Ticker

6/recent/ticker-posts

Salon Hira A Waƙoƙin Bara: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Salisu Sa’in Makafin Zazzau

Waƙoƙin bara waƙoƙi ne da ko dai mabarata ke shiryawa ko kuma suke  amfani da su wajen bararsu. Wasu mabarata kan shirya ‘yan waƙe-waƙe na begen Annabi (SAW) da kuma wasu waƙoƙin da ke tattare da gargaɗi da karantarwa domin rerawa ga jama’a. Babu wani lokaci takamamme da suka keɓe domin yin bara. Sukan yi bara kowane lokaci wato safe da rana da yamma, kai har ma a cikin dare (Sarkin Gulbi 2007: 49-50).

Salisu Sa’in Makafin Zazzau

Salon Hira A Waƙoƙin Bara: Nazari Daga Wasu Waƙoƙin Salisu Sa’in Makafin Zazzau

Abdullahi Mujaheed
mujaheedabdullahi@gmail.com
+2348069299109, +2348156747550
Jami’ar Jihar Kaduna

Rabiu Bashir
+2348035932183, +2348022261880
Jami’ar Jihar Kaduna
   

1.0 Gabatarwa

Nazarin salo gona ce babba mai kunyakai da yawa; shi ya sa kowane manazarci sai dai ya ɗebi iya kadadar da zai iya nomewa daidai da manufar nazarinsa. Masana irinsu Mukhtar (2004) da Yahya (2001) da Garba (2012) da sauransu sun sha rubdugu kan wannan fage na salo a mabambantan lokuta cikin ayyukansu. Daga ayyukan ire-iren waɗannan masana, an gano cewa ba komai ba ne salo illa dabara ta isar da saƙo. Shi ya sa salo ke taka muhimmiyar rawa wajen isar da saƙo a cikin aikin adabi; walau a waƙa ko a zube ko kuma a wasan kwaikwayo. Saboda haka mawaƙa suke amfani da salo wajen ƙawata waƙa domin isar da saƙo cikin dabara da azanci mai armashi. Har ila yau, duk da kasancewar Salisu Sa’in Makafin Zazzau mabaraci, amma ya kasance ma’abocin sarrafa salo a cikin waƙoƙinsa na bara domin isar da saƙonninsa cikin armashi. Har ila yau, an lura cewa salon hira yana sahun gaba cikin irin salailan da yake amfani da su a waƙoƙinsa. Saboda haka, alƙiblar wannan takarda ita ce nazarin salon hira a waƙoƙin bara na Salisu Sa’in Makafin Zazzau. Sai dai kafin nan, za a yi tsokaci game da salo da waƙoƙin bara. Sai kuma tarihin Sa’in Makafin Zazzau a taƙaice. Daga bisani kuma a ƙwanƙwance salon hira a waƙoƙin Sa’in Makafin Zazzau.

2.0 Salo a taƙaice

Salo muhimmin al’amari ne a Hausa, don haka a yayin da (Yahya, A. B. 2001:1-3) yake nazarin salo ya riƙa kawo misalai da wasu zantukan Hausawa game da salon inda sukan ce, “salon magana” idan an yi wata magana daban da yadda aka saba yin ta yau-da-kullum. Haka kuma manazarcin ya ƙara da cewa, Hausawa kan ce, “sabon salo” wanda ke nufin sabuwar hanya ta daban da yadda aka saba da wani al’amari. Sannan kuma “sabon rawa” a Hausa yana nufin wata dabara ko hanyar yin rawa. Yahya ya ci gaba da cewa idan Bahaushe ya ce, “sabulun salo” yana nufin sabulun da aka bi wata hanya ta daban wajen yin sa. A ƙarshe ya bayyana salo da cewa dabara ko hanya ko wayo. Ko kuma kwalliyar magana ce mai tasiri a kan mai jin ta. Haka kuma salo shi yake bayyana saƙo, shi ke kai saƙo inda aka nufa da shi. Salo dabara ce ko hanya mai yin kwalliya ga abu domin abin ya kwarzanta ko ya bayyana. Duka-duka dai,

