙi a farfajiyar al’adarsu.
1.1
Fashin Baƙin Matashiya
Buƙatar daidaita akalar kalmomin matashiyar binciken, ita ta sanya a wannan muhallin za a bayyana ma’anar
kalmomin jirwaye da tsafi da kuma waƙa.
1.1.1
Jirwaye
Ƙamusun Hausa
CNHN, (2006:219) ya fassara kalmar jirwaye da: “Dabbare-dabbaren da ruwan da ya
zubo ko ya ɗigo kan yi wa jikin mutum.”
A wannan
bincike, an ɗauki ma’anar jirwaye da irin dabbare-dabbaren da al’adun tsafi
suka yi a ɗiyan waƙokin Musa Ɗanƙwairo ta
yadda mugunyar tsafin kan yi tasiri a
zuciyar mai gudanar da shi wanda har yakan hana masa yarda da sakamakon Mahalicci a dalilin wasu buƙatun zuciya da suka sha
gaban ransa.
1.1.2 Tsafi
A wannan bincike,
an kalli kalmar tsafi da ayyukan da Hausawa kan aikata da nufin neman ɗaukaka
ko wata buwaya ko kariya ko kuma kare martabar gado wanda aikata waɗannan
abubuwan sun ci karo da koyarwar nagartaccen tauhidin (sanin ilimin kaɗaita
Allah) da Musulunci ya zo da shi.
1.2.3
Waƙa
A
Ƙamusun Hausa CNHN,(2006:446)
an bayyana ma’anar waƙa da:
“Wata tsararriyar magana da ake rerawa a kan kari ko rauji.” Waƙe kuma shi ne yi wa wani mutum ko wani abu
waƙa.” Gusau, (2003:111)
yana ganin a ma’anar waƙa a matsayin: “Wani zance ne
shiryayye cikin hikima da azanci da yake zuwa gaɓa-gaɓa bisa ƙa’idojin tsari da
daidaitawa, a rere cikin sautin murya da amsa-amo na kari da kiɗa, sau da yawa kuma a tare da armashi.”
Ƙarƙashin wannan ma’ana da aka bayar, an fahimci waƙa a
matsayin sarrafaffen zance da aka ƙuƙƙulla shi cikin hikima, ake kuma rerawa da
rauji mai armashi ta hanyar hawa da sauƙa na muryar.
1.3
Manufar Bincike
A tsari na bincike, ba a son a gudanar da shi kara-zube
ba tare da bayyana manufar da ta ja hankalin mai bincike ya quduri aniyar
gabatar da binciken ba. Manufar wannan bincike ita ce, zaqulo gudunmawar Musa Ɗanƙwairo Maradun ta fuskar fito da wasu al’adun Hausawa tare da yayata
yadda suke a cikin ɗiyan waƙoƙinsa domin hannunka mai-sanda ga al’umma kan
aikata wasu miyagun ala’adu.
1.3 Maƙasudan Bincike
Daga cikin maƙasudan wannan bincike sun haɗa da:
1.
Fito da yadda Musa
Ɗanƙwairo yake kawo jirwayen tsafi a
cikin waƙoƙinsa.
2.
Lalubo hanyoyin da
yake amfani da su wajen nuna wa al’umma illar da ke tattare da tsafi.
3.
Zaƙulo irin tasirin
da jirwayen tsafi ya haifar ga masu sauraron waƙokinsa.
4.
Fito da saƙonnin da ɗiyan
waƙoƙin Musa Ɗanƙwairo masu ɗauke da jirwayen tsafi ke isarwa ga al’umma.
5.
Ƙalailaice dangantakar
da ke tsakanin tsafin da waɗanda ake dangantawa
da tsafin a cikin waƙoƙin.
1.4
Tambayoyin Bincike
Wasu daga cikin tambayoyin da binciken
zai sanya a gaba da nufin amsawa sun haɗa da:
1. Ta yaya Musa Ɗanƙwairo yake fito da jirwayen tsafi a waƙoƙinsa?
2. Waɗanne hanyoyi Musa Ɗankwairo yake
amfani da su wajen nuna wa al’umma illar da ke tattare da tsafi?
3. Wane tasiri jirwayen tsafi ya haifar ga masu sauraren waƙoƙin Musa
Ɗanƙwairo?
4. Waɗanne irin saƙonni ɗiyan waƙoƙin Musa Ɗanƙwairo ke isarwa ga al’umma kan
jirwayen tsafi?
5. Ta wacce hanya aka sami dangantaka tsakanin
tsafin da waɗanda ake dangantawa da tsafin a cikin waƙoƙin Musa
Ɗanƙwairo?
