Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsafe–Tsafen Maguzawa: Nazari A Kan Bukukuwan Maguzawan Kwatarkwashi (4)

Kundin Binciken Neman Digirin Farko (B.A Hausa) Wanda Aka Gabatar A Sashen Harsuna Da Al’adu Jami’ar Tarayya Gusau.

Tsafe–Tsafen Maguzawa: Nazari A Kan Bukukuwan Maguzawan Kwatarkwashi (4)

NA

ABDURRAHMAN LAWALI

Bokaye

BABI NA UKU

TARIHI DA SHUGABANCIN MAGUZAWAN KWATARKWASHI

3.0 GABATARWA

            A babin da ya gabata na yi tsokaci a kan ma’anar Maguzanci, kuma su wane ne Maguzawa, da yadda Maguzawa ke yin Maguzanci da amfanin Maguzanci da Maguzawa sa’arnan aka kammala babin da naɗewa.

            A wannan babin za mu yi bayanin taƙaitaccen tarihin Maguzawan ƙasar Kwatarkwashi, da dangantakar Maguzawan Kwatarkwashi da wasu Maguzawan ƙasar Hausa, al’adun Maguzawan Kwatarkwashi da sana’o’in Maguzawan Kwatarkwashi. Daga ƙarshe mu biyo da naɗewa.

3.1 TAƘAITACCEN TARIHIN ƘASAR KWATARWASHI

Haɗaɗɗiyar daular Katsina ta fara mulkin garuruwan da ke ƙarƙashin daular Zamfara tun farkon mulkin daulolin ƙasar Hausa. Asalin garuruwan da ke ƙarƙashin yankin ƙasar Katsina duk suna ƙarƙashin shugabancin sarkin Katsina.Yawanci masu mulkin garuruwan Katsinawa ne, waɗanda suka yaƙi ɓangaren wata ƙasa; sauran ko ba yaƙi ba ne, sai zaman lafiya a tsakanin garuruwan da suke maƙwabtaka da su. Sanadiyyar haka ya sa suke ƙarƙashin mulkin ɗaya daga cikin garuruwan kamar haka: Zurmi da Kiyawa da Ƙaura – Namoda da Rawayya da ‘Yandoton – daji da Maru da Bunguɗu da Magami da Dauran da sauransu. Garuruwan da ke ƙarƙashin daular Katsina a can da bayan masarautar Katsina ta ba su walwalar samun ‘yanci ga waɗannan garuruwan, wasu ko saboda jaruntaka suka maida yankin ƙasar ƙarƙashin mulkin Zamfara.

Bayan wannan ne aka samu garuruwan kamar haka: Tofa da Magami da ‘Yandoton – daji da Bunguɗu da Wonaka da Rawayya da Ɗangulbi da Dauran da Mada da Moriki da Ɗankurmi da Gada da Maru da sauransu. Wannan ya faru tun ƙarni na goma sha biyu zuwa na sha ukku (12 – 13). An samu ƙasashe da garuruwa cikin ƙarni na goma sha biyar zuwa na sha shida (15 – 16).Wannan ko ya faru ne tun kafin jihadi na Shehu Usmanu Ɗanfodiyo waɗannan garuruwa suke ƙasar Zamfara don su ne tushen Zamfarawa na farko.

3.2 DANGANTAKAR MAGUZAWAN KWATARKWASHI DA WASU MAGUZAWAN ƘASAR HAUSA

Kamar yadda muka ambata tun farko cewa, su Maguzawan Kwatarkwashi wato waɗan da ba su karɓi kowane irin addini ba, wanda daga ƙarshe ya haddasa yaƙin su da Shehu Usmanu Ɗanfodiyo. Wannan shi ya sa suka fantsama cikin duwatsu inda suka ci gaba da gudanar da rayuwarsu ta Maguzanci.

