Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsafe–Tsafen Maguzawa: Nazari A Kan Bukukuwan Maguzawan Kwatarkwashi (6)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Tsafe–Tsafen Maguzawa: Nazari A Kan Bukukuwan Maguzawan Kwatarkwashi (6)

NA

ABDURRAHMAN LAWALI

Maguzawa 

BABI NA BIYAR

KAMMALAWA

5.0 GABATARWA

            A babin da ya gabata na yi bayani a kan ire – iren bukuwan Maguzawa da al’adunsu da hanyoyin mallakar macce a Maguzance.

            Wannan babi yana ɗauke da bayanin kammalawa, sakamakon bincike, shawarwari da manazarta.

5.1 BAYANIN KAMMALAWA

Kamar yadda na yi bincike a wannan littafin kundin digirin farko a kan abin da ya shafi al’adun Maguzawan ƙasar Kwatarkwashi waɗan da ba su da addini sai na gargajiya. Wato Maguzanci ke nan, wato yadda Maguzawa ke gudanar da harkokin rayuwarsu a lokacin addinin kakanni na bautar tsafe – tsafe a bukukuwan Maguzawan Kwatarkwashi wanda suka iske su suna yi a matsayin abin da suka yi imani da shi.

Sanadiyyar yaɗuwar addinin Musulunnci mafi yawancin Maguzawa sun musulunta. Sai dai har yanzu ana samun su jefi – jefi tare da burbushi ko nason al’adunsu na Maguzanci.

A kan haka na rubuta wannan littafi wanda ke nuna yadda al’adun Maguzawan ƙasar Kwatarkwashi da ke yankin ƙasar Zamfara suke aiwatar da al’adunsu. Na kasa aikin babi – babi tun daga na ɗaya har zuwa na biyar.

5.3 SHAWARWARI

            A wannan aiki na fuskanci abubuwa da dama, waɗanda nake ganin sun ba ni matsala don haka ina shawartar ‘yan uwana ɗalibbai da su maida hankali a kan karatunsu domin samun sauƙin gudanar da bincikensu wanda zai yi sanadin samun sakamako mai kyau.

            Ina ƙara shawartar ‘yan uwana ɗalibbai da su yi biyayya ga malamansu da duk wani mai haƙƙi domin samun kyakkyawar nasara a kowane yanayi da mutum ya samu kanshi a ciki.

MANAZARTA

Tuntuɓi masu gudanarwa.

Post a Comment

0 Comments