Ticker

6/recent/ticker-posts

Mu Koyi Ka'idojin Rubutu (Kashi na 4)

Daga taskar shugaban marubuta da manazarta rubutacciyar waƙa ta ƙasa (Mai Bazazzagiya).

Mu Koyi Ƙa'idojin Rubutu (Kashi na 4)
Sulaiman Salisu Muhammad
Sashen Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe,
Jami'ar Jihar Kaduna.
Email: sulaimasalisumuhammad@gmail.com
Phone: 08067917740

ka'idojin rubutu

Fadakarwa: Darasin da ya gabaci wannan, na 3 ne ba na 2 ba.

Yadda za a yi amfani da wakilin suna da dirka a rubutu:

Akwai wakilan sunaye a harshen Hausa kamar haka:

Ni

Kai

Shi

Ke

Ita

Mu

Ku

Su

Akwai dirka iri biyu:

Ne, mai yin ishara ga namiji

Ce,  mai yin ishara ga mace

A duk lokacin da wakilin suna da dirka suka zo a tare, kowanne gashin kansa yake ci. Ba a hade ake rubuta su ba. Misali:

Ni ne      ba    Nine      ba

Kai ne    ba    Kaine    ba

Shi ne    ba    Shine    ba

Ke ce     ba    Kece     ba

Ita ce     ba    itace     ba

Mu ne   ba    Mune    ba

Ku ne    ba    Kune     ba

Su ne    ba    Sune     ba

A yanzu ka dauki biro da takarda ka rubuta kowanne sau goma. Ta haka ne za ka saba da rubuta su babu kuskure.

Sulaiman Mai Bazazzagiya

Post a Comment

0 Comments