Kuma idan mun koma wajen wata hikima ta kama maiki ko hawan maiki! Lalle kowa ya san da cewa maiki dai ba ƙaramin tsuntsun da mutum kan iya kamawa ba ne. Dole ne sai wata hanya ta sihiri ko tsafi. Domin ko mahalbi da ke yawon halbi yana da wuya su kai inda maiki yake, balantana ace an halbe shi. Kuma ba wai halbinsa ba ma, a a, wai mutum ya kamo shi daga kogon dutse. Inda su kuma ‘yan wasa suna tare da shi suna ta kiɗe – kiɗe har shi maikin ya sauko zuwa ƙasa. Sannan ya nufi zuwa fadar Sarkin Kwatarkwashi na wancan lokaci. Kuma suna hawan maikin domin gudanar da al’adunsu na gargajiya don biyan buƙatarsu na tsafe – tsafe da sihirce – sihirce na hanyoyin rayuwarsu. Kuma maikin zai kwana nan gidan sarki, su kuma jama’a na ta gudanar da shagulgulan su, kuma suna yi wa wanda ya hau wannan maikin kyauta.Wannan shi ke nuna cewa za a samu shekara mai albarka ke nan. Amma idan gari ya waye, za a sallami wannan maiki ya koma gidansa cikin dutse inda aka kamo shi.

Kuma wani abun mamaki a nan shi ne, shi wannan maiki da aka kamo, ba wai ana ɗaure shi ba ne idan ya sauka, a a, ana sakin sa ne kuma ya tsaya da kansa inda ake gudanar da waɗannan wasanni a fadar sarki. Kuma har yakan tsuguna a kusa da shimfiɗar sarki har gari ya waye. Wato har a tashi daga wurin wasan kafin a sallame shi ke nan.

Bayan wannan, Maguzawan Kwatarkwashi na da wasu manya – manyan hanyoyin tsafe – tsafe, wato na gudanar da Maguzanci kamar ta hanyar yin amfani da wani tsafi wanda ake kira Magiro. Shi wannan Magiro suna amfani da shi ne lokacin aurar da ‘ya ‘yansu mata. Shi wannan Magiro yana da kama da bori, domin kuwa akan buƙaci ya hau kan ita wannan amarya kafin a kaita gidan mijinta.

Haka kuma akwai wani irin tsafi da Maguzawan Kwatarkwashi ke yi wanda ba a taɓa ganin irin sa a cikin kowace irin al’umma ta Maguzawa ba.Wannan irin Maguzanci shi ne wanda ke jagorancin haɗa kan Maguzawa ko ina da ke ƙasar Hausa, lokacin bukinsu. Wannan Maguzanci kuwa shi ne wanda ake kira (Kyauka) wanda za a tsakuro bayaninsa a cikin bukin cikar shekara.

3.3 TSARIN SHUGABANCIN MAGUZAWAN KWATARKWASHI

A yanzu tasirin shugabanci ya banbanta da na lokacin Maguzawa saboda a wancan lokacin, kome a fadar mai gari ake gudanarwa.Ana gabatar da al’amurran jama’a na sassansu a kan shari’a irin ta al’adarsu da suka gada  ta bautar tsafinsu. Yanzu duk hukunce – hukuncen shari’a ya koma ga gwamnatin tarayya da gwamnatin jahohi har zuwa ga ta ƙaramar hukuma.Su ke gudanar da harkokin shugaban ƙasar baki ɗaya ba kamar yadda ake yi ba lokacin da ake bin al’adun gargajiya wanda aka gada tun asalin kakanni.

Duk da haka ba a bar sarakuna a baya ba, saboda su ne iyayen ƙasa, su ke ba da shawara tare da kula da jama’ar ƙasar nan tamu. Da yake garin Kwatarakwashi ba ƙaramar hukama ba ne, amma tana ƙarƙashin ƙaramar hukumar Bunguɗu ce a yanzu. Suna da tsarin shugaban na fada, don sarautar garin mai daraja ta uku ce; akwai dagaci da hakiminsa, tare da masu unguwa da sauran shuwagabannin sarautar gargajiya a garin Kwarkwashi da ƙauyukkanta da kewayen duwatsu kamar haka:-

Mai girma Sarkin Kwatarkwashi da Garkuwa da Galadiman Kwatarkwashi da Bunun Tofa da Ɗan – sankala Sarkin Samawa da limamin gari da ladani da na’ibi da sakataren sarki da mai ba shi shawara a majalisarsa da ‘yan majalisarsa na fada da sarkin dogarai tare da dogarawan fadar sarkin.