Salo yana nufin duk wata dabara ko hanya a cikin waƙa wadda aka bi domin isar da saƙo. Ita wannan dabara ko hanya tana yi wa waƙa kwalliya ta yadda saƙon zai isa ga mai saurare ko karatun waƙar (Yahya, 2001:3)

Salo a waƙoƙin baka wata hanya ce da makaɗi ke kyautata zaren tunaninsa cikin azanci domin ya cin ma burinsa na isar da saƙo a waƙa.  salo a waƙoƙin baka abu ne wanda yake daɗa fito da ainihin kyansu ko muninsu, ta haka za a iya gane waƙoƙi masu karsashi, masu hikima da balaga da kuma waƙoƙi marasa ma’ana, marasa inganci. Salo ke nan ma’auni ne na rarrabe zaƙin waƙa ko ɗacinta.  Salo kuma hanya ce ta sarrafa harshe a jujjuya shi ta yadda za a iya taƙaita manufa ko a sakaya ma’ana ko kuma a kaifafa tunani. Za a iya karkasa salon sarrafa harshe zuwa gidaje guda biyu wato adon harshe da kuma aiwatar da shi. (Gusau, S.M. 20003:53-54).

Salo yana da wuyar ganewa duk da yake dai ana iya gane wasu sigoginsa.  “salo shi ne hanyoyi ko dabarun isar da saƙo”. Kuma salo ya ƙunshi zaɓi a cikin rubutu ko lafazi sannan kuma daɗi ko armashin zance da ingancinsa ya dogara ne game da yadda mai magana ya zaɓo kuma ya saƙa kalmominsa a kan kyakkyawan tsari wajen isar da saƙonsa (Ɗangambo, A. 2008:34).

 Don haka salo azanci da basirar fasihai ne wajen ƙulla tunani, salo kan takure ma’anar abin da ake magana cikin ‘yan kalmomi. Salo yakan bayar da hoton abu ko al’amari cikin bayani, yakan ƙunshi kwalliya ko tamka ko alamci ko mutuntawa ko dabbantarwa ko ƙarangiya ko kinaya ko jerin sarƙe ko ɗinkin baiti ko salo-rakwacam da sauran azancin magana, waɗanda sukan ɗarsu a zuciyar mai saurare ko karatu ya yi zurfin tunani a kansu. Salo shi ne yadda harshen fasihai ke bayyana hoton zuciyarsu. Salo na iya zama duk wani abin da ya kyautata magana, ya ƙawata ta a zuciyar mai sauraro. Sannan kuma sauƙi ko tsaurin salo ya danganci lokacin da fasihai suka yi ƙirƙira, ƙwarewar mai sauraro game da harshe ma yakan taimaka a fahimci salo.

3.0 Waƙoƙin Bara

Waƙoƙin bara waƙoƙi ne da ko dai mabarata ke shiryawa ko kuma suke  amfani da su wajen bararsu. Wasu mabarata kan shirya ‘yan waƙe-waƙe na begen Annabi (SAW) da kuma wasu waƙoƙin da ke tattare da gargaɗi da karantarwa domin rerawa ga jama’a. Babu wani lokaci takamamme da suka keɓe domin yin bara. Sukan yi bara kowane lokaci wato safe da rana da yamma, kai har ma a cikin dare (Sarkin Gulbi 2007: 49-50). Shi ya sa Muhammad (1983), ya ce ta hanyar bara, Namangi ya fara shirya waƙoƙinsa waɗanda galibi jigoginsu na addini ne. Wasu mabaratan kuwa sukan ɗauki waƙoƙi ne da wasu mawaƙan suka wallafa su riƙa amfani da su wajen jawo hankalin mutane su ba su sadaka. Da irin wannan tunani ne Bunguɗu (2015:104-105) ya bayyana waƙar bara a matsayin waƙar da mabaraci/mabarata ke amfani da ita yayin da yake/suke aiwatar da baransa/su. Ana kiran su waƙoƙin bara domin amfani da ake yi da su wajen aiwatar da bara. Waƙoƙin da ake bara da su sukan kasance na baka ko rubutattu. Na bakan su ne waɗanda tun a wajen samar da su an ƙudurci tsara su ne saboda a yi bara da su, mafi yawa domin almajirai. Akan kuma sami wasu waɗanda ba almajirai ba ne sai dai domin sauran mabarata manya, amma haka bai hana su ma wasu almajirai su yi amfani da su wajen bara ba. 

