Wannan takarda ta ƙunshi nazarin Waƙar Sarkin Musulmi Abubakar Na III wanda Salihu Jankiɗi ya rera. An yi amfani da Mazhabar Tarken Gargajiya yayin wannan nazari.
Tarken
Waƙar
Sarkin Musulmi Abubakar Na III Ta Salihu Jankiɗi: Duba Zuwa Ga Mazahabar Tarken
Gargajiya
Idris
Abubakar
Gabatarwa
A wannan takarda da za a gabatar za a
yi tarken waƙar Sarkin Musulmi
Abubakar na III waƙa mai taken
“Abubakar Kashe Gwangwanin Maza” wanda makaɗi
Salihu Jankiɗi ya yi. Sannan za a ɗora
wannan nazarin ne ta hanyar la’akari da mazahabar Tarken Gargajiya. Ma’ana za a
ɗora aikin ne ya zuwa kan manufofin wannan mazahabar ta tarken
gargajiya. Amma kafin a shiga nazari kai tsaye, yana da kyau a yi ɗan
taƙaitaccen bayani dangane da wannan mazahaba
ta tarken gargajiya, domin wannan mazahabar ce za ta na haskaka mana hanya ko ɗora
mu a hanya wajen yin wannan tarke/nazarin. Mazahabar Tarken Gargajiya an ƙirƙiro ta ne tun
lokacin da aka fara nazari da tarken adabin al’ummomin duniya, har ya zuwa farkon
ƙarni na 19 lokacin da sabbin matarka
suka kunno kai. Tarken Gargajiya shi ne tarken da ake yi a can baya kafin
kafuwar makarantu ko hanyoyin tarke na zamani. Saboda haka, tarken gargajiya ne
ya mamaye fannin tarken adabi shekaru da dama da suka wuce. A taƙaice tarken gargajiya na nufin hanyar tarke da ta fi daɗewa
kuma da ta liƙe ma karatun
adabi, mai duba yanayin ɗan-adam da halayen ƙwarai.
Wannan mazahabar ta yaɗu ne a cikin duniyar tarken adabi a wajen ƙarni na 18 da 19 a Turai a ƙasashen Larabawa d.s.
Wannan mazahabar tana da wasu manufofi
da duk mai son yin tarken adabi zuwa ga wannan mazahabar zai yi la’akari da suw
ajen yin nazarinsa. Wasu daga manufofinta su ne:
Ø Duba
aikin wata fasaha a gargajiyance
Ø Neman
bayanin manazarci da tarihinsa da kuma zamaninsa
Ø Bayyana
ra’ayi game da aikin adabi, wato game da kyansa, ta amfani da zantukan yabo ko
kushe da malamai ke darajanta shi kamar kyau, da dama-dama, ko ba kyau, d.s. (Ɗangambo, 2007:7).
Ø Kawo
misalai kaɗan, amma babu cikakkiyar fiɗa
ta aikin adabi ko fito da ainihin manufofinsa.
Ø La’akari
da salo da nahawu da azanci da jigo da kyakkyawar manufa.
Ø Fito
da muhimmancin aikin kansa ko ƙarfin
harshen da aka rubuta aikin da shi.
Ø Ba
da wasu shawarwari yadda za a bunƙasa
aikin idan akwai wata naƙasa da aka gano
daga gare shi tare da la’akari da yadda aikin fasaha ke zama kamar wani madubi
na haskaka yanayin muhallin ɗan-adam.
Baya
ga waɗannan akwai kuma wasu matakan da ake son yin amfani da su
wajen tarken adabi a kan tarken gargajiya da ya shafi salon aiwatarwa kamar
haka:
-
Shin harshen fayyatacce ne?
-
Shin harshen ya yi dai dai da yadda mai magana da masu
sauraro ke ciki?
-
Shin harshen mai sauƙi
ne?
-
Shin harshen miƙaƙƙe ne (babu harshen damo)?
A
taƙaice waɗannan
su ne abubuwan da za su yi min jagora wajen yin wannan tarke na waƙar Sarkin Musulmi Abubakar na III, wanda Salihu Jankiɗi
ya yi masa waƙa mai suna
“Abubakar Kashe Gwamgwamin Maza”.
Bayanin
Tarken Wannan Waƙar
Wannan mashaba da muka yi bayani a
sama tana ɗaukar ra’ayin mutuntakar ɗan-adam.
