Ticker

6/recent/ticker-posts

Suturar Mata A Bukukuwan Sallah: Hannun Agogo Ya Koma Baya

A yayin da kullum ilimi ke ƙara yawaita, abin da ake tsammani shi ne al'umma su siffantu da halaye da ɗabi'u na gari da suka dace da koyarwar addini. Anya kuwa ci gaba da ake samu bai kasance na mai tonon rijiya ba?

Imrana Hamza Tsugugi

Abaya

Ranar Sallah wuni ne na musamman da Shari'a ta ware domin musulmi su yi nishaɗi da walwala bayan kammala wasu muhimman Ibadu, wato azumi da aikin Hajji.

An amince wa dukkan Musulmi ɗebe kewa irin wadda addinin ya yi wa ƙaidi. 

Daga cikin nau'ukan sakewa da aka yarda a yi a wannan rana, akwai sanya sabbin tufafi da cin abinci da shan abin sha na halal. Kowane jinsi ana tanadar musu irin suturar da ya kamata su sa, dai dai da yadda al'adarsu take. Suturar mata Hausawa ta ƙunshi riga da zani da kallabi da kuma mayafi. Irin wannan shiga tana nuna cikar kamala da sanin mutuncin kai. A lokacin bukukuwa na aure ko haihuwa ko salla, akan ga mata da irin wannan sutura.

Juyin zamani ya yi wa suturar matan Hausawa ɗiban-karan-mahaukaciya, matan aure da 'yan mata sun ari kayan ado na maƙwabtan ƙabilu na gida da na waje. sai dai galibin waɗannan suturun babu mutunta kai a cikinsu. 

Abin da na lura da shi a wannan sallar shi ne kashi 85 cikin ɗari na mata suna sanye ne da suturar Allah-wadai. Adon da suke yi ya wuce minsharri, salon ɗinkin ba shi da maraba da ƙirar jikinsu, ƙarin gashi kamar 'ya'yan Yahudu, adon fuska tamkar birai a daji, abin dai babu kyan gani.

A 'yan shekarun da na yi ina nazarin salon shigar mata da samari a lokutan salla, ban taɓa ganin mafi muni irin na bana ba. Suturar da mata suka sanya tana fito da dukkan wata ƙiira ta jikinsu, yadda duk wani namiji da ya amsa sunansa sai hankalinsa ya ɗauku, gyalen ma na al'ada a kafaɗa ko wuya ake maƙale shi, ga gashin doki an zubo shi har gadon baya, ana tafiya ana yauƙi ana tauna cingam yana ƙaras, ƙararas, ana burtso shi wajen baki. An yi ƙunshin lallen Sudan tun daga hannu har ƙafa, wasu an zizara musu shi a wuya da ƙeya zuwa gadon baya, ta yadda dai ko ba ka so sai ka kalla.

Ga idanunsu ƙyar a kan maza, ba ko ƙiftawa, suna karya harshe suna rangwaɗa.

A gefe ɗaya kuma ga samari masu budurwar sha'awa, suna jiransu a gefen katanga da surƙuƙun lungu. Ƙazantar dai ta ɓaci.

Lalle ya kamata iyaye su tsaya su yi karatun-ta-natsu, su tuna cewa Allah zai tambaye su game da kiwon 'ya'yan da ya ba su, duk shigar da 'ya ta yi wadda ta haifar da fasadi, suna da nasu kamashon, wajibi ne su hana 'ya'yansu irin wannan muguwar bamagujiyar shigar.

Malamai su ma suna da rawar da za su taka wajen daƙile wannan mummunar ta'adar.

Muna roƙon Allah ya shirya zuri'armu ya ɗora mu a kan dai dai.

Amin summa Amin.

Post a Comment

0 Comments