Kamar dai yadda Ampah da Babajo, (2009), suka nuna cewa waƙoƙin bara na almajirai suna sanya tausayi ga zukatan masu saurare har su ba su sadaka. Haka kuma Almajirai suna zagayawa yawon bararsu ne gida-gida; da safe ko da maraice domin neman abinci. Suna yin haka ne ta hanyar yawo da kwanukan cin abincinsu, suna rera wasu waƙoƙi. Saboda haka,  waƙoƙin bara waƙoƙi ne da suka ƙunshi jawo hankalin masu saurarensu domin su rinjayu da saƙon da mabaratan/almajiran suke isar masu, (Ampah da Babajo, 2009).

Daga abin da ya gabata, za a iya cewa waƙar bara da waƙoƙin mabarata abubuwa biyu ne masu yi wa juna shigar giza-gizai, domin kuwa duk waƙar da ake amfani da ita yayin da ake gudanar da bara ta kasance waƙar bara, ko da kuwa ba mabaracin ne maƙirƙirinta na asali ba. Sa’annan kuma akwai waƙoƙin da mabarata ke tsarawa da ba na barar ba, hasali ma waƙoƙi ne masu mabambantan jigo kamar na sauran mawaƙa gama-gari. Salisu Sa’in Makafin Zazzau ɗaya ne daga cikin irin waɗannan mabarata, waɗanda suka rikiɗe mawaƙa daga bisani. A cikin waƙoƙinsa akwai waƙoƙin bara kamar ‘Barar Zamani’ da ‘Waƙar Yabo’ da sauransu. Akwai kuma waƙoƙinsa a matsayinsa na mabaraci waɗanda ba barar ce manufarsu ba, ba kuma saƙon barar ne a cikinsu ba, misali,‘Waƙar Rajista’ da ‘Gargaɗi ga Masu Shanƙwaya’ da sauransu, (Mujaheed, 2017).

4.0 Salisu Sa’in Makafin Zazzau Cikin Tarihi

An haifi Sa’in Makafin Zazzau, cikin shekarar 1933 a ƙasar Daura, daga bisani kuma shi da iyayensa suka baro ƙasar Daura da ƙuruciyarsa, suka koma Rafin-Mai-Baka. Cikakken sunansa shi ne Salisu Abdullahi Rafin-Mai-Baka, kuma iyayensa ba makafi ba ne. Ya sami lalurar makanta ne tun bai wuce kwanaki arba’in a duniya ba,bayan ya yi fama da  cutar ƙyanda. Duk da haka, ya yi karatun addinin Musulunci gwargwado a lokacin ƙuruciyarsa, sai dai bai samu yin karatun boko ba (Mujaheed, 2017).

Cikin shekarun 1960 Sa’in Makafin Zazzau ya koma birinin  Zariya da zama, inda ya zauna wajen maigidansa mai suna Sa’i Ibrahim ɗan Tofa wanda daga gare shi ne Salisu ya sami sarautar ‘Sa’in Makafi’ bayan rasuwar Sa’i Ibrahim ɗan Tofa. Daga bisani ya koma garin Kaduna da zama a farkon shekerun 1970. Sa’in Makafin Zazzau ya kasance ma’abocin hulɗa da gwamnati domin yana waƙoƙin farfaganda da yaɗa manufofin gwamnati.  Shi ya sa bayan shahararsa, kusan kowane lungu na arewacin ƙasar nan da kudu-maso-yamma babu jihar da bai sanya ƙafarsa ba, ko dai a karan kansa, ko kuma gayyatar sa ake yi, (Mujaheed, 2017).