A taƙaice za a iya cewa
mazahabar tarken gargajiya babu wata fitacciyar hanya ko rattaɓaɓɓiya
da aka tsara kuma ake amfani da ita. Sai dai hanya ce kara-zube dan bayyana
ra’ayi game da ingancin adabi (Ɗangambo,
2007:9) & (Gusau, 1992:12). Saboda wannan ne ma wannan mazahabar ta ginu a
kan wannan manufa, ta bayyana ra’ayi game da aikin adabi, wato game da kyansa,
ta amfani da zantukan yabo ko kushe.
Don haka a matsayina na mai atrken
wannan waƙar mai suna
“Abubakar Kashe Gwangwanin Maza” Na Salihu Jankiɗi
wanda ya yi wa Sarkin Musulmi Abubakar na III zan yi amfani da zantuttuka na
yabo ko kushewa da malamai ke darajanta shi da kalmomi yabo ko akasin haka
kamar yadda Ɗangambo (2007) ya
kawo na bayyana ra’ayina game da wannanw aƙa
na Salihu Jankiɗi ya yi wa Sarkin Musulmi Abubakar na III.
A taƙaice zantuttuka na yabo da kushewa da malamai suke amfani da
su wajen bayyana ra’ayi game da ingancin waƙa
ko adabi su ne kamar haka:
-
-
Ta burge ni
-
Ta waƙu Kyau mai daraja ta I
-
Ta yi
-
-
Ta yi kyau Kyau
mai daraja ta II
-
Ta gamsar
-
-
Dama-dama
-
Ɗan dama-dama Kyau mai daraja ta III
-
Ba yabo ba fallasa
-
-
Ba ta shige ni ba
-
Ba ta min ba ba
kyau
-
Ba tai kyau ba
A
taƙaice waɗannan
su ne irin kalmomin da ake amfani da su wajen bayyana ra’ayi game da kyan waƙa ko kushe ta. Don haka a matsayina na mai nazarin wannan waƙa na Salihu Jankiɗi
zan iya cewa “Ba ta shige ni ba”. Dalili kuma shi ne tun daga farkon waƙar har zuwa ƙarshe
babu wani al’amari da ya taɓo wanda zai nuna halayya
ko zamantakewa na ƙwarai a cikin
al’umma. Ya ƙare waƙarsa ne ta fuskar yabo kawai. Yana ta fifita sarkin Musulmi
Abubakar na III a kan kowanne sarki. Ni a gani na kawai Maula ce yake yi don
kansa ba don al’umma su saurara su amfana ba.
Don haka wannan waƙar kamar yadda na ambata a baya da cewa “Ba ta shige ni ba”.
Don haka na hukunta wannan waƙar
da “Ba kyau”. Ma’ana ita ce ajin ƙarshe
na darajojin da masana suka kawo wajen yanke hukuncin ingancin waƙa. Domin wannan mazahaba ta tarken gargajiya ta ban dama in
bayyana ra’ayina game da kyanta ko muninta ta hanyar amfani da kalmomin da na
ambata a baya.
Baya ga wannan, tarken gargajiya yana
neman bayanin mawaƙi ko makaɗi
game da tarihinsa da kuma zamaninsa. Ga ɗan
taƙaitaccen tarihin Salihu Jankiɗi
kamar haka:
Taƙaitaccen Tarihin Salihu Jankiɗi
Sunan mahaifinsa Alhassan, mutumin
Sakkwato ne kuma hadimin sarkin Sudan Nagwamatse. Mahaifin Jankiɗi
makaɗin kalangu ne, sannan ya yi wa sarkin Sudan Ibrahim waƙoƙi da dama. Mafi
yawa daga cikin waƙoƙinsa ya yi masa su ne a fagen yaƙi. Kakansa kuwa shi ne Gi’iye da ake yi wa laƙabi da “Ɗantigari
mai abin kiɗa”. Mahaifiyarsa kuma ita ce Hadijatu wadda ake yi wa laƙabi da “Umma Tsohuwa”.
Tarihi ya nuna an haifi Salihu Jankiɗi
a Rawayya ne wanda a halin yanzu take ƙarƙashin hukumar kwatarkwashi
a shekarar 1852. Makaɗi Salihu ya sami tarbiyya ta ddini da ilimin Musulunci mai
yawa. Hakan ne ma ya ba shi damar sawwara waƙoƙinsa tare da jefa kalamai na Larabci a ciki. Akan yi masa
kirari da cewa, “Da safe Malam, da yamma Maroƙi”.
