Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazari Kan Yadda Yaro Ke Tashi Da Koyon Harshen Farko

Wannan takarda ta ƙunshi bayani game da “koyon harshe” da “tashi da harshe.”

Tashi da Harshe

Nazari Kan Yadda Yaro Ke Tashi Da Koyon Harshen Farko

Idris Abubakar

Sharar Fage

          A cikin wannan bincike na nazari kan yadda yaro ke tashi da koyon harshen farko, an yi ƙoƙarin kawo abubuwa kamar haka:

Ø Ma’anar harshe

Ø Hasashe game da asalin samuwar harshe

Ø Yadda yaro ke tashi da koyon harshe

Ø Baiwa na magana

Ø Baiwa na fahimta

Ø Haɓakar harshe da kuma yaɗuwarsa

Ø Ire-ire yaɗuwar harshe

Ø Hanyoyin yaɗuwar harshe

Dalilin Bincike

          Ɗalibai da dama sun yi ta yin rubuce-rubuce a wannan ɓangare na nazarin kimiyyar harshe. Amma kashi 80% cikin ɗari sukan yi rubuce-rubucen su ne a ɗaya daga cikin rassa na kimiyyar harshe. Na ga yana da kyau in gwada samo wani abu dangane da yadda ake fara koyo ko tashi da harshe ba a aji ko wani wurin karatu ba.

          Kasancewar duk wani aiki da ɗan Adam ya ƙudiri aniyar aiwatar da shi akwai dalili. To wannan binciken ina so in gano yaya ake yi yaro yake fara magana. Ma’ana waɗanne matakai ake bi kafin yaro ya yi magana.

Ma’anar Harshe da Matsayinsa

          Idan aka ce harshe, ana nufin magana ke nan wadda ake ji a fahimta. Harshe shi ne abin da ya bambanta ɗan Adam da sauran dabbobi. Harshe a wurin ɗan Adam, linzami ne na tunani, sauran dabbobi kuwa sai dai su yi kuka, ko gurnani ko haushi ko haniniya, don su nuna fushin su, ko murnan su, ko wuyarsu ko daɗinsu. Hatta aku wadda ke kwaikwayon ɗan Adam, yana yi ne ba tare da tunani ba.

          Amma harshe a yadda kowa ya san shi, shi ne wani tsoka ne a cikin bakin ɗan Adam wanda yake taimaka wa mutum wajen yin magana da shan ruwa da tauna abinci. Sai dai a fannin ilimin kimiyyar harsuna, harshe yana nufin sadar da manufa a tsakanin al’umma ta wajen yin furuci wanda ake dangantawa da ma’ana, al’umma ko ƙabila shi ne hanyar hulɗa ta wajen magana.

          Mutum kaɗai ke gwada fasaharsa da nishaɗinsa ta hanyar harshe. Yakan yi waƙa ko wani azanci kamar karin magana ko habaici ko wanin waɗannan. Ba don harshe ba, da ko sunan mutum ba zai samu ba, balle har ya samawa abubuwan da ke kewaye da shi suna. Harshe baiwa ce da ɗaukaka wanda Allah ya ba ɗan Adam. Da ita mutum yake sadarwa da mu’amala. Harshe shi ne maƙunshin ilimi da tarbiyya, ra’ayin al’umma da hikimominsu, da tarihinsu da abubuwan san su da ƙin su, da harshe ake faɗarsu da adana su har a bar wa na baya abin gado.

          A fannin ilimin kimiyyar harsuna kuma ake yin nazari a kan shi ne riƙe kimiyya wato (linguistics) da ingilishi fannin kimiyyar harsuna fannin ilimi ne mai faɗin gaske wanda ya tara abubuwa da dama kamar haka:

Ø Fannin asalin harshe

Ø Fannin sigar harshe

Ø Fannin koyon harshe

Ø Fannin haɗuwar harshe d.s.

Haka kuma kowanne matakai a cikin waɗannan yana da nasa ɓangarorin. Asali idan ka ɗauki fanni da yake magana a kan jigogin harshe akwai abubuwa kamar haka:

i.                   Ɓangaren nazarin sauti

ii.                 Ɓangaren da yake nazari  a kan sarrafa furuci

iii.              Ɓangaren nazarin ginin kalmomi

iv.               Ɓangaren nazarin ma’ana

Asalin Samuwar Harshe

          Ɗan Adam ya daɗe yana mamakin irin daman da Allah ya ba shi na iya yin magana, wadda a sanin mu ɗan Adam ne kaɗai ke da wannan baiwar. Amma masana kimiyyar harsuna da dama a duniya sukan yi muhawara a kan shin mene ne asalin harshe? Ko da yake an sami ra’ayoyi da dama dangane da abin da ya shafi asalin samuwar harshe kamar haka:

1)    Akwai masu ra’ayin cewa dukkanin harshe na duniya tushensa ɗaya ne, haka kuma lallai ɗan Adam na tare da harshen sa na asali. Wato Allah ya halacci ɗan Adam ne tare da harshen da yake magana da shi.