Wannan shi ne tsarin shugabanci a garin Kwatarkwashi da kewayen ƙauyukkan shi gaba ɗaya.

3.4 AL’ADUN MAGUZAWAN ƘASAR KWATARKWASHI

Kamar dai yadda muka sani cewa kowace al’umma tana da irin nata hanyoyin tafiyar da al’adunsu, ya Allah ta ƙarƙashin wata doka ta addini ko ta gargajiya wadda kowane daga cikin al’umman nan ya yarda da ita. Kuma ya bayar da gaskiya da ita, da kuma kiyaye dokokinta. Haka su ma al’ummar Maguzawan Kwatarkwashi suna da irin wannan tsari da suke gudanar da rayuwarsu a cikin wasu muhimman lokuta idan sun taso.

3.5 SANA’O’IN MAGUZAWAN KWATARKWASHI

Maguzawa suna da sana’o’insu na gado da suka gada tun daga kakanninsu. Suna gudanar da su ne domin samun abun da suka ci da kuma juyawa yau da kullun, musamman aikin hannu. Asalin sana’o’in Maguzawa daga aikin hannu suka fito ta hanyar don ta nan ake gudanar da kasuwanci wanda ya samu asali fatake masu tafiye – tafiye daga gari zuwa gari. Suna da sana’oin da suke gudanarwa na hannu kamar haka:

a)      Noma: Noma tushen arziki na duƙe tsohon cinaki. Akwai tsafin da ake yi ma gona komi yawanta sai ta koma ƙarama, akwai na ruwan sama watau su zubo ko ba lokacin damina ba, ko don kayan gona su yi kyau.

b)     Baushi: Masu zuwa halbin namun daji da na cikin kogo a nan cikin duwatsu da samansa ana samun su birai da maiki, sukan je daji ba su samo komi ba, ko wani abu ya koro mutum daga saman duwatsun don ban tsoro.

c)      Kiwo: Kiwo abu ne wanda suka gada tun kakanni, tun waɗanda ake kiwon a gida har na zuwa daji kamar awaki da bunsura, tumaki da raguna, zabbi, kaji, agwagi da sauransu.

d)     Wanzanci: Yin aski da tsaga da kaciya da ƙaho don neman lafiya da tsaftan jiki tare da bin gado don sanin asalinsa.

e)      Ƙira: Su ne maƙera masu ƙere – ƙeren wuƙa da takobi da barandami da kwashe da hauya da lauje da sauransu. Duk su ke yin su saboda aikin gado ne gare su.

f)      Sassaƙa: Su ke sassaƙa turmi da ɓota da taɓarya da mucciya da sanduna da gora. Duk ana amfani da su ne don kare kai da taimakon kai, saboda ci gaban rayuwa.

g)     Fawa: Su ne masu kula da yankan dabbobi don a ci a sayar ma jama’a bisa ga gado.

h)     Rini: Wannan sana’a ce da ake yi don a sake ma tufa launinsa zuwa wani launin da ake so. Misali, daga fari zuwa baƙi ko wanin haka.

i)       Ɗunki: Masu saƙar tufafi na sawa. Misali, riga, wando, hulla da takalma daban – daban bisa ga al’ada don sayarwa ga mutane su amfana da shi.

Wannan shi ne tsarin sana’o’in Maguzawan ƙasar Kwatarkwashi da yadda suke gudanar da su; tare da siddabarun tsafin da suke yi. Saboda imani da amincewa da faruwan wani abu, bisa ga al’adar gargajiya ta masu bautar tsafin Magiro na magajin duwatsu, ya sa sana’o’in Maguzawa suka yi tasiri a wannan zamani.

Post a Comment

0 Comments