Salihu shi ne sunansa na yanka, amma
ana masa laƙabi da Jankiɗi.
An ce ya sami laƙabin Jankiɗi
ne a lokacin da ƙanin mahaifiyarsa
ya je karɓan jinjirin da aka samu, sai ya lura da jan da Allah ya yi
masa sai ya ce “Barakallah wagga ɗa
Umma Jankiɗi”. Tun daga wannan lokaci wannan laƙabi ya bi shi.
Ƙuruciyarsa
Salihu Jankiɗi
ya buɗe idansa a Kwantagora a nan ne ya yi rayuwarsa ta ƙuruciya. Ya tashi yana yaro mai ƙarfi da kurari. Jankiɗi
ya yi dambe da kokawa da sauran wasu ayyukan samartaka na sha’awa saboda
kasancewar Salihu ta tashi cikin yaƙe-yaƙe kafin zuwan Turawan Mulkin Mallaka, duk abubuwan da ya yi
na yarinta na nuna ƙarfi da bajinta
ne.
Iliminsa
Salihu kamar yadda aka ambata a baya,
ya yi karatun allo inda har ya sauƙe
Alƙur-ani mai tsarki, ya kuma karanta
wasu daga cikin littatattafan addini kamar ƙawa’idi,
ishmawi, ahalari, da kuɗabi, d.s.
Koyo
da Fara Waƙa
Alhassan shi ne ya fara koya masa kiɗa
da waƙa inda ya soma kiɗi
har ya fara kaɗa kuntakuru wato kanzagi. Daga nan kuma ya shiga cikin
yayunsa mata masu amshi. Lokacin masu yi wa mahaifin nasa amshi su ne:
Ø Umma
Tsohuwa
Ø Aishatu
Ø Halimatu
Bakaba
Ø Salihu
Jankiɗi
Sannan
kuma yana da yara irin su:
Ø Aishatu
Ø Halima
Ø Bahago
Ø Ajiya
d.s.
Sannan
yana da mataimaka kamar su:
Ø Makaɗi
Ibrahim Ɗankaro
Ø Abdullahi
Ø Musa
Ɗangaladiman Labbo
Ø Muhammadu
Tambai d.s.
Sannan
kuma a wancan lokacin sa’o’insa a waƙa
akwai:
Ø Ibrahim
Narambaɗa
Ø Ibrahim
Gurso Mafara
Ø Buda
Ɗan Tanoma Argungu
Ø Aliyu
Ɗandawo
Ø Muhammadu
Sarkin Taushin Katsina
Bayan
rasuwar mahaifinsa ya ci gaba da kiɗan
kalangu a garin Kwantagora. A dalilin yaƙe-yaƙe Salihu ya tashi ya kama ƙasar
Anka. Daga baya ya koma Bungudu na ɗan
wani lokaci daga bisani ya sake komawa Kwantagora. Bayanw ani lokaci kuma sai
ya koma gida Rawayya a 1903-1915. Sai Jankiɗi
ya koma garin Tsafe har zuwa mulkin ‘Yandoto Abdullahi (1928-1948) ya
tashi daga Tsafe ya koma Gusa lokacin mulkin Sarkin Katsina Gusa Muh’d
mai akwai.
Jan-kiɗi
ya ji daɗin zaman Gusau inda ya mallaki gida babba da zuriya, akwai
inda yake nuna hakan a waƙarsa inda yake
cewa:
Jagora: Ni Jankiɗi ba ni zuwa ko’ina,
Y/amshi: Kwadain ba shi wucewa Gusau
Bayan da aka fitar da Sarkin Katsina
Gusau mai akwai, aka naɗa Shehu ɗan Sama’ila (1943-1945)
sai Salihu ya koma wajen Sarkin Musulmi Abubakar na III ya zama shi ne
ubangidansa. Sannan aka naɗa Jankiɗin
Sarkin Taushin Sarkin Musulmi.
Salihu Jankiɗi
ya yi waƙoƙi da dama a rayuwarsa, kaɗan
daga ciki sun haɗa da:
Ø Abubakar
Kashe Gwangwanin Maza
Ø Arziƙi ya yi kai as Sarki yau Sunusi ke Mulkin Kano
Ø Mai
Katsinawa Dikko Adili
Ø Jafaru
bajimi Ɗan Ishiyaku Sarkin
Zazzau ya haɗa maza
Ø Mujaddadi
ka-ke birni, Muhaddadi kake daji d.s.
