Ticker

6/recent/ticker-posts

Gayyata! Gayyata!! Gayyata!!!

Farfesa Salisu Ahmad Yakasai da Abu-Ubaida Sani suna farin cikin gayyatar ku zuwa wurin ƙaddamar da littafinsu mai taken “Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA).

Rana: Asabar, 22/05/2021
Lokaci: 10:30 Na Safe
Wuri: Babban Ɗakin Taro (Convocation Hall), Jami’ar Bayero, Kano

Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Salisu Ahmad YAKASAI
Department of Nigerian Languages
Usmanu Danfodiyo University, Sokoto
Phone: 08035073537
Mail: syakasai@gmail.com

DA

Abu-UbaidaSANI
Department of Languages and Cultures
Federal University Gusau, Zamfara
Phone No. (+234) 08133529736
Email: abuubaidasani5@gmail.com
Site: abu-ubaida.com

Dangane da Diwanin Waƙoƙin Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Martaba da ƙimar mutum su ne suke bayyana wane ne shi a cikin al’umma. Martaba ita ke ƙunshe wasu sifofi da suka danganci halayya da tunani da ƙawazuci da zamantakewa a rayuwar mutum. Hasali ma, batun ƙima da martabar mutum sun wuce yadda ake ganin su a zahiri. Wato siffofin da suke tattare a cikin ƙima da martaba, su ne suke kammala cikar mutum.

Na farko daga cikin waɗannan siffofi shi ne sauƙin kai. Mutumin da ya zama mai sauƙin kai, ba shi da wuyar mu’amala da sauran jama’a. Sai dai kuma sau nawa ka taɓa cin karo da irin wannan mutum? Mutum ne mai ƙana’a da sanin yakamata. Hasali ma, shi mutum ne wanda ba shi da saurin fushi ko kasala, kuma murmushi ko fara’arsa na inganta yanayi cikin hulɗa.

Irin wannan mutum yana bayar da goyon baya tare da ƙarfafa guiwa a rayuwar al’umma. A kowane lokaci ƙofofinsa a buɗe suke, wato a shirye yake domin sauraron jama’a da kuma ba su shawara ta gari, kuma duk inda ya je ba ya ɓuya. Saboda haka ya kasance aboki ta yadda mutane za su tunkare shi domin ba da shawara dangane da al’amuransu na rayuwa, musamman ma da yake ba batu ba ne na kuɗi, face kyawun hali.

Shin ko halayenmu suna taimakawa wajen yin mu’amala da zuciya ɗaya, kuma ko hakan na sa a sami sakamako cikin al’amuran yau da kullum na abokan hulɗa? Ba shakka duk wanda ya tafiyar da rayuwarsa a cikin sauƙi, to za a ga yadda jama’a suke kewaye shi cikin aminci da riƙon amana.

Wata siffar kuma ita ce ta ƙarfin hali. A nan ƙarfin hali da muke magana shi ne na ɗa’a da ladabi da biyayya. A zubi da tsarin rayuwa, babu abin da ya dace kuma muke buƙata face ƙarfin hali domin faɗin gaskiya. Muna kuma buƙatar ƙarfin hali musamman a lokacin da muka sami kanmu cikin yanayi na yin zaɓi tsakanin abu mai kyau da kuma marar kyau, a lokacin da babu mai kallon mu.

Muna buƙatar ƙarfin hali domin kasancewa masu gaskiya da adalci cikin mu’amala da sauran jama’a. da zarar al’umma ta samu mutum mai ƙarfin hali a matsayin jagora to rayuwar wannan al’umma za ta kasance cikin dacewa. Irin wannan ƙarfin hali shi ne ƙololuwar zama namiji. Akwai kuma ladabi da biyayya cikin aiki ko wajabci. Muna iya tantancewa tsakanin mutum mai ƙwazo da kuma biyayya. A yayin da imani yake miƙa wuya ga aiki ko umurni, ƙwazo kuwa himmatuwa ce ga abin da aka sa a gaba.

