Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsafe–Tsafen Maguzawa: Nazari A Kan Bukukuwan Maguzawan Kwatarkwashi (5)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Tsafe–Tsafen Maguzawa: Nazari A Kan Bukukuwan Maguzawan Kwatarkwashi (5)

NA

ABDURRAHMAN LAWALI

 

Maguzawa

BABI NA HUƊU

BUKUKUWAN AL’ADUN MAGUZAWAN KWATARKWASHI

4.0 GABATAWA

A babin da ya gabata na yi tsokaci a kan yadda taƙaitaccen tarihin ƙasar Kwatarkwashi, dangantakar Maguzawan Kwatarkwashi da da Maguzanci, Tsarin shugabancin Maguzawan Kwatarkwashi, Al’adun Maguzawan ƙasar Kwatarkwashi da sana’o’in maguzawan Kwatarkwashi.

            A wannan babin zan yi bayani a kan ire – iren bukuwan Maguzawa da al’adunsu da hanyoyin mallakar macce a Maguzance.

4.1 BUKIN CIKA SHEKARAR MAGUZAWAN KWATARKWASHI

            Kamar yadda muka sani ɗan – Adam mutum ne wanda Allah ya nufa da son jin daɗin rayuwa, sai dai idan bai samu ba, ya yi haƙuri. Kamar haka su ma Maguzawa suna da lokaci da suke keɓe wa irin wannan buki ko shagulgula, wato bukin cika shekara.

            Irin wannan bukin ana gudanar da shi ne bayan an gama aikin gona, kuma amfanin gona ya zo gida. Kamar dai yadda Maguzawa kan inganta sauran bukukuwa irin su aure, bukin zanen suna, bukin kaciya da sauransu, haka shi ma wannan bukin cika shekara suke gudanar da shi. Inda za su aika da goron gayyata zuwa duk inda wasu ‘yan uwansu suke domin gudanar da wannan buki.

            Maguzawan Kwatarkwashi suna amfani da wannan aljani na tsafinsu wanda suke kira Kyauka domin gudanar da wannan buki na cika shekara. Bayan ranar gayyata ta zo, Maguzawa kan tafi gidan shi wannan aljanin Kyauka domin rarrashin sa da ya amince su zo da shi domin gudanar da wannan wasa ko buki. Amma kafin a tafi wurin dole ne a tanadi tulunan giya, baƙaƙen bunsura kamar guda hamsin (50) da jajayen zakaru kamar guda ɗari biyu (200) waɗan da za a yanka masa ya sha jini domin neman amincewarsa.

            Bayan ya amince za a biyo hanya zuwa gari, za a kirawo gwanaye don aljani Kyauka masu ɗaukar kayansa waɗanda da ma an riga an tanade su don irin wannan buki. Sannan su sa ma shi Kyauka wannan suturar. Irin kayan kuwa su ne:- Baƙaƙen tufafi na saƙi da suka haɗa da riguna, zannuwa da sauransu. Sannan zai yi ta yin wasanni iri – iri, ana kaɗe – kaɗe yana rawa, yana fitar da abubuwa na ban tsoro daga jikinsa. Kuma shi wannan buki na cika shekara kan iya ɗaukar kwana goma sha huɗu ana gudanar da shi. Kuma ana zuwa ga sarakuna irin su sarkin tsafi da sauransu.

            Kamar yadda aka sani cewa ba a kallon wasar Kyauka da fararen tufafi, haka nan Bahillace ba ya zuwa kallon wasan Kyauka domin a nasa gani, wai ba duk kowane Bahillace ba ne ɗan halak ga ubansa. Don haka, mai farar sutura da Bahillace ba su zuwa kallon wannan wasan. Idan kuwa suka kuskura suka tafi, tasu ta ƙare. Saboda haka, kafin wannan wasan ta Kyauka ta soma, sarakuna sukan aikawa talakkawansu da cewa su san irin waɗannan ƙa’idoji, idan suna son zuwa kallon wannan wasan.

            Wannan wasa na Kyauka wasa ne wanda ke ƙara fitar da darajar Maguzawa, kuma wanda yake a dole ne a ji tsoron su.Domin idan ka ga yadda Kyauka ke wasa, lalle ka ga abin tsoro. Domin kuwa ita wannan wasa ana fara ta ne da misalin ƙarfe goma sha biyu na dare. Amma da zarar ya fara wannan wasan, ko ina zai haske kamar rana. Wani lokaci ka ga wuta ta kama ta yi sama kamar tafiya rabin kilomita ɗaya wadda kai kanka ba za ka iya tabbatar da iyakacin tsawonta ba. Kuma wani lokaci za ka ji ya yi gumza wadda za ka ji ƙasa na motsi kamar za ta tsage, sai ka ga kowane mutum da dabba sun firgita baki ɗaya. Amma abin mamaki sai ka ga Maguzawa ba su ko damu ba, sai dai ba shi magana kawai suke yi suna yi masa kirari suna cewa;- “Mun tuba, Baba ɗiyanka, Baba ka ga ta kowa, taka ta yi wuyar gani, Ubangiji mabiyanka aiki ba da kai ba a fasa” Haka dai za ka ji suna ta faɗi kuma suna watsa masa turare da giya. Sannan sai ka ji ya yi shiru kuma ya ci gaba  da wasanni iri – iri waɗan da ɗan – Adam bai taɓa gani ba a cikin rayuwarsa na ban tsoro ba. Wanda idan ya yi su za ka ji kamar duniya za ta tashi.Domin kuwa ita kanta ƙasa za ka ji tana motsi, itatuwa kamar za su faɗi domin tsananin iska. Haka Kyauka ke gudanar da irin wannan wasansa har ranar da sarki ya sallame su. Inda zai ba su babbaƙun shanu da bunsura da zakaru da sauransu. Sa’annan su koma gida. Daga ƙarshe su sallami shi Kyauka su mayar da shi gidansa, sai kuma wata shekara dai – dai wannan lokaci.

4.2 BUKIN WASAN BAURA DON NUNA JARUNTAKA

            Wasan baura ana gudanar da shi sau ɗaya a shekara, a lokacin kaka bayan an cire kayan gona an kawo gida. Ranar kasuwar garin ake gudanar da ita. Tana cikin bukin wasanninsu na shekara da ake aiwatarwa na al’adun gargajiya da suka gada tun kaka da kakanni a Maguzance. A ƙofar gidan magajin garin nan ne ake gudanar da ita. Kamar yadda aka saba a Maguzance, ana wannan wasa domin nuna jaruntakar Maguzawan ƙasar Kwatarkwashi a fili don ana yin ta kamar wasan “Dambe”. Sai dai tafi kama da wasan kokowa wadda muka sani. Ita wannan wasa ta baura idan za a gudanar da ita ana share fili tare da yi masa zobe da ‘yan kallo na ko’ina da suka zo. Su ko a bisa al’ada sai kowanensu ya je wurin bautar tsafin Magiro na Magajin dutse domin neman sa’a. Sa’annan a shigo da guda – guda, ana yi masu kuwa da kirari tare da ihu gaba ɗaya. In an zo za a yi kirari ga ɗai – ɗansu, sai su sa wasu zobba masu bala’in kaifin gaske kamar reza. Da su ne ake bugun mutum a duk inda aka samu, ko a fuska ko a kunne ko a kunci da dai sauran sassan jiki. A nan ake bugewa har a kai wani ƙasa kwance galala a cikin jini baje – baje. Amma akwai maganin da suke sawa idan an bugi mutum har fata ta yanke. Suna haɗa kashin shanu a kwaɓa da wani magani, sai a shafa wurin, shi kenan zai tsaya, ya koma shafewa kamar ba a yi yankan ba.

            Masu wasar da ‘yan kallo duk suna gaf ne da bakin duwatsun tsafi, wanda ake bi ta ƙarƙashinsa a hau samansa. A nan kusa da wurin akwai kogunan duwatsu daban – daban da manya da ƙanana ana ce masu, “komo”. Ana haɗa waɗanda ba su taɓa sanin juna ba, wanda yake kowanensu ana ji da shi a garinsu a kan jaruntakarsa ta wannan wasan Baura ƙwarai. 