Rasuwarsa
Salihu Jankiɗi
ya rasu ranar Juma’a 13 ga watan Oktoba 1973 a lokacin yana da shekara 120 a
duniya. Allah ya gafarta masa, amin.
A taƙaice wannan shi ne taƙaitaccen
tarihin Salihu Jankiɗi kamar yadda wannan mazahaba ta tarken gargajiya ta buƙaci mai nazarin da zai ɗora
aikinsa a wannan mazahabar dole ya kawo bayanai game da makaɗi.
Baya ga wannan, mazahabar tarken
gargajiya takan kawo misalai kaɗan, amma babu cikakkiyar
fiɗa da adabi dangane da manufarsa.
Dangane da wannan kuma, manazarci zai
fito da manufar (wato jigon waƙar)
ta hanyar kawo misalai kaɗan kamar yadda aka buƙata,
amma babu cikakkiyar fiɗa. A wannan waƙa
mai suna “Abubakar Kashe Gwangwanin Maza” na Salihu Jankiɗi.
Za a iya cewa manufa/jigon shi ne ZUGA. A wannan waƙa Jankiɗi ya nuna wa jama’a cewa Sarkin Musulmi Abubakar na III fa ya
zarce kowa. Don haka kar ma wani ya gwada ja da shi. Za mu tabbatar da haka
idan muka dubi waɗannan baitocin kamar haka:
Jagora: Fitila mai korewar duhu,
Sabulu mai wanke dauɗa,
Abubakar annurin duniya,
Farin ciki ya ƙaru ga kamai,
Ya kyautata wa
Musulmi hamdala.
‘Yan
amshi: Shugabanin sarkin duniya, Abubakar
Kashe gwangwanin maza.
Idan muka dubi waɗannan
baitocin za a ga Jankiɗi yana fifita Sarkin Musulmi ta hanyar zuga. Inda ya ƙira shi a matsayin fitila mai kawar da duhu, sannan ya sake
cewa shi sabulu ne mai wanke dauɗa,
da kuma shi annurin duniya ne. kamar yadda aka sani fitila dai takan sa wuri ya
yi haske don haka a nan an samu zuga sosai. Bayan haka an san cewa sabulu shi
ke kawar da duk wani dauɗa a nan ma an sami zuga sosai.
Haka zalika idan muka ƙara duba waɗannan za a tabbatar da
cewa Jankiɗi ya koɗa Sarki Musulmi Abubakar na III kamar inda yake cewa:
Jagora: Suna adawa tare da tsegumi,
Mahassada kun kwan da baƙin ciki,
Sun sake tsidau ya girma,
Abin da Allah ya yi ku hanƙuri,
Ku daina tsegumi ku
bi gaskiya.
‘Yan
amshi: Shugabannin sarkin duniya, Abubakar
kashe gwangwanin maza.
Idan muka duba waɗannan
ma, za a ga cewa Jankiɗi mahassadansa su yi haƙuri
su daina tsegumi su zo su bi gaskiya. Allah ya riga ya yarda Abubakar ya zarce
kowa.
Ya ƙara
wannan zuga inda yake cewa:
Jagora: Birnin Kano, Daura da Haɗeja,
A bi ku ba wata tantama,
Katsinawa har da zage-zagi,
A bi ku ba wata tantama,
Yarabawa har da Nufawa,
A bi ku ba wata tantama,
Gombe, Katagum har da Bauchi,
A bi ku ba wata tantama,
Shehun Barno da ba ya ya isa,
Sarkin musulmi shi ake son gano,
Kowa ya ga Shehu haƙiƙa ya gira,
Amshi: Shugabannin sarkin duniya, Abubakar
kashe gwangwanin maza.
A wannan wurin ma ya zuga Abubakar
inda ya kira garuruwa daban-daban a faɗin
ƙasarnan, sannan ya nuna duk mutanen
wannan yankin sarkin Musulmi suke son gani.
Sannan idan muka dubi amshin waƙar kanta zuga ne ta fuskar fifiko inda yake cewa “Shugabannin
Sarakin duniya, Abubakar kashe gwangwanin maza”. A nan ya nuna cewa duk faɗin
duniya a cikin sarakai babu ya sarkin Musulmi. Wato shi ne ma sarkin sarakuna,
sannan ya kira duk wani namiji da gwangwani in ba da sarkin Musulmi Abubakar na
III.