Salisu Sa’in Makafin Zazzau ya yi zaman aure da mata uku lokaci guda, wato Rabi da Amina da Yalwa. Ko da yake ya auri wasu matan a mabambantan lokuta. Haka kuma ya haifi ’ya’ya goma sha uku, cikin goma sha ukun nan, goma maza ne, uku mata. Sa’annan cikin wannan adadi, uku suna raye, goma kuma sun rasu, (Mujaheed, 2017).

Bugu da ƙari, an naɗa Salisu Abdullahi a matsayin Sa’in Makafin Zazzau a shekarar 1968, lokacin Sarkin Makafi Umaru. Kafin naɗin, ana kiran sa ‘Wazirin Samari’ ne. A ƙarƙashinsa kuma, akwai yaransa da suke masa amshi waɗanda kowannensu da sarautarsa, (Mujaheed, 2017).

Dangane da waƙa kuwa, Sa’in Makafin Zazzau bai gaji waƙa ba, walau ta wajen mahaifi ko mahaifiyarsa, basira ce Allah (SWT) ya ba shi daga waƙoki na bara, har ya kai ga shahara ga waƙoƙi na fadaƙarwa da isar da saƙonnin gwamnati ga al’umma. Ya fara waƙa ne tun yana Kano, musamman a lokacin da yake tare da ubangidansa Magaji na Ɗambatta, wanda aka ƙaddara shi ne ya koya masa waƙoƙin baran. Har ila yau, ya daɗe yana ‘yan waƙoƙinsa na bara, kafin shahararsa a wajajen shekarun 1965/1966 sakamakon rikicin juyin mulkin da ya kunno kai a lokacin. Wannan ne ya haifar da waƙarsa ta “Soja” wadda ta shahara sosai kuma ita aka fara sanyawa a gidan rediyo domin fadaƙar da jama’a dangane da muhimmancin haɗa kan ƙasa, (Mujaheed, 2017).

Daga wannan lokaci, duk abin da ya tusgo daga manufofin gwamnati da take buƙatar a jawo hankalin jama’a, ko a gargaɗe su, sai Sa’in Makafin Zazzau ya shirya waƙa a kan abin, ya riƙa rera ta yayin da yake bararsa. Idan ‘yan jarida suka ji shi, sai su ɗauka su watsa a gidajen rediyo. Da abin ya ci gaba, tun yana yi a matsayin sa-kai, har ya kasance gwamnati ko hukumomin gwamnati musamman Hukumar Watsa Labarai da Gidan Rediyon Tarayya na Kaduna, suka riƙa neman sa domin ya tsara waƙoƙi game da wasu manufofin gwamnati, idan sun kunno kai. Alalmisali, sauyin kuɗi da aka yi a shekarar 1973 Sa’in Makafin Zazzau ya yi waƙar ‘An mana Sabon Launi’ wadda ta yi matuƙar tasiri ga manufar da ake son cim ma ga al’umma. Haka kuma ya yi waƙa game da sauya tuƙi daga dama zuwa hagu, duk a waɗannan shekaru. Ta haka ne yakan sami abin masarufi daga hukumomin da suka ɗauki alhakin waƙokin.Wannan ya haifar da kyakkyawar dangantaka tsakanin Sa’in Makafin Zazzau da gwamnati, (Mujaheed, 2017).

Wajen shirya waƙoƙinsa, Salisu Sa’in Makafin Zazzau da yaransa, sukan zauna ne su tsara yadda amshinsu zai kasance, bayan tattaro bayanai game da abin da kayan cikin waƙokin za su ƙunsa, kafin su rera kowace waƙa. Daga nan ne, sai su rera a duk lokacin da ake buƙata. A wasu lokutan kuma, yakan ƙiri waƙa nan take idan buƙatar hakan ta taso. Dangane da waƙoƙinsa na farfaganda kuwa, gidajen rediyo su ne suke kasancewa mahaɗa tsakaninsa da gwamnati. Ta hanyar su ne yake samun bayanai game da abin da duk ake buƙatar ya waƙe, (Mujaheed, 2017).