Matuƙar amsar waɗannan
tambayoyi suka fito a cikin wannan bincike, ana iya cewa layar binciken ta yi kyawun
rufi[1].
1.5
Hanyoyin Bincike
Gaskiyar Hausawa da sukan ce: “Idan raƙuminka ya ɓata kana iya regawa har cikin ramin gyare. A ƙoƙarin gudanar da
wannan bincike, an ɗan yi kazar-kazar irin na ƙananan ɗalibai ta yadda aka
ziyarci ɗakunan adana bayanan ilimi
(Libraries) inda aka sami zarafin leƙa wasu ayyuka masu alaƙa da binciken da
ake gudanarwa. Tuntuɓar wasu ɗaiɗaikun mutane da ke da alaƙa da wasu fadojin da
Musa Ɗanƙwairo ya yi wa waƙa ya taimaka ainun. An sami damar duba littafin Diwanin Waƙoƙin Musa Ɗanƙwairo da
Gusau,(2019) ya rubuta. Saboda maganar Hausawa da ke cewa: “Waƙa a bakin mai
ita ta fi daɗi.” An saurari wasu waƙoƙin da aka nazarta ta hanyar faifan memori.
Bugu da ƙari, shirin kundin mawaƙan Hausa da rediyon Tarayya na Kaduna (FRCN) yake gabatarwa, wanda suka
tattauna da Alhaji Ibrahim Muhammad (Ɗanmadamin Birnin Magaji) ya zamo tamkar
tsintuwar guru ne a cikin suɗi ga wannan bincike.
1.6
Ra’in Bincike
Nazarin tsaro ta ɓangarori guda biyu da suka haɗa da , tsaro na jiki da
kuma tsaro na gari[2],
shi ya buɗe tunanin wannan takarda ta kallon tsafi a matsayin wata hanya da
Hausawa kan bi a gargajiyance da nufin tabbatar da buƙatarsu ta tsaron kai da
kaya. Kasancewar tsaron kai da kaya a matsayin buƙatun ɗan Adam musamman ta fuskar zamantakewa, shi ya ba da haske a ɗora wannan bincike a kan ra’in
buƙatun ɗan Adam (Theory of Human Needs). Wannan ra’i dai Abraham Maslow ne ya ƙirƙiro shi a 1943 a cikin zanen da
ya yi mai hawa-hawa irin na dalar gyaɗa. Maslow ya kawo tsaro a matsayi
na biyu na buƙatun ɗan Adam. Bayansa kuma, an sami
wani masani mai suna Burton da ya
yi amfani da ra’in a wata takarda da ya
gabatar a 1979. Ado, (2019:112)[3]. Daga
cikin abin da Burton ya gano, ɗan Adam yana da buƙatar tsaro da walwala da tarayya da
wasu (ba ya son kaɗaici) da son ƙauna da burin a gan shi a wani matsayi da zai
iya wani abu na ƙwarewa kan aikinsa da kuma buƙatun samun wani matsayi na
rayuwa. Don haka wannan bincike yake hasashen, buƙatar cimma waɗannan
burace-burace shi yakan kai shi ga kauce wa hanyar da ya kamata a bi domin a
same su. Baya ga haka, wannan bincike kan iya hawa tunanin Bahaushe da ke cewa:
“Tsafi gaskiyar mai shi.”
2.0 Wane Ne Musa Ɗanƙwairo ?
Musa Ɗanƙwairo Maradun, wani shahararren Mawaƙi ne da aka yi a ƙasar Hausa. Tushensa daga ƙasar Zamfara ya fito.
Ayyukan Gusau, (1987) da Gusau, (2019) da Rabi’u, (2019) sun fito da abubuwan
da ya kamata a fito da su a rayuwarsa. Amma duk da haka, sunansa na yanka shi
ne Musa, sunan mahaifinsa Usmanu Ɗankwanagga, mahaifiyarsa kuma ana kiranta da
‘Yarnunu. Ya gaji kiɗa da waƙa daga wurin mahaifinsa. An haife shi a shekarar
1909 a garin Ɗankadu cikin Ƙaramar Hukumar Mulkin Talatar Mafara[4],
Jihar Zamfara. Ya koyi kiɗa da waƙa a wurin yayansa mai suna Abdu Kurna (Sarkin
Makaɗan Maradun). Babban Ubangidansa shi ne, Uban ƙasar Tsafe Alhaji Aliyu II .