            Akwai mutumin da ya fi fice ƙwarai a wannan wasa ta Baura, ana ce masa “KALAGU” don shi ne ma magajin tsafin Magiro ya ba shugaban wasan Baura na ƙasar Kwatarkwashi don ya riƙa gudanar da ita yadda ya kamata. Kuma ga garuruwan da suka fi yin fice a ƙasar kamar su: Hujrin giya, Samawa da Sankalawa, su ne manyan garuruwa. Ana son ko wane ɗan wasa ya zo da makiɗansa don ya yi masa kiɗa domin ya yi zafin nama da jaruntaka, tare da nuna ƙwazonsa a fili. A wurin haɗuwarsu makiɗan suna faɗin haka a cikin kiɗa da kirarin ‘yan wasa:

“Ga ka nan tafe!

Ga ka nan tafe baƙo!

Ga ka nan tafe baƙo, ba a san halinka ba!”

            Duk ‘yan wasan suna ciccika suna hurji, har sai an gwada tsakaninsu sa’annan a san na ƙwarai wanda shi ne jarumi.

 

 

 

4.3 BUKIN WASAN TASHEN MAGIRON MAGAJI

            Wannan wasar tashe ana gudanar da ita ne a shekara idan aka dawo daga wasan tsafin bautar Magiro na magajin dutse. A bisa ga al’adar tasu sai an gama bautar shekara sa’an nan a aiwatar da ita. Ga yadda ake aiwatar da ita:

            Da kaka ake gudanar da tashen bayan an gama ɗebe kayan gona sarai ba sauran komi sai karan gona ko su ko an fara adana su saboda dabbobi. Don tashen murnar kewayowar shekarar bautar tsafin Magiro na magajin duwatsun Kwatarkwashi da gama bautar lafiya, tare da murnar samun amfanin gona na wannan shekara mai yawa. Akan haka ne yaran Maguzawa ke gudanar da al’adunsu da suka iske tun daga kaka da kakanni ta gudanar da wannan wasa ta raha da annashawa da nishaɗi da ban dariya ga jama’a na gida – gida ko na kan dandali masu fira a waje. Wannan wasa ta tashe ana gudanar da ita a tsakanin mazansu da matansu, wato ‘yan mata da samarinsu da ke zaune a dandali suna hira barka da samun kewayowar wannan shekara. Sai su mutanen su ce barka kadai, tsafin su ya maimaita.

            Su matansu suna tafiyarsu daban ne, suna gudanar da yadda ake aikace – aikace nasu a gidajensu cikin raha tare da ban dariya. Su samari nasu daban suke yi kuma ba sukan shiga gidajen ba sai na ‘yan uwansu. Amma babban abu gare su shi ne su gudanar da wannan tashe a mazaunin mutane na dandalin hira, a inda dattijai iyayensu suke zama. Ana kwaikwayon ayyukan gargajiya ne na gado kamar ƙira, noma, wanzanci da sauransu. Su yara ƙanana su ke haɗewa mazansu da matansu. To Maguzawa sun yarda da haka don su ma su gudanar da nasu daban har su iya a hankali. Bayan haka, ana samun manyan  mutane suna gudanar da wannan wasa na tashe matsakaita, masu aure, nasu yakan zo ne daga ƙarshen watan da suke yi, don kamar kowane rukunin jama’a suna da nasu lokacin yin tashe.

            Da haka ne ake gudanar da wannan wasan tashe na tsafin bautar Magiro na magajin duwatsu, har akai ƙarshensa a cikin raha da annashawa da ban dariya ga jama’a don shi ne watan farin cikinsu.

4.4 AL’ADUN DA SUKA SHAFI RAYUWAR MAGUZAWA

            Al’adun Maguzawa suna nufin sababbiyar hanyar rayuwarsu. Don haka, al’ada ita ce hanyoyin gudanar da rayuwa ta yau da kullum da ke faruwa ga rukunin jama’a masu zama wuri ɗaya ko yankin gari, ko ƙasar baki ɗaya. Maguzawan ƙasar Kwatarkwashi sun samu kansu a wannan yanki tun kaka da kakanni. Masu salsalar asali waɗanda suka fara zama a wannan wuri, su ne suka samar da al’adun rayuwa a tsakaninsu. Don haka suke gudanar da komai nasu a bisa wannan tsari na yau da kullum. Sun kuma ƙunshi matakan rayuwarsu na tun daga haihuwarsu  har zuwa mutuwarsu. Akwai yadda ake gudanar da abubuwan da suka shafi tsarin rayuwarsu tun daga al’amurransu na kasuwanci har zuwa abin da ya shafi shugabanci da sauran ƙananan bukukuwan wasanni da suke gudanarwa daban – daban.

            Ga su kamar haka, bi da bi a tsare, tare da bayanansu da yadda ake gudanar da bukukuwan kamar haka a jihar Zamfara.

a.      Auren Maguzawan ƙasar Kwatarkwashi

b.      Haihuwa a Maguzance

c.       Mutuwa a Maguzance

d.     Sauran fannoni na al’adun Maguzawa

4.5 NEMAN AUREN MAGUZAWAN ƘASAR KWATARKWASHI

            Aure hanya ce ta ƙulla zama tare tsakanin jinsi biyu na mace da namiji ba tare da an iyakance adadin zamansu ba. Sai idan mutuwa ta yi halinta.Ana yin aure bisa ga samun yardar da amncewa a tsakanin saurayi da budurwa. Da kuma samun amincewar iyayensu da kakanninsu domin gudanar da shi, kamar yadda al’adarsu ta zo da shi.

            Al’adun Maguzawa sukan fara la’akari da shekarun waɗanda za a yi ma aure tsakanin saurayi da budurwa ko mace da namiji.Sai dai an fi duba na mace in ta kai shekara goma sha bakwai zuwa sha takwas (17 – 18). Daga nan ake yi masu aure da namiji da ya kai shekaru goma sha takwas zuwa ashirin (18 – 20). Kafin a kai ga aure, suna gudanar da soyayya a tsakaninsu tun daga haɗuwarsu da suke yi a ranar cin kasuwar garin, musamman ma in lokacin kaka ta yi (lokacin da aka gama aikin gona). Saboda mata suna zuwa cin kasuwa a ƙauyuka da garuruwan da ke kewaye da duwatsun. Don haka, su ma maza ba a bar su a baya ba. Samari suna zuwa cin kasuwa don ba wani sauran aikin gona da ya rage a daji. Samari da ‘yan mata suna haɗuwa a ƙauyukan da garuruwan don gudanar da kasuwancinsu tare da gudanar da samartaka da ‘yan matanci a tsakaninsu da marece bayan rana ta yi sanyi.

            Bayan ‘yan kasuwa sun fara watsewa, irin dattijai maza da tsofaffin mata da sauran waɗan da bai kamata su tsaya ba. Daga nan ne sai makiɗa su fara aikinsu na kiran ‘yan mata duk inda suke a lungun kasuwar. Idan suka ji wannan ƙarar kalangun,to sai su zo ko sun sayar da abin da suke talla, ko ba su sayar ba. Sai bayan sun taru sosai har sun fara gudanar da rawa. Bayan an taru sai su fara rawa ta ɗai – ɗaiku don jawo hankalin samari da ‘yan kallo mazansu da matansu. Ana taruwa ƙwarai da gaske a yi ta kiɗa. Wasu daga cikin ‘yan matan da samarin sun riga sun gana da junansu a wurin kasuwanci. Wasu ko ba su samu dama ba sai a dandalin taron kiɗa ne za su yi nasu zaɓe ta hanyar nuna soyayya da ƙaunar juna. Sai tana cikin gudanar da rawa ya shiga ya taya ta kuma ya yi mata kari sosai. Haka za a yi ta yi har lokacin tashi ya yi. Kowa ya koma ƙauyensu da garuruwansu sai kuma wata ranar kasuwa ta gewayo. Bayan sun gama rawa tare, ya gama zuba mata karin kuɗi, sai su fito don wasu su shiga, su ko suna gefe don yin zance ko hira a tsakaninsu saboda soyayya ta shiga kenan. Shi zai faɗa mata ƙauyensu ko garin da ya fito, idan ba daga gari ɗaya suke ba. Ita ma haka za ta yi mashi kuma za ta gayyace  shi zuwa garinsu ko gidansu don ya ga iyayenta.Ko kuma shi ya gayyace ta zuwa garinsu a gidansu don iyayensa su san cewa ga wadda yake so ta zo. Wannan gayyata da ake yi tsakanin saurayi da budurwa na zuwa garuruwansu shi ne ake ce ma “Tsarance”.