Kafin rasuwarsa, ya yi waƙoƙi da dama, kuma ta hanyar waƙoƙin ne, yake samun duk abin masarufin da yake buƙata a rayuwarsa ta yau da kullum. Haka kuma ta hanyar waƙa ya sadu da jama’a daban-daban, wanda hakan ya sa ya sami shahara da ɗaukaka a duniya. Salisu Sa’in Makafin Zazzau ya rasu ne a watan 8, na shekarar 1988, (Mujaheed, 2017).

5.0 Salon Hira A Waƙoƙin Sa’in Makafin Zazzau

Salon hira ya ƙunshi muryar mai magana fiye da ɗaya, wato mawaƙi ya ƙadarta cewa da shi da wani ne ke magana, ko kuwa wasu masu magana biyu ko fiye ne ke wa juna magana. Salon hira yakan taimaka wa mawaƙi a ƙoƙarinsa na isar da saƙonsa ta hanyar sa mai saurare ko karatu ya zamo ya ƙara kusantar mawaƙi. Wato, sai mai saurare ya ji daga bakin waɗanda mawaƙi ke magana a kansu, ba wai daga bakin mawaƙin ba (Yahya 2001:109).

Shi kuwa Alamuna cewa ya yi salon hira a waƙa ya ƙunshi jin muryar mai magana fiye da ɗaya ne, wato mawaƙi mawaƙi ya ƙaddara das hi da wani suke magana, ko kuma wasu masu magana biyu ko fiye ne ke wa juna Magana. Ya ƙara da cewa irin wannan salo yana daga cikin salailan da mafiya yawan mawaƙan fina-finan Hausa ke amfani da shi cikin waƙoƙinsu kasancewar mafi yawa waƙoƙi ne na soyayya, inda a wurin aiwatar da waƙar mawaƙin kan ƙaddara cewa saurayi da budurwa ne ko mata da miji ke hira kan soyayyarsu.

Idan aka duba bayanan masana dangane da ko mene ne salon hira a taƙaice, za a iya cewa wata hanya ce ko dabara ta isar da saƙo a cikin waƙa ta yadda mawaƙi kan ayyana cewa suna tattaunawa ne da wani a wani mutum guda ɗaya ko wasu mutane da yawa a wani bigire ko yanayi, don haka maimakon ya kawo wa mai saurare labarin yadda hirar ta kasance a tsakaninsa da mutumin ko mutanen kawai kai tsaye, sai ya saƙo hirar da yadda ta kasance a waƙe, inda shi kuma mai saurare zai rinƙa jin hirar da kuma yadda take gudana a tsakanin mawaƙin da aboki ko abokan hirar tasa, yana tambaya suna amsa masa ko kuma ana tambayarsa yana amsawa. Watau dai shi irin wannan salo yana zuwa ne da tsari na tattaunawa a tsakanin mawaƙi ko fasihi da wani ko wasu mutane a cikin waƙa.

Yawanci makafi mutane ne da Allah yake halittarsu da hikima da azanci na musamman duk da kasancewar ba su gani, hakan ya sa suna da yawan son hira da kuma tattaunawa da mutane domin su ƙara samun wani sabon ilmi ko labari na wani abu ko wani wuri da ba su iya zuwa ba, don haka ba zai kasance wani abin mamaki ba a sami irin wannan salo a cikin waƙoƙin bara, waɗanda yawanci waƙoƙi ne da ake aiwata da su a cikin mutane domin neman abin masarufi. Don haka waƙoƙin Sa’in makafin Zazzau na cike da irin wannan salo. Misali :

A waƙarsa ta ‘Bayanin Wulli’, Sa’in Makafin Zazzau ya yi amfani da irin wannan salon yayin da ya je rumfar wani tela bara, inda a cikin waƙar ya kawo wa mai saurare abin da ya gudana a waƙe cikin hira. Ga yadda hirar tasu ta kaya:

 

                        Ya ce mini Malam Makaho

                           Wancan wane ne?