Ya fara waƙa da waƙoƙin noma, daga nan kuma sai ya shiga waƙoƙin fada. Daga
bisani, ya ɗan taɓa waƙoƙin jama’a. Alhaji Musa Ɗanƙwairo ya rasu yana da
shekara 82 (1909-1991). Ya rasu ya bar matan aure da ‘ya’ya goma sha bakwai[5]
da jikoki da dama. Kuma wani abin
sha’awa, har yanzu gidan Ɗanƙwairo bai mutu ba, a yanzu haka (2021) jikansa[6]
ne ke riƙe da muƙamin Sarkin Makaɗan Maradun (garinsu Musa Ɗanƙwairo) kuma yana
tare da zuriyar Ɗanƙwairo suna ci gaba da tafiyar da sana’arsu ta kiɗa da waƙa.
Ba iya kiɗa da waƙa Ɗanƙwairo ya tsaya ba a lokacin da yake raye, yakan taɓa sana’o’in noma a lokacin damina da kuma kiwo.
2.1 Asalin Tsafi
Dangane da asalin
samuwar Tsafi a wurin Bahaushe, Bunza(2006:35) ya kalli asalin samuwar tsafi ne
ta tushen kalmar a farko, inda ya tabbatar da cewa:
“Kalmar
“Tsafi” asalinta daga Bahaushe take kuma ba hatsin bara ba ce.”
Sarkin Gulbi, (2013:746) ya tabbatar da
cewa:
“Samuwar tsafi cikin al’umma wani Mahadi ne
mai dogon zamani, domin babu wanda zai bugi ƙirji ya ce ga lokaci, ko wata
al’umma da suka fara aiwatar da tsafi. Hasali ma abu ne da ake iya samu a
kowace al’umma da ke a doron ƙasa tun a zamani mai nisa. Sannan kowace al’umma
da tsafin da take bugun gaba da shi wajen bautarsu da biyan buƙatun rayuwarsu.”
Ƙarƙashin waɗannan
bayanai da aka samu daga wurin masana, a na iya cewa, “Tsafi” yana daga cikin al’adun
Hausawa masu nisan zangon da ba za a iya tantance takamaiman wanda ya fara
gudanar da shi ba.
2.2 Ma’anar Tsafi
Ƙamusun Hausa CNHN, (2006:449) ya fassara kalmar tsafi da:
“Hanyar ba da gaskiya da wani abu
daban
ba Allah ba.”
Ibrahim,(1982:30)
ya nuna tsafi a matsayin:
“Ɗaya daga cikin addinin gargajiya na Hausa, sai dai irin wannan bauta ba
wani gunki ake sassaƙawa ana bauta masa ba.............”
Bunza, (1990:42) ya bayyana tsafi da:
“ Abin da ake nufi da tsafi ko
sihiri shi ne duk abin da fahimtar haƙiƙaninsa ya yi zurfi ko ya ƙayatar tare da gigitar da
hankulan masu gani ko kuma saurare, kuma ya kasance masu zurfin hankali da
tunani ne. A taƙaice dai ta bin hanyoyi da hulɗa da aljannu da shaiɗanu da kuma gabatar da
nau’o’in sadaka, da yanke-yanke tare da tattara himma waje guda da kuma
janye-janyen sunaye da faɗin waɗansu maganganu
barkatai, mai tsafi yake iya gudanar da tsafinsa.”
Bugu da qari, Bunza, (2006:35) ya sake fito da ma’anar
tsafi da cewa:
“ Wasu hanyoyi na gargajiya musamman yi wa
iskoki hidima da yanka da bauta domin biyan wata buƙata ko kuma ko samun wani amfani ko tunkuxe wata cuta.”
Adamu,( 2012:43). Yana ganin tsafi a matsayin:
“Samun tasirin gudanar da wasu abubuwa da suka
fi ƙarfin Ɗan’adam, ta hanyar tattara himma waje guda da nufin jawo ƙarfin aljannu da sheɗanu da faƙi da taurari don samun taimakonsu wajen gudanar da
abubuwan mamaki da razanarwa.”
Sarkin Gulbi, (2014:33) ya fito da ma’anar tsafi da:
“Hanya
ce da ta jagorancin imanin Bahaushe da sauran al’ummar da ke doron ƙasa dangane da haka, idan ana
magana a kan Tsafi ba komai ake magana ba, illa wata hanya ta bauta da al’umma
suka aminta da ita, wajen biyan buƙatunsu na yau da kullum da ake danganta da umurnin iskoki da hidimarsu.”