            Bayan sun zama jiki tsakaninsu yana haɗuwa da ita a duk ranar kasuwa ko ta garinsu ko ta wani gari don yin zance, sai ya fara zuwa garinsu wajen zance. Ita kuma idan bai zo ba ko in ta samu hali ita ma sai ta je garinsu don tayi zance da shi. Za ta gayyace shi ya je garinsu don wasar da ake gudanarwa a duk shekara a tsakanin ‘yan mata da samari. Inda ‘yan mata daban – daban suke taruwa su ɓarje guminsu don yin rawa iri – iri a tsakaninsu don samarinsu su ga abin da ya ba su sha’awa da gwanintar da suke nunawa. Samarin za su riƙa yi masu kari har a tashi wasan.Wannan ita ce hanyar rayuwar da Maguzawan ƙasar Kwatarkwashi ke bi wajen neman aure a tsakanin saurayi da budurwa. Kafin gudanar da aure akwai matakai kamar haka:

1.      Haɗuwarsu a kasuwa da wurin wasan kiɗan kalangu

2.      Tsarance a tsakanin budurwa da saurayi

3.      Shigowar iyayensu

4.      Hawan duwatsu don kamo maiki daga sama zuwa ƙasan duwatsun.

4.5.1 SOYAYYAR TSARANCE TSAKANIN SAURAYI DA BUDURWA

            Wannan tana faruwa ne tsakanin saurayi da budurwa bayan sun haɗu a kasuwa sun yi zance sai ta umurce shi da ya kwana a gidansu kamar yadda al’adarsu ta nuna. Galibi a kan ba su ɗaki ne su yi hira har dare ya yi ba tare da sun sani ba.Idan ya gane dare ya yi zai fito, sai ta faɗo wa iyayenta cewa zai tafi. Sai a samu tsofaffi a gidan su zo su yi masa maganar cewa ya kwana a nan ɗakin mana. Idan dai da gaske yake yana sonta. Ita za a yi mata magana duk abinda ya dace tayi mashi na so da ƙauna, ka da ta yarda ranshi ya ɓaci. Kuma za su ji abun da ya gudana tsakaninsu daga tsafin gida. Idan tsafinsu ya kai su gobe. Shi ke nan sai a rufe su a ɗaki ɗaya su kwana tare har gobe. Amma shi namijin ba zai yarda ya kusance ta ba saboda amincewa da ke tsakaninsu na so da ƙauna a kan aure, tare da nisanta ga kauce ma abin bautar su bisa ga dokokinshi. Za su kwanta tare har safiya ta waye ba zai kula da ita ba, baya ga hirar da za su yi ta yi har barci ya ɗauke su. Safiya ta waye sannan a buɗe su. Kafin ma su ga ɗiyar tasu, ta faɗa masu abin da ya faru za su iya yanke hukuncin abun da ya faru a tsakaninsu tun daga jiya zuwa wayewar safiyar yau.

4.5.2  BUKIN WASAN KALANKUWA

            Ana gudanar da shi ta hanyar gayyatar juna a tsakanin saurayi da budurwarsa. Ita ke fara aiko masa da goron gayyata tana mai cewa ya zo wasan kalankuwa a garinsu. Wato babban birnin ƙasar, nan garin Kwatarwashi don a nan ake gudanar da ita tsakanin ‘yan mata da samarinsu. Za a taru sosai ana ta kiɗan kalangu yana tashi ko’ina a garin da kewayen shi, kowa zai aika mata da damen hatsi. A ranar da zai zo za a yi masa gagarumin tarba tare da kayayyakin abinci iri – iri da na sha, a cikin ɗakin da zai kwana a nan gidansu yarinyar. Farko zai gaisa da ita yarinyar tashi, sai a haɗa shi da yaro don ya gaisa da iyayenta mazansu da matansu. Sa’annan ya dawo masaukin da aka yi masa su ci gaba da hira ko zance da budurwar tasa. Bayan sun gama zance sai ta koma can cikin gida wurin iyayenta ta kwana. Shi kuma ya kwana a nan ɗakin, ba za su sake haɗuwa da yarinyar ba, sai idan ya ji ƙarar kalangu yana tashi. Zai tashi ya nufi can dandalin wasan kalankuwa don ya ga mi ke faruwa ne a can. A lokacin da zai je can an riga an taru ƙwarai tsakanin ‘yan mata da samarinsu, da yara da manya da ‘yan kallo, maƙil a filin. Ita kafin ta je wurin wasan kalankuwan sai an yi dafe – dafen abinci iri – iri da shaye – shaye,kamar su tuwo da naman kaji, da na agwagi da zabbi, ga masu hali har da naman ‘yan kuikuyo da ‘yan awaki, ga fura da nono, ga kuma tulunan giya daban – daban.

Za a raba biyu ne, ɗaya a kaishi can wurin wasar, ɗaya kuma a bar shi nan gidansu yarinyar.Saboda idan ta dawo daga wurin wasar ita da abokaninta za su taru tare da matan maƙwabtansu a cinye abincin sarai na murna da wannan buki. Shi ko bayan an tashi taro sai su koma gefe ɗaya daga wurin dandalin wasan kalankuwan su fara hidimar cin abincin. Amma kafin nan zai isa filin wasan, ya kuma tarar da ana kiɗa, ‘yan matansu suna ta sheƙa rawa. Da zarar an ga samarinsu tafe, to sai a canza kiɗa da cewa su rinƙa shigowa da ɗai – ɗai. Idan sun fara, duk wanda ya ga budurwarsa ta shiga rawa zai natsu ya ga shin me zai faru. Tana cikin yi a lokacin da ta ba shi sha’awa a kan gwanintar ta da tayi ta rawa. Sai shi ma ya shiga tare da abokansa suna rawa, sun kewaye ta. Sai ita ko ta zauna bisa wata kujera da ke nan tsakiyar filin taron, sai ‘yan kallo su riƙa kuwwa da kirari da ihu tare da guɗa.

Bayan sun tafi sai shi ya ci gaba a hankali, ita kuma ta tashi da rawa sosai har ya tsima, ya fara yi mata kari har sai an zo an jaye shi da ita cikin filin don wasu su shigo su ma. Ana yin haka don a tabbatar da cewa fa lalle wance ta samu masoyinta sai jiran lokacin aure kurun. Amma kafin nan sai uwaye sun shigo kuma an nuna jaruntakar hawan duwatsun don ɗauko maiki daga sama zuwa ƙasan duwatsun magajin Magiro.

4.5.3 SHIGOWAR IYAYE GA SHA’ANIN AUREN MAGUZAWA

Bayan an gama wasan bukin kalankuwa na tsakanin ‘yan mata da samari, duk uwayensu suna sane da soyayyar da ke gudana tsakaninsu, sai saurayin ya aika a faɗa gida, wato ga iyayensa game da abunda ke faruwa tsakaninshi da wance. Ko kuma shi ya je wurin iyayensa da kansa amma tare da abokansa don ya faɗi cewa shi ya ga ‘yar gidan wane, kuma yana sonta da aure. Maguzawa suna yin haka ne saboda nuna tarbiyya a tsakaninsu da ɗiyansu saboda akwai kunya.