                                      Da dai na kaso kunnena

                        Sai na jiyo ƙarar walkinshi

                         Da na ce Wulli ne

                                     Kan a jima ai tela ya miƙe

                        Yana yi ta-kanka Makaho

                        Kadan ya zo ni ma zan tsere

 

                        Na tashi na ƙwaƙume tela

                         Sai yai ƙumaji

                        "Don ubaka sake ni Makaho"

                        "Ba za in sake ba tela"

                        Ya ce, a'a Makaho

                        Ni ma na ce a'a tela

                         Ta ya za kai min wannan?

                        Ka san ba za ka iya ba

                        Ta ya ka ce in shigo rumfarka?

                        Ya kai min zagi

                        'Yau ka ga Makahon banza'

                        Ya za ka riƙe ni

                        Kadan ya taho har ni zai kwaɗe

                        Na sau tela na tsinke

                      (Sa’in makafi Ba ni bayanin wulli)

 

Abin lura a nan shi ne, duk da cewa mawaƙin yana labarta yadda ta kaya tsakaninsa da Wulli ne a rumfar tela, sai ya yi amfani da salon hira, inda ya kawo yadda tattaunawar ta kasance tsakanin makaho da tela. Da farko ya nuna cewa tela yake tambayarsa ko wane ne yake tunkaro rumfar tasa? Duk da kasancewar Sa’in makafi mara gani, sai ya yi amfani da wata hikima wada aka san makafi da ita, ta wajen saurarawa su ji motsi ko ƙarar wani abu su iya tantance shi, wadda irin wanna hikimar ce ta ba shi dama har ya gene wanda ya tunkaro su ta hanyar jin motsin walkinsa. Bayan Makaho ya gaya wa tele cewa Wulli ne ya tunkaro rumfar sai fa tela ya nuna masa ya yi ta kansa, domin shi ma ba zai zauna ba, daga nan sai makaho ya ƙanƙame tela sai kuma taƙaddama ta kaure hard a zagi, amma duk da haka dai makaho bai saki tela ba. Duk waɗannan abubuwan da suka faru tsakanin tela da makaho da yadda suka yi ta ja-in-ja cikin zance, Sa’in makafi ya kawo shi ne a waƙe, wanda hakan ne zai ba mai saurare dama ya ji wa kunnuwansa yadda hirar ta kaya tsakanin makaho da tela.

A cikin waƙar ‘Idi Wanzami’ ma, Sa’in Makafin Zazzau ya yawaita amfani da irin wannan salon cikin zantawarsa da mutanen garin Gagawa da kuma Wanzamin da ke masa aski. Misali wurin da ya ce:

Na ce; “Idi Wanzami,

Ka sayi turmin alawayyo,

Ko an yi rashi a gidanka?”

Sai ya ce mani a’a.

Na ce; “Idi Wanzami,

Na Tashar Gagawa,

Ga ƙato saba’in a gabanka,

Ga ƙatti saba’in a gabanka,

‘Yan gayyar noma ne,

Ko kuwa ‘yan ɗaurin aure ne?”

Sai ya ce mani a’a.

 

Na ce; “Idi Wanzami,

Na Tashar Gagawa,

Subhanallahi!

Na ji ka kira limami,

Wai aure zai ɗaura,

Ko kuma zai huɗubar suna ne?

Ko ko zai yi ma hujja’u?”

Sai ya ce mani a’a.

 

Ya ce; “kai tsaya makaho,

Tambayarka ta fa ishe ni,’

Bari dai za na ba ka amsa,

Ka ga hatsin da na bayar,

Hatsin gumbar sadaka ne,

Turmin alawayyo,

Wannan turmin likkafani ne,

Ƙato saba’in kuma,

Wannan ‘yan ɗaukar gawa ne,

Shi ko limami,

Shi ne zai maka sallah.”