Har wa yau, Muhammad, (2015:62) ya kalli tsafi a mahanga
ta Addinin Musulunci inda yake cewa:
“Yin hidima ga wani abu wanda ba
Allah ne ba, ko yin wasu ayyuka na
musamman don neman biyan buƙata daga wanin
Mahalicci, ko yin wasu ayyuka na musamman don neman biyan buƙata daga wanin
Mahalicci ko neman taimakon waninsa kan al’amuran yau da kullum yana yiwuwa
wani abin da ake yi wa hidima ko neman taimakonsa ya kasance iskoki ko
duwarwatsu ko wasu halittu saɓanin Allah Mahalicci.
Bisa ma’anonin da aka zayyano, an fahimci cewa, Tsafi
wata tsohuwar hanyar bauta ce ta gargajiya, wadda ake amfani da ita da nufin
neman wata kariya daga cuta ko kuma neman wata ɗaukaka. A tsarin Mawaƙan baka na fada, sukan ɗauki waɗanda suka yi takarar
neman muƙamin sarauta da iyayen gidansu a matsayin abokan adawarsu, wannan ya
sanya sukan ɗauko duk wasu miyagun halaye da ɗabi’u su ɗora su a kansu da sunan
zambo.[7]
2.3 Tsafi A Tunanin Bahaushe
A ganin Bunza, (2006:39) duk wani magani da ya
ƙunshi sassan jikin ɗan Adam ko bayar da wata rayuwa ko
bayar da jini ko kiraye-kirayen iskoki ko aikata wani aikin assha[8]
Bahaushe yana kallon wannan abin a matsayin tsafi.
2.4 Ire-iren Tsafi
Bunza, (2006:39) ya karkasa rabe-raben tsafi kamar haka:
1.
Tsafin bauta.
2.
Tsafin buwaya.
3.
Tsafi na kare martabar gado.
4.
Tsafi na magani
2.4.1 Tsafin Bauta
Tsoron ɗan Adam na cutuwa daga wani abu da bai sani ba, tare da kwaɗayin sakamakon
wani aiki da yakan aikata, shi ne ya kawo masa tunanin bauta. A wannan haujin
Bahaushe kan yi wa iskoki hidima da nufin neman wasu kariya daga gare su . Bunza,
(2006:40) ya tabbatar da cewa: “Yi wa iskoki ɗa’a ga umarnin da sukan sanya
mutum na hani da horo, shi ne bautar.” Makaɗa Ɗanƙwairo ya fito da wannan saƙon
lokacin da yake wa wani ɗan sarki zambo
inda yake cewa:
Jagora: “Ga wani ɗan sarkin Keffi,
: Can
nig ganai cikin daji,
: Inda tsamiya, yana ta rawa,
: Yana
baya-baya ba ta gani,
Yara : Da ɗan ƙulƙi nai gun Magiro.[9]”
Gindi: Muhammadu Cindo bi da maza,
Mamman ɗan Mamman bajimi.
(Waƙar sarkin Keffi, Alhaji Muhammadu Cindo Yamusa).
A wannan waƙa Ɗanƙwairo ya fito
da hoton yadda ake wani tsafi na bauta a
garin Kwatarkwashi (a can baya, kafin wannan lokaci), domin ya nuna irin yadda
wani ɗan sarki ya manta da Allah ne ke bayar
da mulki ya koma tsafe-tsafen bauta da nufin neman mulki.
Har wa yau, a
lokacin da Ɗanƙwairo ke wa sarkin Gwambe waƙa, ya yi wa wani ɗan
sarki zambo, inda ya danganta shi da gudanar da tsafin bauta. Ga yadda yake
cewa:
Jagora: Ai ga wani ɗan sarkin
Gombe,
: Bai biɗa ga Allah ba,
: Ya sai babbaƙun tumaki,
: Ya sai babbaƙun shanu,
: Sai yak kirayi ‘Yanbori,
: Kullum ana yi mai goge, wawa,
‘Y/Amshi: Bokaye sun canye kuɗinka,
Jagora: Bokaye
‘Y/Amshi: Sun cinye kuɗinka,
Jagora : Ba shi ga Allah ba shi ga Annabi,
Ba shi ga
tsuntsu,
‘Y/Amshi: Ba shi ga tarko,
Jagora : Babu kuɗin kuma,
‘Y/Amshi: Babu sarauta.
Gindi : Gagari gaba gwauran giwa,
: Sarkin Gombe Shehu Na Abba.
(Waƙar Sarkin Gwambe, Alhaji Shehu Na Abba).