Zai ce ya ga yarinya ‘yar gari kaza ko ‘yar gida kaza ko kuma gidansu wane sai a samu tabbatar magana tare da samun yardar junansu. Shi ke nan sai uwaye su taru da na gidansu yarinyar da na saurayin don su tattauna maganar ‘ya‘yansu. Daga nan sai a ba da shedar aure ko kuma kuɗin aure. Za a kuma kawo kaya a gidansu yarinyar daga gidan su saurayin, sai su yi masu maganar aure don a ba su izini su shigo. Shi ke nan sai shekara ta dawo zuwa hawan duwatsun tsafin Magiro na magaji don nuna jaruntakar ɗauko maiki daga saman duwatsun zuwa ƙasa.

4.5.4 BUKIN HAWAN DUWATSU DON ƊAUKO MAIKI

Shi ɗauko maiki a ɗauro ma jarumawan samari domin nuna bajinta kan aure, ana taruwa  ne a ƙofar mai garin a ranar da kasuwar garin take ci. Bayan an taru mazansu da matansu da yara mata da maza da tsofaffi masu sauran ƙarfi a jika waɗan da suka san yadda ake gudanar da bukin da aka gada tun kaka da kakanni. Jarumawan magajin Magiro suna gaba ana biye da su, ana tafe ana kiɗe – kiɗe da raye – raye da ihu da kuma guɗa tare da kirari da ake yi wa masu son nuna gwanintar a kan ɗauko tsuntsun nan na maiki daga saman duwatsun zuwa ƙasansu. Akan ɗaura gashin maikin a kafaɗa tun gida don nuna su ne jarumawan bana.

Bayan jarumawan magaji sun haye sai a ba su umurni da cewa duk samarin su haye kan duwatsun. Bayan an haye a ɗauro masu maikin a bayansu dukkansu, sa’anan ace kuma su koma ƙasan duwatsun. Duk wanda ya kai na shi ƙasa to shi ya isa aure, wanda ko bai samu kaiwa ba sai wata shekara ke nan. A wurin hawa ana samun mutane masu mutuwa ko kakkarewa idan sun faɗo daga saman duwatsun a wurin hawa ko sauka. Kafin su zo nan sai an ci an sha ƙwarai, kuma ba za a fara hawa ba sai an yanka ma tsafin Magiro na magaji baƙaƙen bunsura ko ‘yan kuikuyo don ya sha jini ya sheda. Sai a je da naman gida a dafe kowa ma ya ci.

Kuma yadda aka je wurin bautar haka za a koma gida da raye – raye da kiɗe – kiɗe da sauransu, har a kai cikin gari. ‘Yan kallo duk suna sheda abun da aka yi a wurin ɗauko maiki.Tsafin ya yarda wasu su yi aure, wasunsu ko bai yarda ba sai shekara ta dawo. Daga wannan sai ranar baiko za a raba goro ga ‘yan uwa da maƙwabta da abokan arziki na anguwanni da ƙauyuka da na garuruwa su zo don baikon wane da wance. Za a raba goro a ranar za a zo da tabarma biyu daga gidan ango da garin rogo da hura da nono da gishiri. Ana zuwa da ɗan akuya daga iyayen ango da sauran kayan ciye – ciye da shaye – shaye da na tanɗe – tanɗe da lashe – lashe da makamantansu.

4.5.5 RANAR ƊAURA AUREN MAGUZAWA

A ranar ɗaurin aure, ga yadda al’adar Maguzawa take tun kaka da kakanni. Ranar aure galibi akan sa ranar cin kasuwar garin. Kafin a ɗaura aure ana sa amarya lalle, a yi mata tirgeza a saman turmi. Iyayen ango mazansu da matansu za su haɗu su ɗunguma zuwa gidan iyayen amarya. ‘Yan uwa da abokan arziki za su wuce wurin ɗaurin aure a gidan amarya. Suna isa su ma za su ɗunguma dukkansu su fito wajen ɗaura auren wance da wane.

Sai dai wurin zamansu duk ya bambanta da na kowa daga cikinsu, na tsofaffi daban yake, wurin mata daban, wurin samari da ‘yan mata duk daban suke. Sa’an nan ƙananan yara nasu wuri daban ne. Sannan ɓangaren ango daban na amarya daban. Kowanensu da mutanensa daban – daban. Za a kawo tulunan giya da na hura da nono a cikin tukwane da goruna da ƙwaryayyaki na tuwo daban – daban. Ga nama iri – iri daga na kaza da zabbi, da agwagi da akuyoyi da na bunsurra daban – daban, da soyayye da dafaffe da gasashshe da sauran kayayyakin bukin aure.

Bayan an gama sai a gayyaci kowane ɓangare na ango da na amarya, a samu dattijo ɗaya – ɗaya don su zo a ɗaura aure. Sai kowanensu ya taso su haɗu a innuwa ɗaya don su yi barkwancin auren. Za a samu dattijo ɗaya wanda yafi kowa iya barkwanci daga gidan amarya ya fito da lafuzzan da zai ce, shi ne “Daram” na ɗaura auren wance da wane, in ga masu abu kazar uwa! Ko uba! Da zai raba! Wurin furta wannan lafazi akwai ɓota da barandami da mashi, sai ya buga su a ƙasa tare yana yin kirarin tsafin garin zuwa na ƙasa. Shi kenan sai kuwwa da ihu da guɗa tare da kiɗe – kiɗe da raye – raye da sauran abubuwan jin daɗi.Wasu ma har da zage – zage tare da wasanni iri – iri.

Bayan haka ana samun wani daga wancan dangin, shi ma ya tashi ya yi ihu ana cikin raha sai ya ce shi ne wane ya raba! Wato ya rama zagin da aka yi wa sashensu saiya kawo nasa dalilan ya zauna. A kawo wani abun kunya da wani dangi suka taɓa yi, sai a yi ihu a taɓa, tare da kekkewa gabaɗayansu.Sai a koma a yi ihu a ce shi ke nan. Misali, sata ce ko maita ce, ko kwartanci ko wani abun kunya ne na daban. Yana gamawa sai duk taro a ce “i”, to shi ke nan an raba. Ana raba aure nan wurin ɗaura shi idan akwai wani ƙazafi a tsakanin dangin ko amarya da ango ko wani dalili mai ƙarfi na daban, da sauransu.

Idan an gama za a yi wa amarya wanka a kaita gidan ango. Kafin haka, a wurin wankan ana yi mata tsirara ne tana bisa turmi, a nan sama ake yi mata wankan.Ana gabatar da wasu abubuwa da suka shafi tsafi ta samun jajayen zakaru guda biyu, ɗaya a riƙa kewaya mata a bisa kanta tare da faɗin  tsafin nasu, ana yi mata ado ne ana sa mata gashin maiki a kanta. Ana aza ta kan goɗiya ko asa mayaƙan tsafi, jarumawa masu ƙarfi su ɗauke ta su zagaya da ita, in har wurin tsafin gari za a shigar da ita cikin wani kogo ne na duwatsun garin Kwatarkwashi. Ana ce ma wurin “Kwaman Magiro”. Yana da tsawo ƙwarai, daga nan garin an fita garin Kura. Masana tarihin garin sun ce “Akwai takobi da mashi da barandami irin na da, masu nauyi sosai kamar babban dutsi, tare da kwari da baka duk a nan ciki. In ba ƙato, jarumi, majiyi ƙarfi to ba mai iya tallabasu ko ɗaukar ɗaya daga cikinsu. Sai an taru kamar mutum biyar zuwa goma sannan a ɗauki ɗaya daga cikinsu”.