Su waɗannan siffofi guda uku, idan suka samu a lokaci guda, to ba shakka an yi tanadin abin ƙwarai ga mutum. Waɗannan abubuwa su ne jagora wajen tafiyar da rayuwa. Wato ƙwazo da miƙa wuya su ne sirrin gina kai, kuma cikin ƙwazo ne ake gina mutum. Akwai kuma tausayi. Da yawa mukan sami kanmu cikin so da ƙaunar mutane masu tausayawa. Babu wata hanya ta samun jin daɗi tamkar nuna halin tausayawa. Wato farin ciki yana samuwa nan take amma ba ya ɗorewa. Jin daɗi ko wani abu ne da ke cikin zuciya. Da yawa manzon rahama yakan hore mu da mu bayar maimakon karɓa, musamman ma da yake hannun bayarwa ya fi hannun karɓa. Ba shakka duniya na alfahari da masu tausayi, domin ba a samun nasara sai a cikin tausayawa. Hasali ma ai masu tausayawar nan su ne masu arziƙi a duniya da lahira, kuma da yake sun shayar da al’umma baiwa ta tausayawa, to zukatansu na cike da annuri.

Gaskiya ne cewa fuska ita ce riga, wato ana buƙatar cikakkiyar shiga ta kamala a kowane lokaci. Da ma dai son tufafi cikin ado ba sabon abu ba ne ga tsarin mawaƙa. Hasali ma, ai ma’abuta amfani da tufafi na ƙwarai kan ce jikin da aka kyautata shi yakan tafi tare da halayya, sannan daga baya a samu tasiri ga mutum gaba ɗaya. Wato mutumin da ya sanya tufafi masu kyau yana ɗauke da ƙima cikin daraja ta musamman. Da haka irin waɗannan mutane kan ƙara wa kansu himma da ƙwazo na aiki da armashi, kuma a daɗe ana tunawa da su a cikin al’umma saboda irin ayyukan alherin da aka san su da su.

A insaniya irin ta ɗan adam, abin da ya gabata yanayi ne da ya dace da Aminu Ladan Abubakar (ALAN Waƙa): Wato shahararren mawaƙin da muke gabatar da tarihin rayuwarsa da waƙoƙinsa a cikin wannan littafi mai suna DIWANIN WAƘOƘIN AMINU LADAN ABUBAKAR (ALAN WAƘA). Domin samun cikakken bayanin rayuwa da waƙoƙin ALA, mun kasa littafin zuwa babi-babi har guda goma sha uku (13).

Bayan gabatarwa, a babi na farko an yi bayanin haihuwar Alan waƙa, wato mahaifa da kakanni da ‘yan uwa. Akwai kuma batun aure da iyalansa da iliminsa (karatunsa) da kuma uwa-uba gwagwarmayar rayuwa. Babi na biyu kuma bayani ne a kan matsayin Alan waƙa a duniyar waƙa. Wato lokaci da dalilin fara waƙa da batun uban gida da muradi da fargaba da wasiya da kuma ɗaukakar ALA a duniyar waƙa.

Daga nan kuma sai batun jigogin waƙoƙin Aminu ALA, wato da yake jigogin na da yawa, babi na uku yana ɗauke ne da waƙoƙi na faɗakarwa. A babi na huɗu kuma, mun kawo waƙoƙin Aminu Alan Abubakar (ALAN Waƙa) ne masu jigon siyasa.

Babi na biyar kuwa shi ne ya tattaro waƙoƙin ALAN waƙa, masu jigon soyayya. A nan ɗin ma dai maƙasudin samar da waɗannan waƙoƙi shi ne so da ƙauna duka a cikin soyayya. Daga nan kuma sai batun shugabanci (ko jagoranci), wato tsari na sarauta, wadda idan ta tunkaro to dole a kauce. Babi na shida ne yake ɗauke da waƙoƙin ALA masu jigon sarauta. A babi na bakwai kuma, waƙoƙin ALA ne masu jigon yabo da kuma jinjina.

Sai kuma babi na takwas, inda a nan mun kawo waƙoƙin Aminu ALA ne masu jigo na ganin dama. Wani jigo kuma da yake da alaƙa da na waƙoƙin ganin dama shi ne na waƙoƙi masu jigon talla, a babi na tara. Daga nan kuma sai babi na goma, wanda yake ɗauke da waƙoƙi masu jigon zagin kasuwa. A nan ne msu hikimar magana suke cewa koya ya yi zagi a kasuwa ya san da wanda yake.

A babi na sha ɗaya, mun kawo waƙoƙin ALA ne masu jigon aure, wato batun nan na farko cikin matakan rayuwa. Daga nan kuma sai babi na sha biyu, wato na waƙoƙi masu jigon ta’aziya. A babi na sha uku kuma, waƙoƙin Aminu ALA ne masu jigon ɗaukaka. A nan ne muka bijoro da waƙoƙin tarihi da rukunin gwagwarmaya da na shahara da na ƙalubale da kuma uwa-uba na rukunin nasara.

Post a Comment

0 Comments