2)    Ra’ayi na biyu sun nuna cewa ɗan Adam shi ne ya ƙirƙiro harshensa da kansa bisa waɗannan dalilai:

Ø Mutum ya fara iya magana ne lokacin da wani mai basira ya zauna ya ba wa komai na duniya suna.

Ø Mutum ya fara magana lokacin da ya fara jin zafi, mamaki ko kuma murna.

Ø Har yanzu masu wannan ra’ayin suna ganin mutum ya fara yin magana ne lokacin da ya nemi kwaikwayo ƙwayoyin sautuka na wasu dabbobi. Wato a nan na nufin irin ƙararrakin da suke yi.

3)    Ra’ayi na uku in da suka ce asalin samuwar harshe ya faru ne a lokacin da kamannin ɗan Adam suka canza ko kuma suka sauya daga na kusa da biri. Wato lokacin ne ƙwaƙwalwarsa ta girma sosai har ta sami sarrafa gaɓoɓin magana domin yin furuci.

4)    Ra’ayi na huɗu: Ra’ayin Husumiyar Babila wannan ƙaulin cewa ya yi dukkan harsuna guda ne, wato jikokin Annabi Nuhu ne saboda sun gaji duniyar nan ne bayan ruwan ɗufana daga nan suka yaƙi La’abila-ƙabila a lokacin harshe ɗaya ne suke amfani da shi, daga baya wasu su ka yi tunanin gina gari mai suna Babila bayan sun gina wata husumiyar da za ta kai su sama. Da wannan husumiyar ya yi tsayi sai ta rushe duk mutanen da suka faɗo, sai waɗanda suke cikin gari bakinsu ya juye sai kowa ya fara harsuna daban-daban.

Don haka za mu iya cewa dangane da waɗannan ra’ayoyi da suka gabata, harshe dai kamar yadda Allah ya halicci zanzara da ilimin iya gini, sannan ya ba wa kuɗan zuma furanni, ta hakan ya bai wa ɗan Adam harshe. Dalili kuwa duk inda mutum ya girma sai ka ga ya tashi da harshen garin/wurin. Saboda haka za a iya cewa Allah ya ajiye harsuna ne daban-daban na duniya.

Tashi Da Koyon Harshe

          Harshen da mutum ya buɗe ido a cikinsa, shi ake kira harshe na ɗaya (L1) walau na iyayensa ko kuma na al’umma da ya tashi a cikinta. Idan kuma harshen iyayensa ne shi ake kira harshen uwa (mother tongue). Duk da cewa an san yadda harshe yake da tsari da kuma ‘yan saƙe-saƙe ƙa’idoji, haka an san irin gwaninta da kuma ban mamaki wadda yaro ƙarami kan yi wajen ƙoƙarin gwada harshensa na uwa.

          Haka kuma an lura cewa komai girman mutum da hazaƙarsa, in ya tashi koyon harshe, in dai ba nasa ba ne yakan sha wahala wajen koyo kuma zai yi wuya ya naƙalci harshen daidai, ba kamar waɗanda suka buɗe ido a cikinsa ba, musamman ta fuskar lafazi. A taƙaice Allah ya yi wa ɗan Adam baiwa iri biyu waɗanda suke taimakonsa wajen koyon harshe da zarar ya faɗo duniya su ne kamar haka:

1)    Baiwa na magana

2)    Baiwa na fahimta

Baiwar Magana

          Tana bayyana ne ga ɗan Adam tun daga lokacin da ya faɗo duniya a lokacin ne yake ƙoƙarin koyon furuci da tara kalmomi da kuma naƙaltar nahawu kafin yaro ya yi baki, sannan ya iya faɗan duk abin da ya ga dama. Yakan bi matakai har guda huɗu kafin ya yi magana da kyau kamar haka:

Ø Kuka da dariya

Ø Yin gulatu

Ø Karayar baki

Ø Yin zance raɗau

Ga matakan da akan bi kafin yaro ya koyi harshe:

1)    Daga wata uku => Yaro zai fara yin ƙara iri-iri da kuma yawan kuka.

2)    Daga wata tara => Yaro zai iya haɗa ƙwayoyin kalma iri ɗaya, sannan za a iya shaida sunayen wasu in ya haɗa.