Wasu kayayyakin ƙasar na tarihi har yanzu wasu na nan cikin “Kwaman duwatsun”. A cikinshi ne ake gudanar da tsafin aure tsakanin ango da amarya da kuma na mutuwa. Idan mutum ya mutu sai an kawo shi nan cikin kogo don tsafi ya shaida mutuwarsa, tare da roƙar mashi zaman shi kaɗai a cikin rami ga tsafinsu na ƙasa baki ɗaya. An ce wani yana ɗaukar aƙalla mutum ashirin (20), a nan ake binciken sirrin amarya, ko wani ya taɓa saninta kafin mijinta. To idan ta taɓa aikata wani abu wanda yake da muni sai a shirya su tsakaninta da mijinta. In yana sonta sai a rage kuɗin aurenta ta mayar masa da rabi a ɗaura aure. Idan ba ta taɓa sanin wani ba sai ta rantse da tsafinsu na Magiro na magajin duwatsun Kwatarkwashi. Za a aza ta bisa turmin tsafin ayi mata surƙullensu tare da yadi guda uku, baƙaƙe da ɗan akuya. Ana kuma ɗaura mata gashin maiki don adon amarya ta shiga bukin aure.

Za a nemi ƙatta majiya ƙarfi, jarumai, su uku, don su zo da ɗan akuyan nan wanda za a yi tsafin auren da shi.Za a aza shi bisa turmi, ɗaya yana riƙe da ƙafafu biyu da na gaba da na baya, ɗaya zai ɗauko takobin nan na tsafin ko mashin ko barandamin nan domin a sare ko a kashe ɗan akuyan nan don tsafin ya sha jini. Idan ya aikata haka amma turmin bai rabu ba to sai ya sake sau ukku in ya sare, to tsafin ya ci idan ko bai aikata haka ba to lallai ne tsafin nasu bai yarda da auren ba sai wani lokaci.Idan ya amince to lalle sun zama amarya da ango ke nan, sai zaman aure.

Bayan wannan gaba ɗaya tsakanin amarya da ango, sai tsafin kai amarya. Bayan anyi na ango, ana gabatar da shi a washe gari da daddare, za a je a kai ɗan akuya da zakara da tulun giya duk can za a baro su cikin “Koman dutse”, a koma tun da sassafe, idan an iske an shanye giyar, su ko zakaran ko ɗan akuyan duk sun mutu to lalle tsafin ya yarda da auren. Idan ko ba a shanye giyar ba kuma ba su mutu ba, to lalle tsafin bai yarda da auren ba. Sai bayan wata ɗaya ranar kasuuwar garin a sake komawa wurin tsafin.

4.5.6 ZAMAN AUREN MAGUZAWA

Ga al’adar zaman aure na Maguzawa kusan komai mace tana yi a gidan da aikin daji, da noma, da renon yaran gidan. Ita ke samo ma yaranta abun da za su ci a gidan, ga gyaran abinci kafin a kai ga cin shi. Mazansu ko akwai shan giya, ga biɗar aure duk shekara har dai ace kayan gona sun yi kyau ƙwarai, ga su da gudun mutuwa. Yana raba kayan gona kashi biyu ne, ɗaya a kai gida asa rumbu na ruhewa don ci da shayarwa ga iyalansa. Sauran kuma zai sayar don bukukuwan dangi da yin zawarci domin neman aure. Matar abun da ta noma ne za ta ciyar da ‘ya‘yanta tare da yin hidimomin yaran idan ta tashi. Za ta yo itace na sanwa, ta ɗauko ruwa a rafi tare da sauran ayyukan gidan.

Idan miji zai sake yin wata amarya, to duk hidimomin gidan da ɗawainiyar bukin duk suna ga uwargida. Za ta yi daɓen ɗaki da ba da nata gudunmuwa na zuwan amarya. Amarya za ta yi wata biyu ba ta aikin komai. Sai uwargida, tana sa wa ana yi mata aikin gayya a gonarta. Shi ke nan sai in zai sake wani aure ita ta biyun za ta yi wa amarya hidimar ban da uwar gidan. Ga al’adar Bamaguje bai da iyakar mata sai ya yi ta yi saboda a samu zuri’a masu yawa, ya yi alfahari ko tinƙaho da cewa yana da yawan mutane kaza.

 

 

4.6 BUKIN SUNAN MAGUZAWAN KWATARKWASHI

            Maguzawa a wancan lokacin suna gudanar da al’adunsu na ba su zuwa goyon ciki gidajen iyayensu sai bayan an yi suna bayan sati ɗaya, wato kwana bakwai kenan, sa’annan mace ta je gidan iyayenta don goyon jariri.

            Za a iya tura mata wata tsohuwa a lokacin da take can gidan mijin don a kula da ita saboda lafiyarta da samun sauƙin naƙudar haihuwa. Bayan an haihu lafiya tsohuwar ta wanke jariri da ita mai jegon a yi mata wanka da ruwan zafi, sai a yanke wa jaririn cibi. Ita kuma uwar tana shan kunun jego tun daga ranar haihuwa har zuwa wata uku tana yi ba fashi, don samun lafiyar jikinta da na jaririn ta.

            Zuwa wata biyar (5) ta samu lafiya, idan abin da aka haifa namiji ne ana kashe masa bunsuru ne a matsayin naman ƙauri don rarraba wa mutane. Ita ma mai jego ta yi shagalinta don ta samu ƙarfin jikinta. Idan mace aka haifa ana kashe mata ɗan akuya ne don ya zama naman ƙauri na mai haihuwa. Mai jego ba za ta fito waje ba, a kodayasuhe tana nan a ɗakinta har sai ranar sunan jinjirin ne za ta fara fitowa daga ɗakinta.

            A ranar ana yin asubanci tun da sauran dare a je wurin tsafin garin na wakilin Magiro ko shi tsafin Magiron cikin kogon duwatsun. A nan za a gudanar da tsafin jaririn a sa masa gashin maiki a rufe shi ana yanke dabbobi kamar yadda ake gudanarwa na auren don tsafin ya sha jini ya shaidar da an samu ƙaruwa.

            Ita uwar ana roƙa mata lafiya ne tare da abun da ta haifa a can wurin tsafin. Bayan an gama sai a dawo gida domin a ci gaba da shugulgulan bukin suna.

A al’ada ba za a faɗi sunan jariri ba, ba wanda  ya sani sai kakanninsa, kuma ba za su faɗa ba sai ya girma ya kai ga aure ko a ranar da za a ɗaura masa aure. A lokacin za a faɗa masa sunansa na ƙwarai. Duk wancan lokacin sunansa na laƙani ne ake kiransa da irin nasu na kakanni. Haka bukin suna yake gudana a Maguzawan ƙasar Kwatarkwashi da ke cikin ƙasar Zamfara.

4.7 BUKIN KACIYAR MAGUZAWAN KWATARKWASHI

            Kamar yadda muka sani cewa dole ne kowace al’umma da irin nata hanyar bukin kaciya. Haka nan Maguzawan ƙasar Kwatarkwashi suna da nasu. Suna yi wa ‘ya‘yansu kaciya ko kuidu tun suna da shekara bakwai zuwa goma (7 – 10). Ana yanka masu bunsuru ko ɗan kuikuyo, daga nan sai a ci gaba da ba shi zabbi da kaji ana kuma sa masu magungunan gargajiya don ya samu sauƙi ya warke rauninsa da wuri. A al’adance lokacin sanyi ake yin kaciyar, ba a yi wa yaro wanka sai bayan bakwai uku, ya warke sosai. Maguzawan Kwatarkwashi na gudanar da tasu kaciyar kamar haka:

            Kyauka wani wasa ne da ake yi a cikin daji a lokacin da ake yi wa yara kaciya. Kamar yadda Muhammadu Kalgo (2002) ya ce “Shi dai Kyauka wani aljani ne wanda ake kai wa yara maza idan lokacin kaciya ya yi domin ya yi masu kaciyar”.

