Mu Koyi Ka'idojin Rubutu (Kashi na 1)

    Daga taskar shugaban marubuta da manazarta rubutacciyar waƙa ta ƙasa (Mai Bazazzagiya).

    Mu Koyi Ƙa'idojin Rubutu (Kashi na 1)

    Sulaiman Salisu Muhammad
    Sashen Harsunan Nijeriya da Kimiyyar Harshe,
    Jami'ar Jihar Kaduna.
    Email: sulaimasalisumuhammad@gmail.com
    Phone: 08067917740

    Ƙa'idojin rubutu

    Gabatarwa

    Wato na lura a cikin wannan Tsangaya tamu, kowa ya iya rubutun Hausa, amma ba kowa ya san ka'idojin rubutunta ba. Saboda haka za mu yi iyakacin bakin kokarinmu na ganin kowane dalibi ya koyi ka'idojin rubutu, ta yadda a ko'ina zai iya rubutu ba tare da wata fargabar za a ci gyararsa ba.

    Wannan darasi yana da muhimmanci ga duk wani mai rubutu da harshen Hausa a kowane fanni. Sau da yawa za ka ga mutum ya yi zurfi a karatun Hausa, amma idan ka kalli rubutunsa, sai ka ga akwai gyare-gyare da dama. Wannan ga waÉ—anda ma suka nazarci harshen Hausa a Jami'o'i ke nan. Ina ga waÉ—anda ba su nazarci harshen ba.

    A wannan fagen ma, ni kaina ƘOLO nake. A duk in da aka ga kuskure, sai a ankarar da ni. Na sani a ka'idojin rubutu akan sami sami 'yan bambance-bamcen fahimta a tsakanin masana.

    Sai dai mun yi sa'a a yayin wannan darasi, a gaban babban Shehinmu Farfesa Aliyu Muhammad Bunza za mu rika yi. Da bazarsa za mu rika rawa. Saboda ya riga ya dama mana hurar, sai dai mu É—iba mu sha a cikin littafinsa mai suna: RUBUTUN HAUSA.

    Mene Ne Rubutu?

    Masana da dama sun yi bayanin abin da rubutu ke nufi a tasu fahimtar. Misali:

    "Rubutu wata dabara ce ta yin wasu 'yan alamomi da za su wakilci magana..." (A.M. Bunza 2002)

    Ƙa'idojin Rubutun Hausa:

    Idan ana magana a kan ka'idar rubutun Hausa, ba wani ne shi kadai ya zauna ya ƙaga ya ce dole sai kowa ya bi ba. Masanan harshe ne ke zama daga lokaci zuwa lokaci suna kawo matsaloli da suka shafi rubutun Hausa ana tattaunawa domin a sami daidaito a tsakanin marubuta harshen Hausa.

    A shekarar 1932 ce aka fara yunkurin samar samun ingantacciyar hanyar rubutun Hausa, saboda muhimmancinta a wajen wallafe-wallafe. Wannan yunƙuri ya taso ne a lokacin da Bargery ke yi na rubuta Ƙamusun farko na Hausa.

    A shekarar 1951 an kafa kwamitin inganta Hausa wanda ya dukufa wajen ganin an sami ingantacciyar hanyar rubutun Hausa. A lokacin an yi bitar ƙa'idojin, sannan aka cim ma matsaya gamsasshiya game da su.

    A shekarar 1972, an sake zaunawa an duba waÉ—annan ka'idoji in da aka daidaita wasu matsaloli da aka ga sun taso.

    A shekarar 1980, an sake bitar ƙa'idojin a wurare guda biyu: ɗaya a Jami'ar Ahmadu Bello Zariya. ɗayan kuma a Niyame ta Jumhuriyyar Nijar. Duk dai da nufin samun hanyar rubutun Hausa amintacciya. (Bello: 2005).

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.