3)    Daga wata sha biyu => An san shi da yawan maimaita wasu saututtuka da kuma yin gwalan-gwalantu. Sannan akan shaida wasu kalmomi.

4)    Daga wata sha takwas => Yaro zai iya faɗan kalmomi da yawa daga harshensa. Daga nan kuma aywancin yin gulatu zai fara gushewa, sannan zai fara haɗa ‘yar jimla.

5)    Daga shekara biyu => Za a ga cewa yaro babu gulatu ko ɗaya a bakinsa saboda yana iya amfani da harshen sosai sai dai akwai karayan baki kaɗan.

6)    Daga shekara uku => Yaro yakan san kalmomi masu yawa, kuma ya naƙalci tasarifi mai yawa kamar su bambance jinsi da adadi. Tare da lokutan Hausa.

7)    Daga shekara huɗu => Idan yaro ya kai waɗannan shekaru kusan babu abin da baya iya faɗa kuma babu karayar baki tattare da shi.

8)    Daga shekara biyar => Yaro yakan samu kaifin tunani a cikin harshe, sannan kuma Allah yakan ba shi damar sanin kalmomi sama da 500.

9)    Daga shekara 6-8 => Yaro yana iya amfani da harshensa sosai sannan kuma ya san kalmomi fiye da dubu (1000).

Baiwa Na Fahimta

          Mutum daman an haife shi da baiwar fahimta. Saboda haka makonni ‘yan ƙalilan da zuwansa duniya yake fara shaida muryan ‘yar Adam. Sai kuma ya fara rarrabewa tsakanin maganar so da na ƙi. Ga irin matakan dake faruwa dangane da baiwar fahimta:

1)    Daga wata tara => Yaro yana gane motsi da hannu na ya zo ko kuma ya tafi.

2)    Daga wata sha biyu => Yaro yana fahimtar umarni mai sauƙi m.s. tashi, kul, bari, d.s.

3)    Daga wata sha takwas => A wannan lokaci ne yaro yakan ƙirƙiri nahawunsa wajen kiran baba, mama, d.s.

4)    Daga shekara biyu => Yaro yakan fahimci umarni musamman na irin halin da yake ciki dangane da abun da ya shafi fitsari, kashi, d.s.

5)    Daga shekara uku => A wannan lokaci ne yaro yakan gane tambaya dangane da irin abin da ya shuɗe.

6)    Daga shekara huɗu => Yaro yakan fahimci abubuwa da dama musamman abu mai daɗi da marar daɗi. Sannan kuma ya hargutsa lokuta, m.s. jiya, gobe, d.s.

7)    Daga shekara biyar => Yaro yakan gane abubuwa da dama har waɗanda ba su shafi yara ba.

8)    Daga shekara shida zuwa takwas (6-8) => A wannan lokaci ne idanunsa na zahiri da kuma na zuci duk suna buɗe, saboda haka ne ma akan sa yara makaranta a daidai wannan lokacin.

Don haka waɗannan halaye guda biyu, wato baiwa ta magana da kuma baiwa ta fahimta za a ga duk waɗannan abubuwa na iya faruwa a cikin sauƙi kafin lokacin da aka zayyana.

Yaɗuwar Harshe

          Yaɗuwar harshe ita ce ƙaruwar yawan masu magana da harshe, waɗanda tun farko su ba asalin ‘yan harshen ba ne. akwai yaɗuwar harshe iri biyu kamar haka:

Ø Yaɗuwar harshe a cikin gida

Ø Yaɗuwar harshe a waje

Amma dangane da wannan yaɗuwa na harshe ba haka kawai ake samun wannan ƙaruwa ba sai ta waɗannan hanyoyi kamar haka:

Ø Kasuwanci

Ø Ƙaurace-ƙaurace

Ø Auratayya

Ø Hulɗa da juna/mu’amala

Ø Kafofin sadarwa

Kammalawa

          A wannan bincike da ake gabatarwa an yi ƙoƙari wajen bayyana mene ne harshe da kuma asalin samuwar harshen bisa ra’ayoyi daban-daban. Sannan wannan bincike ya fito da wasu matakai da yaro yake bi kafin ya tashi da harshe ko ya koyi harshe, inda muka yi bayanin abubuwa guda biyu; Baiwa na magana da baiwa na fahimta. Sannan muka yi bayanin yaɗuwar harshe gami da hanyoyin da ake bi harshe ya yaɗu. A taƙaice wannan shi ne abin da wannan takarda ko bincike yake ɗauke da shi.

 

Madogara

Tuntuɓi masu gudanarwa.

Post a Comment

0 Comments