            “Rankaratu” da Wudiga su ma wasu gumaka ne waɗan da ake fara kaiwa waɗan nan yara kafin a kai su wurin da za a yi masu kaciyar ta Kyauka. Kuma Malam Muhammad Kalgo (2002), ya ce “Ana kuma kiran wannan aljani da ‘yan Kyauka ke tsafi da shi da suna “Mai diyaku”. Lokacin yin wannan kaciya ne, tun daga lokacin da yaro ya kai shekara tara (9) kuma har sai adadin yaran da za a yiwa wannan kaciyar ya kai ɗari (100) ko fiye da haka.Kuma ko da yaro zai kai shekara talatin (30) idan har ba su kai wannan adadin ba, to ba za a yi masa kaciyar ba.

            Za a ɗauki dukkan waɗan da za a yi wa kaciyar zuwa wani daji inda za a yi wa kowannensu bukka, wanda zai riƙa zama har sai ya warke kafin ya dawo gida. Ranar kaciya za a gayyaci duk ‘yan uwa na nesa da na kusa domin halartar wannan buki na kaciya. Kuma kowa zai bayar da tasa gudunmawa.Wani bunsuru baƙi, wani jan zakara, kai ga dai su nan. Wasu giya, wasu abinci iri – iri. Bayan an gama kaciyar za a ci gaba da shagulgula a cikin daji wanda za a ɗauki kwana da kwanaki ana gudanarwa.

            Haka kuma, duk wanda zai tafi wurin wannan wasa, dole ne ya tanadi baƙaƙen kayan sawa. Idan kuma mutum ya yi karanbanin zuwa da farar sutura, to shi sai dai uwarsa ta haifi wani, domin kuwa nan take zai faɗi ya mutu. Babu wanda zai san lokacin da za a yi wannan kaciya. Gari na wayewa za a ga yaran duk da kaciyarsu, kuma idan aka tambaye su, su kansu yaran cewa, wa ya yi masu kaciya? Za su ce su ma ba su sani ba, sun ganta ne kawai.

            Kuma bayan kwanakin da yara za su yi a cikin daji, wato kwana goma sha huɗu (14), idan lokaci ya yi iyayensu kan tafi domin dawowa da su gida. Wasu za a tarar sun mutu, kuma iyayen daga zuwansu za a miƙo masu kayan yaran da suka mutu. Da zaran an miƙo maka waɗannan tufafi kasan cewa ɗanka ya mutu kenan. Kuma wannan aljani wanda ya yi masu kaciya, wato Kyauka, shi ne ke tsaronsu, abincinsu da abin shansu duk suna hannunsa.

            Lokacin da iyayen waɗannan yaran suka tafi domin su dawo da su gida, za su shaida wa Kyauka cewa yau za mu tafi da ‘ya‘yanmu gida. Shi kuma zai ce “a’a” bai yarda ba sai fa idan an yi alƙawarin ba shi ɗaya a matsayin ladar aikinsa. A nan ne za a ƙulla alƙawali da iyayen waɗannan yara, su ce za su ba shi, amma sai sun kai bakin garinsu. Shi zai amince kuma ya bi su har bakin garin inda zai tambayi alƙawalinsa. A nan ne fa ake jani – in – jaka sai sun kai ga jifarsa da duwatsu har zuwa nesa da gari, kana ya koma yana mai cewa “ba haka muka yi da ku ba. Amma tun da kun yi mani haka, to Wudiga ya saka da alheri (wato maimakon Allah ya saka da alheri)”. Kamar dai yadda aka riga aka ambata cewa Wudiga gunki ne na tsafin Maguzawa.

            Idan sun isa gida, wanda ke da mata a cikin su ‘yan kaciyar zai tafi ɗakin matarsa, wanda ba shi da mata ya yi ɗakin uwarsa. A nan kuma za a sake ɓarkewa da shagulgula na murnar ganin ‘yan kaciya sun dawo lafiya.A yi ta dafe – dafe da ciye – ciye da shaye – shaye da makamantansu.

4.8 BUKIN MUTUWAR MAGUZAWAN KWATARKWASHI

            Maguzawa suna da hanyoyin al’adunsu na rayuwa bisa ga tsarin bautar tsafin Magiro. Akwai bukukuwan mutuwa wanda Maguzawan Kwatarkwashi ke gudanarwa, idan mutum ya mutu ga yadda suke gudanar da bukin kamar yadda suka gada tun daga kakanninsu:

            Idan mutuwa ta kama su, ta hanyar rashin lafiya ne ko wani haɗari ko ta hanyar faɗa ne ya mutu, in ya bar iyali da yawa to lalle za a yi masa shagulgulan bukin mutuwarsa tare da yin kiɗe – kiɗe da raye – raye. A samu taruwa wurin bukin tun daga kakanni da iyaye da matan da ‘yan uwa da ɗiyansa da jikoki da maƙwabta, tare da abokan arziki duk sun hallara a bukin mutuwarsa.

            A lokacin da yake rashin lafiya ana sa masa wani dattijo ya dinga diba shi don jinya tare da ba shi magungunan warkewa. Idan bai samu warkewa ba ya kai ga mutuwa, shi zai shafe masa idanunsa da ruwan magani a kuma yi masa wanka da su don kada ya ruɓe zuwa kwana uku kafin a je wurin rufe shi.

Ba za a gayawa kowa ba sai bayan kwana uku, a lokacin za a gaya wa mutane cewa wane fa ya mutu, ya zama babu.Wato wane, ya riga mu, wane ya yi kasala bai jure ba. Za a ɗauko gawarsa zuwa wurin tsafin Magiron don ya shaidar da cewa lalle ya mutu ne. An samu ragowa ne, don haka sai a kashe ko a yanka masa daga cikin dabbobin da za a yi bukin mutuwa da su. Ana zuwa da tsofaffi da matsakaita da masu ji da kansu da ƙarfi ƙwarai wato jarummai samari. Za a kai shi cikin kogon duwatsun ne wasu na kuka, wasu na ihu da shewa da kyakkewa, tare da guɗa, ana tafi da baƙaƙen bunsura da kuikuyo da kaji duk uku – uku, waɗan da za a kashe wa tsafin don ya sha jini, tare da tulunan giya da hura da nono da sauran kayan bukin mutuwa.

            Bayan an dawo daga wurin tsafin ana tafe da kaɗe – kaɗe da raye – raye da bushe – bushe za a je can bayan gari wurin rufe shi ana ta ihu da kuka da kyakyewa, ana tafi ana zuba masa ruwan giya. Za a ajiye shi a ƙasa a gina inda za a sa shi ciki. Ana bulbula masa giya a bakinsa da jikinsa. Bayan an sa shi, kafin a rufe shi za a yi masa gargaɗi kamar yadda suka saba kamar haka:

                        “In ka je ka ce kai kaɗai ka rage!

                        Kai kaɗai ne ba sauran kowa!

                        Babu sauran kowa a sararin ƙasa!

                        Kuma ga ka nan ka taho!

                        Babu kowa duk sun ƙare!

                        Babu kowa ne?

                        Duk sun koma!

            Bayan an gama sai mutane su ce:

                        A she wane ya yi kasala!

                        Wane bai jure ba, ya yi kasala!

                        Ai wane bai jure ba!

                        Bai jure ba!

Ya kasa!

            Bayan an dawo da kaɗe – kaɗe da raye – raye da sauran shagulgulan da ake yi na ciye – ciye da shaye – shaye da sauran hidimomin bukin mutuwa da aka gudanar,za a ci gaba har kwana bakwai. Ranar da za a yi bukin sati ɗaya bayan na kwana uku da aka yi sai a jira na kwana arba’in (40).

            Bayan kwana arba’in (40) ana sake gudanar da bukin mutuwa, za a sake taruwa kamar yadda aka yi na farko a yi shaye – shaye da kaɗe – kaɗe da raye – raye ga kuma shagulgulan abinci irin su tuwo da nama, sai dai ba za a shiga ɗakin mamacin ba sai ya kwashe shekara a kwance. Bayan an je an dawo sa’annan a fara shigarsa, ana iya ba wani cikin danginsa ɗakin ya zauna.