Wannan mazahaba ta tarken gargajiya
tana la’akari da salo da nahawu da azancin da aka yi aikin adabi. To a wannan
wuri za a yi nazarin salo da nahawu da azancin da suke cikin wannan waƙar na Sarkin Musulmi Abubakar na III.
Wasu masana na ganin cewa harshen wani
mutum shi ne salo. Salo wani abu ne wanda ya shafi wani mutum, wato ya bambanta
daga wani zuwa wani. Don haka a wannan nazari nawa zan fito da waɗannan
abubuwa na ga wane irin salo ne Jankiɗi
ya yi amfani da shi a wanna waƙar,
su ne kamar haka:
Ø Miƙaƙƙen salo: Wato salo
ne kai tsaye, mai sauƙin ganewa
Ø Salo
mai armashi: Shi ne salon da ya gamsar ta hanyar karsashi da burgewa
Ø Ragon
salo: Shi ne salo mai kashe jiki kuma marar gamsarwa
Ø Tsoho/sabon
salo: amfani da tsofaffin hanyoyi ko sabbi don isar da saƙo
Ø Salo
mai sarƙaƙiya ko mai tsauri: Salo ne mai wahalar ganewa. d.s.
Saboda
idan muka duba wannan mazahabar tana da wasu fitattun matakan yin tarke kamar haka:
i.
Shin harshen miƙaƙƙe ne? (Babu harshen damo)
Za a iya cewa harshen da
Jankiɗi ya yi amfani da shi ba kai tsaye ko mai sauƙin ganewa ba ne. Don haka za a iya cewa salon da ya yi amfani
da shi ne, shi ne “Tsaka-tsaki” shi ba mai sauƙi ba ne, sannan shi ba mai wahala ba ne.
ii.
Shin harshen fayyatacce ne?
Wannan harshe ba
fayyatacce ba ne domin karin harshen Lahajojin yamma ya fi yawa a ciki irin su
karin harshen Sakkwatanci, Zamfaranci, d.s.
iii.
Shin harshen mai sauƙi
ne?
A gaskiya wannan harshen
ba mai sauƙi ba ne akwai ƙaƙale a cikinsa.
iv.
Shin harshen ya yi daidai da yadda mai magana da masu sauraro
ke fahimta?
A’a, domin ba da
daidaitacciyar karin harshe ya yi amfani ba wajen yin wannan waƙar. Akwai kalmomi irin wagga, jegarai, kangarai, d.s.
v.
Shin harshen mai zaburarwa da motsa rai ne?
A gaskiya a nan salon
harshen da ya yi amfani da shi ba mai zaburaswa ba ne. za a iya cewa ya yi
amfani da lami/ragon salo wajen isar da saƙonsa.
Bisa
waɗannan matakai na yin tarke a wannan mazahabar zan iya dunƙule nazarin salo na wannan waƙar kamar haka:
Ø Zan
iya cewa salonsa a wannan waƙa
yana da salo na tsaka-tsaki.
Ø Sannan
ya yi amfani da tsohon salo a waƙar.
Ya yi amfani da kalmomi irin su:
-
Gwangwani
-
Warki
-
Fitila
-
Sabulu
-
Tsegumi
-
Tsidau
-
Rama
Duk
a matsayin tsofaffin kalmomi.
Dangane da nahawun harshe kuwa a
wannan waƙa ya yi amfani da
gajerun jumloli ne wajen isar da saƙonsa.
Dangane da azanci kuwa an samu
maganganun hikima kamar haka:
-
Fitila mai karewar duhu. A matsayin saye
-
Sabulu mai wanke dauɗa.
A matsayin karin magana
-
Baƙauye babu lissafi.
A matsayin baƙar magana
Sannan
Jankiɗi ya fito da ƙarfin
harshen Hausa a wannan aiki inda ya kawo karorin harshen Hausa a fakaice a waƙarsa kamar:
Kananci, Dauranci, Haɗejiyanci,
Katsinanci, Zazzaganci, Guddiranci, da Bausanci, d.s.
Sannan dangane da ba da wasu
shawarwari da wannan mazahaba ta nemi manazarci ya bayar ta yadda za a bunƙasa aikin idan akwai wata naƙasa da aka gano a gare shi.