 

Wannan misali ne na salon hira, wanda yake nuna irin tattaunawar da ta wanzu tsakanin makaho da kuma Idi wanzami, wadda duk wannan hirar ta kasance ne a tsakaninsu kafin a fara yi wa makaho aski. Mawaƙin ya kwararo wa mai saurare ne yadda hirara ta kasance, inda ya fara da kawo tambayar da ya yi wa wanzamin lokacin da ya gan shi da turmin alawayyo, ko shin an yi rashi ne a gidansa, amma sai wanzami ya amsa masa da cewa a’a. Daga nan kuma sai ya tambaye shi su kuma waɗannan ƙartin har mutane saba’in me za su yi? Shin noma za su yi masa? Ko ɗaurin aure za su je? A nan ma sai wanzami ya amsa wa makaho da babu ko ɗaya. Makaho bai haƙura ba sai kuma ya sake tambayar wanzami cewa ya ji yana kiran Limami ne, shin aure zai ɗaura ko kuma huɗubar suna zai yi, ko kuma wata tambayr wanzami zai yi masa? A nan ma sai wanzami ya amsa masa da babu ko ɗaya. Daga ƙarshe dai wanzami ya yi fushi ya nuna cewa tambayoyin fad a makaho yake yi masa sun fara yi masa yawa, don haka sai ya amsa masa da cewa, ya fa sani hatsin day a aika da shi na sadaka ne za a yi, sannan turmin alawayyo likkafani za a yi masa da shi, su kuma waɗannan ƙarti guda saba’in su ne za su ɗauki gawar makahon, a yayin das hi kuma Liman shi ne zai yi masa sallah. Idan aka duba za fahimci cewa Sa’in makafi ya zaɓi ya yi amfani da wannan salo ne na hira domin ya kawo wa mai saurare irin bahallatsar da ta faru tsakaninsa da Idi wanzami, wanda ya je rumfarsa domin ya yi masa aski, amma sai ya ga wasu baƙin abubuwa da wanzamin ken aiwatarwa don haka bai yi ƙasa a gwiwa ba ya fara tambaya shi kuma wanzamin na amsa masa. Wanda yin hakan ne ya ba mai saurare damar jin tattaunawar da ta gudana tsakanin wanzamin da kuma makaho.

A cikin waƙar ‘Direba Makaho’, a nan  ma Sa’in Makafi ya yi amfani da wannan salo na hira, inda ya ba mai saurare dama ya saurari hirar da ta wakana tsakaninsa da masu mota. Misali inda y ace:

Da zuwana Legas,

            Da ni da abokan aiki,

Yaya muka ƙare?

Sai na je wajen Hausawa,

Na ce; “Salamu alaikum,

Hausawan Legas,

Ga baƙo na makaho,

Amma fa ina da jawabi,

Ni ina da jawabi,

So nake na kama sana’a,

Ni fa barar nan ta dame ni.”

 

Sai suka ce; “To malam,

Yanzu nan wane aiki za kai?”

Subhanallahi!

(Sa’in Makafi: Direba Makaho)

 

Idan aka duba wannan ɗan waƙar, Sa’in Makafi ya kawo wa mai saurare hirar da ta gudana ne a tsakanisa da wasu Hausawa a garin Legas a lokacin da ya tafi neman sana’a kasancewar ya gaji da bara . Sa’in Makafi ya kawo hirar ne ta hanyar nuna yadda ya je ya samu waɗannan Hausawa suna zaune a wurin kasuwancinsu, amma bai faɗa musu kai tsaye ba sai day a yi musu sallama, wadda it ace al’adar duk wani baƙo na kirki kamar yadda Hausawa suka tabbatar cewa “baƙo babu sallama mugu ne”. Bayan makaho ya yi sallama ne sai kuma ya gaya wa mutanen dalilin zuwansa garesu, wato ya zo ne domin ya bayyana musu cewa shi fa barar da yake yi ta dame sa kuma bai ɗauke ta a matsayin sana’a ba, don haka ya yanke hukuncin zai fara wata sana’a. bayan Hausawn Legas sun saurari jawabin makaho sai kuma suka amsa masa ta hanyar tambayarsa da cewa to shi a nasa tunanin wane irin aiki zai yi a matsayin sana’a kasancewarsa makaho? Duk wannan tattaunawar da ta gudana tsakanin makaho da Hausawan Legas Sa’in makafi ya kawo ta ne a waƙe ta yadda mai saurare zai ji yadda hirar ke gudana tsakanin mutanen da kunnuwansa, wanda dalilin sarrafa salon hira ne a cikin waƙar.