            Bayan bukin kwana arba’in sai na juya kafaɗar gawar don cika shekara ɗaya da mutuwa.Akan yi shi ne idan ya shekara ɗaya, amma idan mutum ba ya da hali yana iya bari har ya samu sannan a yi.Wato a bisu bashin bukin mutuwar kenan. Wannan shi ne bukin gawa na ƙarshe wanda daga gareshi ba wani sauran bukin mutuwa. Don haka ga masu arziƙi za su ɗebe kunya ga ‘yan uwansu, za a taru kamar yadda aka saba taruwa har wannan taron ma sai ya fi sauran domin wannan shi ne babban bukin mutuwa. Za a gayyaci mutane tun daga unguwanni, da ƙauyuka, da  garuruwan ƙasar Kwatarkwashi masu bautar tsafin Magiro magajin duwatsun.

            Za a yanka duk dabbobi nan a cikin raminsa, bayan an fito da su kafin a ajiye su ana faɗin waɗan da suka kawo mishi kayan bukin mutuwa, ana kwara wa raminsa giya,  daga nan sai kirari kamar haka:

                        “Tsoho ka kwanta lafiya!

                        Mun gode ma!

                        Mun gode ma arzikin ka!

                        Mun gode ma tsafin Magiro!

                        Mun gode ma kwanan Magiro ta magaji!”

            Bayan haka sai shugaban tsafin ƙasar Kwaarkwashi ya ce magaji jikan Magiro ya amsa!

                        “Kwanta lafiya in ji Magiron magaji!”

            Daga nan sai a dawo gida a ci gaba da shagulgulan mutuwa har zuwa kwana uku ana yin bukin. Sai a kira matan mamacin ko su nawa ne don su yi rawa ta al’adar mutuwa, ana yi masu kiɗa da kirari. Daga nan sai a raba su zuwa ga manyan abokansa, don su matan ba su da gadon komai na dukiyar da ya bari, sai ɗiyansu ke da wannan gado.

4.9 HANYOYIN GARGAJIYA NA MALLAKAR MACCE A MAGUZANCE

            Akwai hanyoyi masu yawa da Maguzawan ƙasar Kwatarkwashi ke mallakar macce kafin a ɗaura masu aure da ita kamar haka:

i.     Neman Aure: A na mallakar mace ta hanyar neman aurenta bias ga yarjejeniya ta magabatan miji da mata.  

ii.     Yaƙi: A na mallakar mata ta hanyar yin yaƙe – yaƙe tsakanin wani gari da wani, ko wata nahiya da wata, idan wani ya ci wani gari da yaƙI sai auratayya ta shiga tsakani.

iii.  Samame: A na mallakar mace ta hanyar samame. Wannan wata dabara ce ta mallakar mace ta hanyar kawo ma gari samame lokacin da masu garin suna gonaki ko kuma a yi samako.

iv.   Hari: A na mallakar mace ta hanyar kawo hari a cikin gari, wanda shi wannan hari yana kasancewa a taso ma gari kai tsaye. 

v.      Tsintuwa: A na mallakar mace ta hanyar tsintuwa sai ta zama matar mutum.

vi.   Bashi: A na mallakar mace ta hanyar bashi tsakaninta da mijinta ta hanyar yarjejeniya.

vii.Saye: A na mallakar mace ta hanyar saye a wancan lokacin da akwai bayi. Sai mutum ya tafi ya sawo baiwa ta zauna a matsayin matarsa.

viii.    Kyauta: A na mallakar mace kyauta ta hanyar uwayenta su ba da ita ga wani sadaka, a matsayin aure gare shi.

ix.    Kwartanci: A na mallakar mace ta hanyar kwartanci, ko shige, ko tsallaka katanga. Wanda zai iya kasancewa da yardar mace ko kuma babu. 

4.10 LALACEWAR MAGUZANCI A KWATARWASHI

Lalacewar Maguzanci a ƙasar Kwatarwashi ta faru ne ta dalilan:

·         Zuwan Turawa

·         Shigowar baƙin haure

·         Samuwar ilimin boko da tsarin yankuna

Mutanen garin Kwatarwashi yaransu da manyansu sun taka rawa wurin biɗar ilimin addinin Musulunci ƙwarai da gaske. Ba don komi ba sai don su gane addinin gaskiya. Su bar bautar tsafi a yankinsu. Saboda zaman shi addinin gado tun daga kakanninsu aka fara shi zuwa lokacin da suka bar shi zuwa ga addinin gaskiya. A kan haka ne kuwa aka samu karkato mutanen da su dawo ga kaɗaita Allah tare da yarda da Annabin Allah wanda Allah, ya aiko masa da manzanci shi ne Annabi Muhammad (S.A.W). Tare da neman gafarar Ubanhiji Maɗaukakin Sarki Allah bisa abun da suka aikata na bautar tsafin Magiro.

Duk da haka har yau akwai masu bin bautar tsafin Magiro na magaji, sai dai sun ragu ƙwarai don ‘yan kaɗan ne suka rage. Daga baya masu zuwa wurin bautar tsafin Magiron su ma duk sun matsa can cikin daji. Sai dai suna zuwa a duk shekara in ta yi don zuwa bautarsu na aure ko haihuwa ko na mutuwa.

Bayan haka, addinin Musulunci ya ci gaba da yaɗuwa ƙwarai har aka kai ga samun maluman addinin Musulunci don su yaɗa ilimin bauta ma Allah sosai. Ga kuma masallatai a cikin garin da kewayen garuruwan ƙasar Kwatarkwashi. A sanadiyyar haka ne aka samu ɓalɓalcewa ko lalacewar bautar tsafin Magiro a garin Kwatarkwashi, daular ƙasar Zamfara a shekara ta (1804/05) a ƙarni na sha tara.

4.10.1 ZUWAN TURAWA GA MASU BAUTAR MAGIRO

Bayan jihadin Shehu Usmanu Ɗanfodiyo ya zama abu na farko wurin ɓalɓalcewar bautar tsafin Magiro ga Maguzawan Kwatarwashi a shekara – shekara; sai wasu suke komawa ga wancan bautar tsafin Magiro na addinin gargajiya na gado. Ana cikin haka, sai ga Turawan mulkin mallaka sun ɓullo ƙasar Zamfara bayan hijirar sarkin musulmi Attahiru na ɗaya, a sanadiyyar  yaƙe – yaƙen da ya yi na musulunci a kan turawan mulkin mallaka. Masu son kame ƙasar Hausa su mai da ita ga mulkin da ba na Musulunci ba. Don su kauda mulkin addinin Musulunci suka ɗauro yaƙi tun daga ƙasarsu ta Ingila zuwa nan ƙasar Hausa Daular Usmaniyya. A zuwansu sun ya da zango ne a garuruwan Hausawa da yawa kafin su iso cibiyar Daular Usmaniyya a garin Sakkwato. Sun fara aje sansaninsu a garin Zuru da Yauri da Birnin Kebbi da Kwatarkwashi. A sanadiyyar wannan zaman suka yaɗa nasu addini na Kiristanci don suna taimaka masu ta hanyar abinci da sha da sutura da kuma kula da lafiyarsu da warkar da kutare, da makafi, da guragu da masu ciwon inna, musamman ma na garin Kwatarkwashi.

Bayan sun gama yaƙin daular Usmaniyya, sai suka koma wuraren da suka fara zama don sun gano ba su da addini sai na gargajiya suke bi. Masu tasiri musamman ma ga garuruwan da ke kewaye da duwatsun sun yi masu gine – ginen gidaje da wurin bautarsu “chochi”. Turawa sun ci gaba da ba mutanen garin kuɗi tare da kayan sana’o’i a kan noma da kiwo da sauran ƙere – ƙere na gargajiya. Da haka suka yi sanyi ga addininsu na gargajiya. Sai dai mabiya addinin gaskiya suna nan cikin Musuluncinsu ba ja da baya.