2.4.2 Tsafin Buwaya
Ga al’adar ɗan Adam bai cika son ƙasƙanci ba, wannan dalilin ne yakan sa ya yi duk
abin da ka iya yiwuwa da nufin samar wa abin da zuciyarsa take so (idan ba a yi
katari da wanda yake bin addini da gaskiya ba). Wanna ta sanya Makaɗa Ɗanƙwairo
ya fito da wannan nau’i na tsafi a cikin waƙarsa, saboda ya nuna wa masu
saurarensa yadda wasu sukan yi wasu ayyuka na kauce hanyar tauhidi da nufin
neman ɗaukaka. Misali, lokacin da Makaɗa Ɗanƙwairo yake cewa:
Jagora: Ga
wani ɗan sarkin ƙasar Tcahe,
: Yai baƙar
tagguwa yai baƙar riga.
Yara: Yai baƙin wando ga
baƙin rawani ga kai nai,
: In yai baƙi ƙirin ba ka gane shi,
: Sai nic ce wagga sabga ta tsahi ce.
Gindi: Shirya
kayan faɗa mai gida Tsahe,
Ali ɗan Iro bai ɗauki raini ba.
(Waƙar ‘Yandoto Tsafe, Aliyu II).
A tsarin Bahaushe, idan ya yi nisa a tsarin bautar iskoki
(bori) da camfi yakan riƙi wasu ɗabi’u su zame masa tada a gare shi, da nufin
neman ɗaukaka ko kuma wata kariya daga abubuwa masu cutarwa. Irin wannan tunanin Makaɗa yake so ya fito da shi domin
ya nuna yadda wani ɗan sarki ya shiga tsafi da nufin neman ɗaukaka.
2.4.3 Tsafi Na Kare Martabar Gado
Bunza, (2006:45) ya nuna idan Bahaushe ya gaji wata sana’a daga gidansu
akwai wasu asirrai da babu wanda zai san da su sai ɗangado. A sirran kuwa na
‘yan Tsafe-tsafen da aka saba ne, domin maganin mai son ya wulaƙanta sana’ar.
Makaɗa Ɗanƙwairo ya bayyana wannan nau’i na tsafi a lokacin da yake yabon wani
mai sana’ar noma da wanzanci a waƙoƙonsa na kiɗan noma. Ga bain da yake cewa:
Jagora: Wanzamai tsoronka sukai,
‘Y/Amshi: In dai an ka zana suna,
Kai ɗai aka
jira,
Jariri ba shi
askuwa sai ka zo.
Gindi: Ya riga su gona,
Mai kalmen
wuce maza ɗan Musa.
(Waƙar Giye Ɗanmusa)[10]
A wannan ɗan
waƙa Makaɗa ya fito da irin bajintar Giye Ɗanmusa ta mallakar magungunan
tsafe-tsafe na kare martabar gadon gidansu. Gaskiya ne, gadon gida alala ga
raggo. Kuma kowa ya tsare gadon gidansu bai karambani ba, in ji masu magana.
2.4.4 Tsafi Na
Magani
“A tsarin zamantakewa, cututtukan zuciya na neman biyan
buƙatar soyayya da farin jini da ɗaukaka waɗanda ake ganin idan ba a biya su ba
zuciya ta tawaya.” Ibrahim, (2002:366). Irin wannan yanayi, shi ne ya sa Bunza,
(2006:47) ya gano cewa: “Tsafin magunguna nau’in tsafi ne da Bahaushe ke yi
kawai bisa ga abin da rai ke so yadda yake son abin.” Makaɗa Musa Ɗanƙwairo
Maradun ya fito da irin wannan nau’i na tsafi a lokacin da yake ƙulla turken
zambo ga wasu ‘ya’yan sarakuna na Birnin
Gobir da na Tsafe. Ga abin da yake cewa:
Jagora: Wani ɗan sarkin Sabon Birni,
Bai samu
sarauta ba na ganai,
Ƙaura nig
gamu da shi,
Ga wuƙa tai a
hannu nai.
Amshi: Irin gidan Bawa Jangwarzo,
Na Sanda ya
ci garin arna.
Jagora: Ya ce tunda ban yi sarauta ba,
Ba ri yanzu
in ta batun tauri.
Gindi: Irin gidan Bawa Jangwarzo,
: Na Sanda ya ci garin arna.
(Waƙar Sarkin Gobir, Alhaji Ibrahim).
Kasancewar Shehu
Usmanu Ɗanfodiyo cikin Bunza, (2006:51) ya nuna tauri tsafi ne, wannan ta sanya
makaɗa ya nuna yadda wani ɗan sarki ya koma tsafi saboda bai sami sarauta ba.