Haka dai mawaƙin ya ci gaba da sarrafa irin wannan salo na hira a cikin waƙar tasa ta ‘direba Makaho’ domin ganin ya kawo wa mai saurare irin irin yadda hirar tasu ta ƙare da waɗannan mutane da ya samu da nufin su samar masa da aikin da zai rinƙa yi domin neman na abinci a maimakon bara da yake yi. Inda ya ce:

Na ce; “Hausawan Legas,

Ku saya mani moto,

Mu je mu cika ta da lodi,

Mu je mu ɗau fasinja,

Karen motanmu makaho,

Ɗan kamashonmu makaho,

Kwandastan namu makaho,

Akawun namu makaho,

Duk babu mai ido a cikinmu.”

 

Sai suka ce; “ kai malam,”

Daga nan babbansu ya miƙe,

Ya ce; “Kai tsaya makaho,

Ka san mu nan,

Ka san mu Hausawa ne,

A cikin nan namu,

Wa zai yarda ya ɗauki asara?

A saya maka mota,

In ka saka ta a rami,

Ai a yi ba uwa ba riba,

Na ce; “Allah zai kare,”

Sai suka ce; “Kai malam,

Mu mun yarda da Allah,

Amma wajenmu ba mu da mota.”

 

A nan Sa’in Makafi ya ci gaba da kawo wa mai saurare yadda tattaunawarsu da Hausawan Legas ta wakana ne ta hanyar sarrafa salon hira, inda ya jiyar da shi yadda yake roƙon Hausawan da su saya masa mota domin ya zaɓi tuƙi ne a matsayin sana’ar da za ta maye gurbin barar da yake yi. Ya gaya masu cewa shi ne dai zai tuƙa motar a matsayin direba duk da kasancewarsa makaho, haka kuma da yaron motar da ɗan kamashon da zai yi musu lodi da akawun motar duk makafi ne. Bayan Hausawan Legas sun saurari jawabin makaho sai suka amsa masa ta bakin babbansu wanda ya bayyana masa cewa, su fa Hausawa ne, don haka babu wani wanda zai iya yin wannan kasadar a cikinsu domin gudun asarar da za ta faɗa masa yana ji yana gani ya ɗauki kuɗi ya sayi mota sannan  ya hannantata ga makaho, wanda a ƙarshe tana iya yin haɗari. Duk da jawabin waɗannan mutane makaho bai haƙura ba sai ya ci gaba da ƙoƙarin lallashinsu ta hanyar nuna masu ƙaddara da Allah, tare da ƙarfafa musu gwiwa cewa Allah zai iya kare su tare da motar, sai dai a ƙarshe dai haƙarsa ba ta cim ma ruwa ba, domin haka suka gaya masa cewa sun fa yarda da Allah da kuma ƙaddara, amma duk da haka ba su da motar da za sub a shi ya tuƙa. Mawaƙin ya sarrafa wanna salo ne na hira saboda mai saurare ya ji irin yadda tattaunawar ta gudana tsakanin makaho da Hausawan Legas a waƙe. 

6.0 Kammalawa

Muhimmancin salo a waƙa ba ya misaltuwa, saboda salon ne ke kwarzanta mawaƙin da waƙar, kuma shi ne yake rayar da harshe, ya kuma kaifafa tunanin mai ji ko mai sauraro kuma ya sarrafa shi tare da bayyana shi cikin irin fahimtar da ake buƙata. A wannan aikin, an nazarci salon hira ne a waƙoƙin Salisu Sa’in Makafin Zazzau, waɗanda galibinsu waƙoƙin bara ne. Saboda haka, an kawo bayani kan salo da waƙoƙin bara da kuma taƙaitaccen Tarihin mawaƙin. Daga ƙarshe aka fayyace fasalin salon hira a waƙoƙinsa. An gano cewa salon hira yana kan gaba cikin salon da mawaƙin yake amfanin da shi wajen gabatar da waƙoƙinsa. 

7.0 Manazarta

Tuntuɓi masu takarda.

Post a Comment

0 Comments