A kan haka addinin Kiristanci ya yi tasiri ga wasunsu sosai. Dangane da haka na ce lalle a nan ma saboda samun addini biyu a ƙasar, to fa bautar tsafin ya ɓalɓalce ƙwarai da gaske. Turawa sun shigo yaɗa addinin Kiristanci a ƙasar Hausa ta daular Usmaniyya tun daga kudanci zuwa arewacin Nijeriya, don sun zo ne ƙarƙashin su koma ƙasa ɗaya, ƙarƙashin addininsu na Kiristanci a shekara ta (1903) bayan sun samu wurin zama.

4.10.2 RUSHEWAR BAUTAR MAGIRO

Bayan masu mulkin mallaka Turawa sun ba da nasu gudunmawa ga masu bautar tsafin Magiro. Sai Allah Maɗaukakin Sarki ya ba su Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato firimiyan jihar Arewacin Nijeriya mulkin ƙasar nan. Shi ma ya taka rawa sosai don ganin cewa mutanen Kwatarkwashi masu bin addinin Turawa da na bautar tsafin Magiro na gargajiya duk sun dawo ga na Musulunci, addinin gaskiya. Don haka, gwamnatin Sardauna ta taimaka ma mutanen garin ƙwarai da gaske. Daga nan aka samu shigowar baƙin haure da suka shigo a sanadiyyar aikin jirgin ƙasa daga Zariya zuwa Gusau har wucewa Ƙauran Namoda a shekara ta (1920 – 1929).

Saboda haka gwamnatin arewacin Nijeriya ta Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato ta taimaka wajen dawo da martabar addinin Musulunci, musamman ma garin Kwatarkwashi, a ƙarƙashin Jama’atun Nasarar Islama (J.N.I), ta Nijeriya ta samu ‘yancin kanta daga Turawan mulkin mallaka na Ingila a shekara ta (1960). To nan ma tsafin Magiro da Kiristanci duk sun rage ƙarfi sosai, amma bautar tsafin Magiro shi kan ya watse saboda gaskiya ta bayyana “ƙarya ko dole ta dushe,” sai Musulunci addinin gaskiya.

 

4.10.3 TASIRIN ILIMIN BOKO GA RUSHEWAR MAGIRO

Samuwar ilimin boko ya yi tasiri ƙwarai a garin Kwatarkwashi don ya taimaka wurin ɓalɓalcewar addininsu na gargajiya wato “Bautar Tsafin Magiro”. Turawan Ingila da suka zo yankin ƙasar sun gane cewa ba su da wani addini sai na gado, wanda ya yi tasiri ga wasun su a shekara ta (1960 zuwa 1968). A kan haka suka taro mutanensu don son yaɗa addinin Kiristanci sai suka zauna a gefen gari suka ba da abinci iri – iri da tufafi da kuɗi tare da taimaka masu a fannin kiwon lafiyarsu ta hanyar ba su magunguna da gidajen zama da asibiti da chochinsu ta addinin Kiristanci.

Ba a an karo ba sai mutanen ƙauyukka da garuruwan Kwatarkwashi suka yi ta komawa addinin Turawa, amma ban da babban birnin garin. Shi kam yana nan cike da masu bin addinin Musulunci sosai. Sai dai duk da haka masu zuwa yin bautar tsafin Magiro ‘yan kaɗan ne, har lokacin mulkin Alhaji Shehu Aliyu Shagari, Turakin Sakkwato a shekara ta (1979 zuwa 1983). Bayan janar Olushegun Obasanjo ya ba shi mulki har zuwa juyin mulkin da aka yi masu wanda janar Muhammadu Buhari Daura ya yi, a shekara ta (1983 -  1985). A wannan lokaci da Burgediya Garba ke gwamnan jihar Sakkwato aka sa doka da ta hanasu zuwa bautar tsafin Magiro na shekara. Masu zuwa kamo maiki a saman duwatsun don nuna jaruntakar tsafin duk an ce su bari. Sa’an nan ita ko ƙungiyar Izalatul Bidi’a Wa Iƙamatus – sunna (JIBWIS) ta taimaka ƙwarai wajen yin wa’azi na Musulunci ga mutanen da aka hana, to da yawa kuwa sun dawo ga Musulunci.

Duk da haka ba su rabu da yi ba sai shekara ta (1987 zuwa 1989), a nan ne aka sake hana su a lokacin gwamnan mulkin soja na Sakkwato Ahmadu Daku. A wannan shekara ne fa ta faru ta ƙare, saboda suna cikin yin hidimominsu na bukukuwan aure da ake hawa duwatsun bautar tsafin. Ga ‘yan kallo sun taru ana kiɗe – kiɗe da bushe – bushe tare da kirari da waƙoƙinsu, ga kayan shaye – shaye nan da ciye –ciye kamar yadda suka gada. Bayan an fara hawan duwatsun, duk samarin jarumawa da za a ba sun haye an kuma fara ɗauro masu tsuntsun maiki a bayansu don su sauko da shi ƙasan duwatsun daga saman su, wasu daga cikinsu sun kai ƙasa, a nan aka samu wani tsuntsun maiki ya farka daga barci, sai ya tashi da wanda aka ɗaura ma shi a baya, ya yi sama da shi sosai. Aka yi ta kallonshi, bai yiyuwa a harbe shi tunda tare da mutum yake ɗan uwansu, sai ya dawo saman duwatsun. Shi ke nan da mutumin da tsuntsun maikin ba a gane namansu duk sun fashe. Shi ke nan sai aka bari baki ɗaya, aka bar zuwa bautar tsafin. Ta haka ya lalace babu shi. Sai suka koma Kiristanci a chochi, saboda zaman Turawa a garin aka fara yin makarantar boko a shekara ta (1940 zuwa 1945). Kafin yaƙin duniya na biyu da bayanshi a yankin ƙasar Zamfara.

An samu tsarin yankunan jahohi da ƙananan hukumomi a lokacin mulkin soja Janar Yakubu Gawon a shekara ta (1967 zuwa 1975). Sai Janar Murtala Ramat Muhammad (1975 zuwa 1976), zuwa lokacin Alhaji Shahu Shagari a shekara ta (1979 zuwa 1983). Waɗan nan shuwagabanni su ne suka ƙirƙiro da yankuna da jahohi da ƙananan hukumomi don ba da ‘yanci da ci gaban hukumomi tare da matsowa da mutane kusa da gwamnati. Daga waɗancan shekarun zuwa lokacin mulkin soja na Janar Ibrahim Badamasi Babangida a shekara ta (1991) duk garin Kwatarkwashi yana ƙarƙashin ƙarmar hukumar Gusau. Sai a wannan shekara aka mai da shi ƙarƙashin ƙaramar hukumar Bunguɗu har zuwa yanzu.

Bayan wannan, a shekara ta (1996), lokacin mulkin Janar Sani Abacha aka ƙirƙiro jihar Zamfara saboda kusantowar gwamnati ga jama’a, a yankin garin Kwatarkwashi. An yawaita kiraye – kirayen jama’a ta hanyar wa’azi da hanyoyin addinin Musulunci ke yi ga masu biyar addinin gargajiya da Kiristanci.

Bayan an yi siyasa, Allah Maɗaukakin Sarki mai Sarauta ya ba Alhaji Ahmadu Sani Yariman Bakura mulkin jahar Zamfara a matsayin gwamna, a shekara ta (1999 zuwa 2006), ya ƙaddamar da shari’a bayan ya shekara ɗaya da hawa mulkin. Wannan ƙaddamar da shari’a ta yi tasiri ƙwarai, musamman ma ga mutanen Kwatarkwashi waɗanda ke zaune a saman duwatsu. A farkon shekara ta 2001(25/1/2001) aka samu mafi yawan garuruwan masu bin addinin Kiristanci tare da fastocinsu suka koma addinin Musulunci ta hanyar wa’azin gari da gari na jahar Zamfara zuwa lunguna don isar da saƙon Musulunci. Don haka ana iya cewa, Allah Shi ja zamanin gwamnan jahar Zamfara, Ya ba shi haƙuri da juriya ga ‘yan uwanshi Musulmai, tare da taimaka masu ci gaban addininsu baki ɗaya.

Post a Comment

0 Comments