A matsayina na ɗalibi
mai nazarin wannan waƙar na gano wasu naƙasoshi da dama dangane da yadda za a bunƙasa aiki. Su ne kamar haka:
-
Mawaƙin ya rinƙa amfani da salo na kai tsaye, mai sauƙin ganewa muddin ba zai amfani da daidaitaccen karin harshe
ba.
-
Sannan mawaƙi
a halin yanzu su daina amfani da tsofaffin kalmomi a waƙarsu domin shi ilmi a kullum yana tafiya ne da zamani.
-
Sannan mawaƙi
in zai yi waƙa ya daina amfani
da salon yarinta muddin saƙon
da yake son isar wa ba a yara ƙanana
ba ne.
A
taƙaice waɗannan
su ne irin shawarwarin da na bayar domin bunƙasa
wannan fanni.
Manazarta
Ɗangambo, A. (2007)
“Ɗaurayar Gadon Feɗe
Waƙa”.
Gusau, S.M. (1993). Jagoran Nazarin Waƙar Baka: Kano Benchmark publishers limited.
Zulyadaini, B. & Abba, M. (2000). Nazarin Waƙar Baka Published: Gaskiya Corporation limited, Zaria.
Rataye
Waƙar Abubakar Kashe Gwangwanin Maza Na
Salihu Jankiɗi Na Sarkin Musulmi Abubakar III
Jagora: Shugabannin sarakin duniya, Abubakar
Kashe gwangwanin maza
‘yan
amshi: Shugabannin sarakin duniya,
Abubakar Kashe gwangwanin maza
Jagora: Ka yi ba ya wargi ba, ya na Kangara,
Irin hali nai sai gagara
tauri,
Mu je ga gidadin mu lafiya,
Irin halin morin buɗar
jege rai.
‘yan
amshi: Shugabannin sarakin duniya,
Abubakar Kashe gwangwanin maza
Jagora: Fitila mai korewar duhu,
Sabulu mai wanke dauɗa,
Abubakar annurin duniya,
Farin ciki ya ƙaru ga komai,
Ya kyautata wa Musulmi
hamdala.
‘yan
amshi: Shugabannin sarakin duniya,
Abubakar Kashe gwangwanin maza
Jagora: Ai idan masara tambutuƙa sai Yamal,
Sun sani abokai sarkin
Musulmi,
Shehu da kansa kai shuka ya
isa.
‘yan
amshi: Shugabannin sarakin duniya,
Abubakar Kashe gwangwanin maza
Jagora: Ka yi ba hassan ba karin sai wagga ka faɗa,
Ka san mutuncin sarki ya fi,
San sakar ruwa da kan shuka
sai yau.
‘yan
amshi: Shugabannin sarakin duniya,
Abubakar Kashe gwangwanin maza
Jagora: Suna adawa tare da tsegumi,
Mahassada kun kwan da baƙin ciki,
Sun sake tsidau ya girma,
Abin da Allah ya yi ku hanƙuri,
Ku daina tsegumi ku bi
gaskiya.
‘yan
amshi: Shugabannin sarakin duniya,
Abubakar Kashe gwangwanin maza
Jagora: Ai san ka ta rama sai ka hankali,
Kun san baƙauye ba zai gagarai ba,
Sama babu lissafi.
Ku gagarai haddasa a yi sarki
mandamo.
‘yan
amshi: Shugabannin sarakin duniya,
Abubakar Kashe gwangwanin maza
Jagora: Birnin Kano, Daura da Haɗejiya,
Katsinawa har da Zage-zagi.
Amshi: A bi ku ba wata tantama
Jagora: Yarabawa har da Nufawa,
Gombe, Katagum har da Bauchi
Amshi: A bi ku ba wata tantama/
Jagora: Shehun Borno da ba ya isa,
An gwada ma da ainihin
gaskiya,
Duniya har da ta ku
tahukunta,
Sarkin Musulmi shi ake son
gani,
Kowa ya ga Shehu haƙiƙan ya gira,
Gafara sosai ya tsira (duk ku
taso ku shiga aljanna).
‘yan
amshi: Shugabannin sarakin duniya,
Abubakar Kashe gwangwanin maza
Jagora: Shugabannin sarakin duniya, Abubakar
Kashe gwangwanin maza
‘yan
amshi: Shugabannin sarakin duniya,
Abubakar Kashe gwangwanin maza
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.