Ya ci gaba da kawo wannan turke a ɗan waƙarsa, a lokacin da yake yabon sarkin
Tsafe Ahaji Aliyu ‘Yandoto II inda yake cewa:
Jagora: Ga wani na jayayya da Ali,
: Har yau bai fasa ba,
: Ya zo gun boka nai,
:
Wai a yo mai dibi,
: Da boka yad diba mai,
: Yac ce ba ka sarauta,
: Sai in ka ci tauri,
: A she magana mai sauƙi,
: Ya ci maganin icce,
: Kuma ya ci maganin ƙarhe,
: Bai sami sarautar Tcahe ba,
:
Sai tciga tat taso mai,
: A
gaida baran ɗan kurjal.
Yara :
Ƙi-gama ka bi jiki ka goge.
Gindi: Na Amadu baƙon dole,
:
Shi yak kashe wargi Ali,
:
‘Yandoto ana saunarka.
(Waƙar Sarkin Tsafe Alhaji AliyuII).
A wannan ɗan waƙa makaɗa ya fito da yadda wani ɗan sarki
ya riƙa cin maganin tauri domin ya zama sarki. A wannan wuri makaɗa ya yi haka
ne domin ya fito da turken nau’in tsafin magani da Hausawa suke amfani da shi.
3.0 Tafiya da Waiwaye
Mai Daɗi
Kasancewar Musa
Ɗanƙwairo dattijo ne da ya ratso sauye-sauyen zamani, yakan fito da turken wani
abu daga cikin ɗabi’un sarakunan wancan lokaci na bin dokokin addinin Musulunci
sau da ƙafa. Wannan dalili ya sanya da gaba ta koma baya ga wasu masu neman
mulki (inda wasu suka koma tsafe-tsafe). Hakan ta sanya da yake yabon sarkin Suleja
Alhaji Ibrahim inda ya fito da turken tauhidi domin ya nuna irin yadda sarkin
yake kwatanta biyayya ga addininsa na Musulunci sau da ƙafa. Ga abin da yake
cewa:
Jagora: Ba shi yab ban mamaki ba, wajen,
Sarki Ibrahim dubi irin
addu’a,
Da Sarki yai man,
Ƙwairo da munka zo
bankwana.
-------------------------------------------
Jagora: Bayan salatin Manzon Allah,
Ya ja La’ilahi sau goma,
Ya ja mani,
‘Y/Amshi: Rabbana Ataina[11]
had da,
Inna Fatahana[12]
yaj ja man.
-----------------------------------
Jagora: Ya ja mani Rabbana Ataina,
‘Y/Amshi: Had da Ƙul lan Yusibana[13]
yaj ja man.
Gindi: Mai ƙasas Suleja ɗan Musa,
Ba a kai maka wargin
banza,
Iro mai sulken hwaɗa na
Habu sarki.
(Waƙar Sarkin Suleja, Alhaji Ibrahim).
A cikin wannan ɗan waƙa, Makaɗa Ɗanƙwairo ya fito ƙarara ya nuna sarkin malami ne mai aiki
da koyarwar Addinin Musulunci kwatankwacin yadda magabatan baya su ka yi.
Wannan ta sanya yake nuna ta’ajibinsa gare shi ba don saboda kyautar da ya yi
masa ba. Don haka yake yayata shi da nufin zamowa abin koyi ga sauran al’umma baki
ɗaya.
3.1 Sakamakon Bincike
Daga cikin sakamakon da wannan bincike ya gano
akwai:
1.
Makaɗa da Mawaƙan baka suna taka muhimmiyar rawa a
waƙoƙinsu ta wajen fito da wasu tsofaffin al’adu da nufin hannunka-mai-sanda ga
jama’a.
2.
Takardar ta gano
yadda makaɗa Musa Ɗanƙwairo ya shigo da kashe-kashen tsafin Bahaushe a
waƙoƙinsa.
3.
Maƙalar ta gano yadda
gudanar da tsafe-tsafe kan yi tasiri ga masu neman buwaya da ɗaukaka musamman
ta fusakar neman mulki.
4.
Maƙalar ta gano
yadda Mawaƙa suke yayata wata ɗabi’a da
nufin ankararwa ba wai da nufin fito da ita domin a mayar da hannun agogo baya
ba.Wannan ta sanya a duk wurin da Musa Ɗanƙwairo ya ambaci wani nau’in tsafi,
cikin gaggawa yake komawa ya ambato turken tauhidi (kaɗaita Allah). Wani
lokacin ma yakan fara da ambato turken Tauhidi a matsayin shimfiɗa, kafin ya
shigo na tsafi.
4
Binciken ya gano
yadda al’adun al’umma suke da alaƙa da ayyukansu da tunaninsu na gudanar da
harkokin rayuwarsu.
3.2 Shawarwari
Daga cikin
shawarwarin da wannan bincike zai iya bayarwa sun haɗa da:
1. A kwai buƙatar Malamanmu na Addinin Musulunci su ƙara ruɓanya ƙoƙarinsu
wajen fito da hanyoyin karantarwa mafi sauƙi kan ilimin kaɗaita Allah (Tauhidi)
a tsakanin mutane. Wannan zai taimaka wajen ƙara bishe hasken fitilar tsafi da
take neman kunnuwa a yanzu musamman a sha’anin neman mulki.
2. Ya kamata ga masu zaɓen waɗanda za a naɗa sarakuna ko kuma al’umma masu zaɓen
shugabanni na siyasa, su ƙaurace wa duk wanda aka sami tabbataccen labari yana
hulɗa irin ta tsafi.
3. Yana da kyau matuƙa ga malamanmu da su ƙara fito mana da al’adun Hausawa a
cikin waƙoƙin mawaƙan baka da muke saurara.
4. Ci gaba da bitar saƙonnin Mawaƙan baka a makarantu wata dama ce ta ƙara
fito da al’adun Hausawa cikin sauƙi.
5. Ci gaba da haɗa irin waɗannan taruka tare da ƙara wa masu shirya tarukan
ƙarfin guiwa wata hanya ce ta ƙara tallata falsafar Bahaushe.
3.3 Naɗewa
A
ƙarshe, ko ba a ce komai ba, taron yau ya ƙara gwada mana
akwai ruwa a ƙasa sai dai in ba a tona ba. Da a ce, wasu ‘yan mu muka iya ne
suke da waɗannan Mawaƙa masu basira da hikima, da an ji bugun gaba irin na
ƙarin lamba. Don haka, Makaɗanmu da Mawaƙanmu sun bayar da tasu gudunmawa wajen
fito da saƙonnin da ke ƙunshe a al’adun Bahaushe da suka ƙunshi tarbiyya da haɗin
kan ƙasa da tattalin arzikin ƙasa da kuma faɗakarwa kan munanan ɗabi’u. Fito da
al’adun tsafi da Ɗanƙwairo ya yi a
waƙoƙinsa, wata hanya ce ta faɗakarwa ba don yana kira ga a yi tsafin ba.
Wannan ke daɗa tabbatar da cewa,
Ɗanƙwairo Mawaƙi ne da ya yi amfani da basirarsa wajen isar da saƙon addininsa
na Musulunci a waƙoƙinsa. Hakan ta sanya yakan kawo maganar tsafi da sigar gargaɗi ga ‘ya’yan sarakuna masu
neman mulki ko ta wacce hanya. Binciken ya gano, a duk lokacin da Ɗanƙwairo ya
ambaci wata ɗabi’a ta tsafi a cikin waƙoƙinsa, yakan yi gaggawar fito da turken
Tauhidi kafin ya faɗi ko kuma bayan ya faɗi nau’in na tsafin. Wannan ta gwada
mana Musa Ɗanƙwairo Mawaƙi ne mai tafiya da koyarwar Addininsa. Hakan ta sanya
bai kauce wa dokokin addininsa kuma bai ba wa tsafi mafaka ba. Madalla da abin
da Malam Mudi Sipikin yake cewa game da tsafi:
Camfi da ƙage rashin ilimi
ne,
Tsafi su bori rashin hankali
ne,
Aminci da su kau haƙiƙar ɓata
ne,
Da wauta da shirme da
sharholiya.
(Mudi
Sipikin: Waƙar Gadar zare)
Allah Ya ji ƙan
Musa Ɗanƙwairo Ya gafarta masa kura-kurensa. Amin!
[1] Salon magana ne
da ke nuna aikin binciken ya yi kyawu.
[2]Sarkin Gulbi, (2016:372), ya kalli
tsaro ta fuskar rabe-rabensa zuwa kaso biyu, wato tsaro na jiki da kuma na
gari. Ya ci gaba da cewa, tsaro na jiki
shi ne ya shafi dabarun kariyar kai daga cuta. Misali, magungunan tsari irin
su: Baduhu da layar zana da sagau da shashatau da sauransu. Tsaro na gari kuma,
ana yin sa ne domin samar da kariya ga gida da dukiya da gari da kuma yanki.
[3] Taken
takardar da ya gabatar ita ce: “Daviance, Terrorism and War: The Process of
Solving Unsolved Social and Political
Problems.”
[4] Yanzu tana ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar
Mulki ta Bakura, Jihar Zamfara.
[5] Cikin
‘ya’ya goma sha bakwai (17), goma maza ne bakwai kuma mata.
[6] Sunansa
Alhaji Muhammadu Ɗanjuma ana yi masa laƙabi da Jakkan kiɗi. Rabi’u, (2019:49).
[7] A
siyasar zamantakewar rayuwa, Bahaushe ya aminta da mai gaba da abokin gabarsa
amininsa ne. Wanna ta sanya, idan aka yi takarar sarauta, mawaƙa kan riƙa mayar
da martani ga abokan adawar wanda ya ci sarautar ta hanyar zambo da habaici da
sauransu. Wannan al’ada ita ta yi nisan da abokan adawar sarki na cikin gida
wato waɗanda suka yi takara da shi, sukan zama kamar abokan wasan makaɗa idan
aka duba yadda suke shigo da su cikin waƙoƙinsu tare da fito da kalmomin zambo
da ba’a da habaici a kansu.
[8] A
wannan haujin shi ne akan ga mutum yana aikata munanan ayyuka irin na Luwaɗi da
dangoginsu. makaɗa ya nuna takaicinsa da mamaki ga wani mai adawa da wani
mutuminsa da yake wa waƙa,
inda ya yi masa zambo da: Jagora: Kai ni hwa
abin ga ya ba ni mamaki,
: Ga mai
geme yana rawab bori,
: Al’amarin
ga ya zamo shiririta.
Gindi: Kak ka sake ‘yan maza,
: Su hwaɗa ma,
:Ɗan Umaru Sa’idu
Garkuwan Gwambe.
(Waƙar Garkuwan Gwambe,
Alhaji Sa’idu Umar Kumo)
[9]An yi ayyuka kan tsafin Magiro waɗanda
suka ƙunshi:
Mainasa,
S. (2001). “ Bautar Magiro A Ƙasar Zamfara.” Kundin Digirin B.A. Sashen Nazarin
Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu
Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Alhaji,
R. (2014). “Tsafin Magani: Taƙaitaccen Nazarin Kangida Da Nau’o’insa A Ƙasar Kwatarkwashi.” Kundin Digirin B.A.
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Muhammad,
U. (2015). “ Zumuntar Tsafe-tsafen Hausawa da akarkari.” Kundin Digirin M.A.
Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
A
cikin waɗannan ayyuka, an nuna tsafin Magiro da cewa,
Tsafi ne na bauta da aka yi shi a
Kwatarkwashi ( a shekarun baya masu nisa). A na gudanar da shi a shekara-shekara.
Tsafin yana da shugaba (Magajin Tsafi), a duk lokacin da za a yi shi, akan
ɗunguma da mutane da dabbobi a tafi wurin gudanar da tsafin. Idan masu Bautar
Magiro suka je a matsayin neman biyan wata buƙata sukan sayi turare da zakara
da sauran abubuwa, sai su je gindin iccen da ake zaton nan ne Mazaunin Magiro
tare da Magajin tsafi. Magajin tsafi zai fara ɗaga kansa sama yana kiari yana
cewa:
Gajiyere ba
dawa ba sare,
Gajiyere ba
dawa ɗan Inna,
Da kai aka zuwa
da kai aka dawowa,
In ka yarda mu
dawo, in ba ka yarda ba mu kwana can.
[10] Gusau (2019:68)
[11] Wannan
addu’a ita ce: “Rabbana Atina Fid duniya
hasanatan, wa fil Akhirati hasanatan.”
Allah Ka ba mu kyakkyawa a Duniya, da Lahira. Cfassarar Marubuta).
[12] Wannan
addu’ar ita ce: “ Inna fatahana La Ka Fatahan Mubina, Li Yagfirallahu Ma taƙaddama min zanbika, wa ma ta akhkhara, Wa
ya timma ni’imatuhu alaika, Wa yah diyaka siraɗal mustaƙiym. Wa yansurukallahu
Nasaran aziza.” Haƙiƙa an yi maka buɗi
mabayyani, domin Ubangijinka ya gafarta maka daga zunubanka waɗanda suka gabata
da waɗanda suka jinkirta, sannan ya cika ni’imarsa a gare ka, ya shiryar da kai
tafarki madaidaici, ya kuma taimake ka da nasara buwayayyiya. (fassarar
marubuta).
[13]“ Ƙul lanya sibuna illa ma kabahullahu
lana, Huwa Maulana, Wa alal Lahi fal yatawakkalul Muminun.” (Faɗa musu babu
abin da zai same mu face sai abin da Allah Ya rubuta a kanmu, Shi ne
Mujiɓincinmu, kuma gare Shi ne masu
imani sukan dogara. (fassarar marubuta).
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.